chapter 25

234 19 1
                                    

Halal veer💍
DA dare jirgin da suka biyo zuwa nigeria ya sauka,
Finally lokacin semester break yayi and hutune wanda aka badashi bawani mai yawaba,amma yarda kowanne daya daga cikin su yake jinsa kaman an bada shekara ,

Nuayma,nusayr ,khausar,maimuna da hamma ibi jirgi daya suka bi a ranan da akai hutun,inda shikuma adeel ya shaida mata washe gari zasu taso sabida akwai abunda suke san suyi clearing out "

**
Already yanuwa sunfara zuwa gidan sakamakon bikin saura 2 weeks a yarda akasaka _
Part din nusayr aka basu itada kawayenta sakamakon dakinta da gwawwonta tayi occupying,

Fitowanta kenan a wanka inda ta tarar da su khausar suna ta faman zuba,
Murmushi tayi tacigaba da goge kanta da towel ,wai yau itane akazo taron bikinta da mosoyin ranta ,

Wayanta da yake kan mirror ne yayi kara ,
sunan ummi ne yayi appearing akan Screen din,
Kaman kar tayi picking instead taje sai kuma tayi tunanin ko maganan ba sai taje bane,so sai ta dauka"

Ummi "

Na am nuayma come to my room inasan ganinki"

Amsawa tayi da gata nan zuwa kafun tayi hanging wayan tana jinjina dalilin da yasa ummi ke kiranta"

Da sallama tashiga dakin ummin"
Zaune ta ganta gaban system dinta idanunta kuma dauke da medicated glass
Gefenta koma food flask guda biyu
,karasawa gefenta tayi tazauna "
Ummi aiki kike ne"

Cire glasses din ummi tayi tareda kada kai "yea ina wani aikine akan lecture dazaa yima internships din asibitinmu so i want to write everything down kafun bikinki ya hanani"

Talking about bikinki ayma ,kigan abun yazo mana unexpectedly,although ina miki gyaran da yakamata namiki tunkan ki kai haka wanda aladarmu ne na fulani but still dole na gyaraki yanzun ciki da waje kafun wannan sati biyun duk da yamin kadan,amma I'll try my very best na kwato miki darajan ki gurin mijinki,

Sannan kije kigan kayan lefenki a dakin abbanki"
And yea tun kan su kawo kayan lefe na kai miki dinkin 20 set at least bada na lefensu kika dogaraba ,everything is set and jibi zantura nusayr ga karbu harda na kwayenki"

Godiya tama mahaifiyartatan tana jin wata kaunarta na shiganta and lefe tagani a sannu"

Idanunta ta saukan kan food flask din dayake gefenta tace bude kula nan,

Tsugunnawa tayi tareda bude kula,
Tun a kanshi mara dadin daya daki hancinta tasan akwai kura ,
Budurwan kazane aka dafa shi ,
Yayi wani brown ga dan romo aciki daga gani yasha magani,

Dayan ta bude taga wainan kwai rufi biyu"

Kallonta ta mayar kan ummi tana neman karin bayani"
Murmushi ummi tayi tareda fadi yes ,cinyewa zakiyi,kingan irin wannan kazan zakici kaman guda shida and sai kinshanye roman ciki dukan"

Wannan fried egg din kuma suyan olive oil ne shima sai kin cinye ,kafun gobe kuma ki koma gidan kalthume da zama har sai ana gobe zaa fara biki,kome kike bukata it'll be taken care of"

Kulthume mutuniyar sokkotone and babbar kawar ummi ne"

Naman takeci tana yamutsa fuska,badan dan maggi maggin cikiba bayarda zaayi ya ciwo ,"

Kar ki tauna kashin "

Kada kai tayi tace to ummi,amma kuma dole sai na cinyeta duka?

Harma ki shanye roman sannan ki cinye wainan kwan nan"
I'm sure bakici komaiba ai"
Inkinje gidan kaltume har na sanyi da akeyi da na kayan ciki zata miki ,da tozan rakumi hardasu ganda,
Ke dai ki shirya kawai gobe zan kaiki sai ki gane ma idanunki"

Yanzu ummi dukan wadanchan abubuwan ni zanci?.

