chapter 43

250 15 0
                                    

Halal veer❤

Duk wani belongings nata ta gama hadawa a daren ranan da ta koma "
Dama already tayi sallama da hostel da sababin mutanenta naciki wato su farha so gidansu khausar ta wuce dan kwana"
Fitowanta kenan a wanka daga ita sai bathrobe ,
Tsaye take a bakin mirror tana goge sumanta inda kaman an jefo khausar ta bayyana a gabanta "
Kallonta tayi slightly then ta maida hankalinta kan me take tareda fadin"beb what's up"

Tabe baki khausar tayi kaman zatayi kuka tace mayhap I'm regrating it now "
Dago kai nuayma tayi takalleta tace me kenan"

Letting go of that same one year "ta bata amsa a takaice "
Ajje towel din da take goge kai tayi tareda zama tana facing dinta then ta kama hannayenta tace look here khausar "babu wani abun danasani and nasan cewa you're this down sabida zai zama ke kadai a nan and its nothing, stop getting all this weird idea into your head beb it just a matter of a year and kaman yaune zai kare and we will be all around you to celebrate your great day "
Daga mata gira daya tayi tace and mark you nasan cewa kina wannan abunne sabida nusayr zai tafi huh"
Come on lover girl I'm sure zaina zuwa ganinki often i trust that guy"

Dukan wasa khausar ta kaimata tareda fadin i hate you"
Dafe saitin zuciya nuayma tayi tareda fadin "ummm i know and I love you too.

************************************
NIGERIA

Taso ace a ranan da ta sauka a Nigeria ta sauka ne a gidan su amma da ummi sukazo daukan nusayr da hamma ibi da suka taho tare ta nunamata fafur idan tabisu gida kaman bata daraja surikanta ba ,
Ya so yayi mata kawaicin tabisu din sabida dadewar da tayi bata gansu ba amma abba yace lallai tabi mijinta inyaso ranan da ya tanada domin hada musu bikin tayasu murna tazo gida wato bayan kwana biyu,

Babu yarda ta iya tanaji tana gani ta hau motar da aka turo daga gidan sarautan tareda karfen kafanta wato adeel ,taso ace maimuna ta bisu amma sam tace itama zaazo a daukanta daga gida dan haka dole tanaji tana gani ta hakura ,
Tunda suka shiga motan bai ce mata komai ba hakazalika itama batace masa komai ba illa tunanin wannan gida da bata kaunar zuwansa da zatayi "

Tundaga haraban babban gate ake musu busa,inda maroka keta zuzuta yariman na biu da matarsa nuayma ,babban abunda ta tsana kenan,

A fada suka fara sauka domin kwasan gaisuwa gurin mai martaba inda yasanya musu albarka tareda mata adduan Allah yasa abunda ta karanta yamaza alkhairi a gareta and lastly ya shaida mata kautarsa kuma ta rigata zuwa gida "
A tare suka ma sarki godia inda daga nan suka wuce gurin mai babban daki suka miki gaisuwa kana sukaje gurin Fulani wadda taringa sussune kai duk da murnan dawowan yaron nata datake da sirikanta amma bata nunaba sabida kunya.

Dakin gwago amarya ne na karshe inda suna shiga idanunta suka sauka kan nuayma taji wani abu ya tsaya mata dan bata cire dayan biyu cewa nuayman nada ciki kuma tayi imani da bokanta da ya shaida mata nuayma da adeel saidai suga yara agidan wasu amma baa nasu ba"

Bakaramin tashin hankali tashigaba lokacin da ta tsinci labarin dawowansu gun mai babban daki dan haka batayi kasa a gwiwaba wajen komawa ga bokan ta akan dadadden aikin da yayi mata na hanasu haihu ,
Bokan yakara tabbatar mata dacewa wannan aiki yananan sannan babu abunda zai karyasa dan haka ta kwantar da hankalinta ,to tuna wannan abu datayi yasaka ta kauda tunanin ko cikine da nuayma tabarshi kancewa maybe hutune da take samu bugu da kari kuma yanayin wata kasar daban da ya amsheta ,

Yatsine yatsine tafara bayan sun gaishe ta kafun a wani dakile tace lapia lau angama bautan yahudawan andawo kenan ,
Sudai basuce mata komai ba illa yake da sukai ta aikamata dashi "
Basu wani dade adakinba sukai bangarensu dan sun kosa kar ma ace nuayma da sai yanzu take kara tsanar family din da tashigo ,ace daga dawowanka ko hutawa baabarka kagamaba zaka fara aikin gaishe gaishen balai"
Batabi ta kan gifts din da ake ta nuna mataba dan wanka kawai take bukatan taga tayi sannan tana bukatan shiru da nutsuwa sosai,
Kaman yasan maike ranta yasallami kuyangunta hansatu da baba ladi,cike da ladabi suka fita a bangaren ,
Wanka tashiga kai tsaye ,bayan ta fitone ta shirya da sauri da sauri cikin wata light bakar abaya dan bakaramin kukan yunwa cikinta yake kiraba ,
Tarasa gane wannan sabon uban cin abinci da ta tsira na ba gaira ba dalili amma tafi dangantasa da cewa lapia ce tunda inba lapia ai bazama kasamu daman cin wani abinciba ,

Dining ta nufa kai tsaye ta fara bude warmers ,batayi aune ba sai jin numfashinsa tayi a wuyanta wanda dalilin hakan saida wani gasp dabatayi shirin zuwansaba ya halarceta,
Tana kokarin matsawa agun yayi saurin rike hannayenta guda biyu tareda rungumeta tabaya yana kara shakan kamshin jikinta wanda ita hakan bakaramin daga mata hankali yake ba,
Batacemasa komai ba dan muddin tayi magana to moan ne zai fita daga lips dinta and hakan zai zama babban abun kunya atattare daita ,
Saitin kunneta ya koma tareda rada mata "why the rush baza a jiraniba kenan "
Jin wani yar tayi a jikinta sakamakon yarda yake maganan seductively "

Wani karfi ta tattaro tareda turesa daga jikinta kana ta juyo tana facing dinsa fuskanann a murtuke tafara magana"
Adeel it will be for the best idan kowa yasan matsayinsa a gidanan dan Allah ,just let me be ,da kai zanji koda sick and tiring culture din gidanku,
Please karabu dani karnamaka abunda baizai kyauba har so called kuyangun gidanku suji "
DA haka taja kujera tareda fara serving ma kanta abinci .

Sick and tiring culture din gidanku"
Kalmar da ta fara masa yawo akai kenan ,bai taba tunanin nuayma zata zagi culture na gidansuba duk da cewa shima abun bai dameshi ba amma he respect it and yarda ta fadi abun ya sosa mishi rai ,
Bai kara cewa komai ba yabar gurin.

Bata wani damu ba illa ma tabe baki da tayi dan ko ajikinta abun bai dameta ba at all dan haka takara maida hankali wajen aikama cikinta sakon abincin"
Har dare bashigo dakintaba wanda hakan yamata dadi dan batasan yana rabarta sabida maimakon ta tsani hakan sai ta tsinci kanta da kaunar hakan.

*********
Washe gari tunda ta tashi a baccin safe take tsaki sakamakon yawonta dataji yana tsinkewa ,bata iya hadiyesa dan haka taketa zuryan shiga toilet tana zubarwa,
A Karo na yafi a kirga kenan tana kokarin tashi dan zuwa zubar da yawo kuyanga ladi tashigo "
Koda ta gaisheta kasa amsata tayi sakamakon yawon daya taru mata abaki dan haka da sauri tayi toilet dan zubar da wannan yawo ,

Murmushi ladi tayi tareda saurin fita a sashen dan zuwa kaiwa aynihin uwar dakinta wannan rahotan da dumiduminsa'
Bata tsaya ko inaba sai bangaren mai babban daki inda ta isketa a kishingide tana hutawa a garden dinta ,gefenta kuma kuyangune guda biyu suna mata fifita da mificin gashin dawisu,
cikeda girmamawa ta tsuguna tareda cewa "gaisuwa nake uwar dakina ranki shi dade"

Dan murmushi mai babban daki tayi tareda amsawa cikin girmamawa tace "hala malama ladi na tafe mun da labari mai dadi "
Dasauri ladi ta gyara zama tareda kada kai tace kwarai uwar dakina labarine nake tafe dashi wanda nasan dole zakiyi farin cikinsa dan babu dayan biyu sannan bani tantama kan cewa matar yarima adeel na dauke da juna biyu"

A hankali mai babban daki ta mike daga kishingidan dakate zuwa zama tare da fadin"
Kai ladi ban san wasa ita gimbiyar ta sanar dake hakan "

Kara sunkuyar da kai ladi tayi tareda fadin "aa ranki shi dade amma alamu nagani a matsayina na wadda ta dade a wannan harkan ai ko ina naga mai ciki zan gane "

Aw "cewan mai babban daki ,"kice tsurku kawai kike "
Murmushi tayi irin na manya tace "kije ki dauko doctor habib kuje sashinsu inaso yamata gwaji dan atabbatar domin sonake yazamana ni nafara bama sarki da fulani wannan labarin mai dadi "

Da sauri ladi ta mike jiki na rawa tafita domin aikata abunda mai babban daki tasakata "
Girgiza kai mai babban daki tayi ganin yarda ladi ke rawan jiki aranta kuma tana adduaa Allah yasa da gaske ciki nuayman kedashi dan a rayuwa tanasan adeel din da alkhairi sannan ta wani bangaren tana jin ba dadin larurar danta umar domin tasani cewa da tuni yanzu iyalansa sun cikata ,duk da cewa tana da jikokin gurin yaranta aysha da zainab .

Chu chu.

HALAL VEER √(completed)Where stories live. Discover now