Harda sha ma yarinya"
Sannan yadikkonki ma zata miki namu na fulani so tare zaku zauna a gidan kalthume,
Dan haka sai ki hakura da cika cikinki da abinci"

Badai tace komai ba duba da komenene sukayi domin itane"

DA kyar tagama cinye komai kana ta tafi domin ta deba kayanta ta shiryasu ajaka"

Washe gari bayan maimuna da khausar babu wanda yasan fitansu"
Kara jaddada musu tayi kan nusayr ya kaisu su karbo mata dukan kayanta "

******
2 weeks later

Ummi tazo har gidan kaltume ta daukosu sabida gobe zasu fara biki"
Ita kanta saida ta yaba wani kyau dataga nuayma tayi"

Kodayake dama tasan zatayi dan kalthume tana gyara yayan wanda bata sani ba kuma bare tata"

Hijab har kasa tasaka tareda dora shade a fuskan ta "

Kokarin saka takalmi take kalthume ta miko mata safa tace "
Yarinyana a rufe lallen kar jamaa su gama gane miki kafin goben "

Murmushi tayi tareda karba "

Komai tagama mata, tamata wankin kan gargajiya sannan ta yarfa mata kitso kana yarinyanta zainab tayi mata lalle both ja da baki mai shegen kyau"

Zainab why not mutafi tare yau ?
Nuayma ta tambayi zainab bayan tagama saka safan"

Dafata zainab tayi tace kinsan wanchan tsimin fruits dana hada Miki sai gobe zaa sha and bana san mama ta manta so i have to make sure nadaukoshi da kaina sannan nabaki da kaina kinsha"..

Fadada faraanta tayi tace shikenan".

Ita kanta tasan ta hadu dan a rana tayi ta sake pant kenan,sannan wani daban take jinta"
**
Washe gari ihun wakan fulani da ake ma amare taji akanta ",
Bashiri ta mike tana toshe kunne,
Can Taji an daga ta sai compound,
Basu ajeta ko ina ba sai kan turmi ,kafun ta rufe baki sai jin kindirmo tayi tundaga kanta har kasa luckily da head warmer a kanta ,

Kokarin cire mata hulan wata abiyyar wasanta tayi,
Da sauri tarike tace please aunty kalthume tasa effort sosai wajen mun kitson nan kar kubatashi da kayan kar--
Bata kai ga karasawa ba sakamakon sanyin da taji kanta"
Wadda ta isa ta cire hulan "

Tas suka mata kafun aka bita da ruwan kamshi aka wanke"

Da kyar ta samu suka kyaleta kana taje tayi wanka "

Shigar blue kayan fulani tayi inda khausar ta dandara mata bridal makeup wanda yayi balain fito da ita "
Suna kokarin fita dayake a cikin gida zaayi wayanta yayi kara"

Adeel ne "kokarin dagawa take zainab ta fizge wayan tareda dagawa tace kayi hakuri a kawo maka ita gidanka tukunna ,
DA haka takashe "

Yake kawai nuayma tayi dan batasan tayi magana aga fitsaranta amma tayi kewansa ,ko a gidan aunty kalthume saidai tayi waya dashi a boye shima sau daya rabonda tasakashi a ido kuma tun kan ta baro london"

Biki sukai sosai na aladunsun ,kowa yaci yasha an gode Allah ,inda babban malama nablisi bako tazo tayi waazi sosai akan abunda ya shafi aure"
DA haka dai taro yatashi inda kowa ke sa ran washe gari inda zaayi kamu at the same Rana kuma zaayi dinner "

**
Washe gari bayan ankamata da rana sukayi dinner a hall din kung fu "
Komai cikeda kayatarwa akayishi ,bikine na kece raini,bikin dan sarki wanda yake jinsa a ranshi kaman tsoka daya amiya "

Washe gari ranar asabar aka daura auren nuayma yunus da m adeel muhammad bayero akan sadaki naira dubu dari shima dankyar suka rage sabida abba ya nuna musu albarkan auren ake so ba yawan kudinba"

Bayan daurin aure akayi hawan amarya da ango zuwa yamma inda karfe shida dai dai aka tafi kai amarya nuayma gidan masoyita abun alfaharinta.

So I cut all the weddings formalities"
Lol"

You may continue.

Chuchu.

HALAL VEER √(completed)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant