chapter 44

249 14 0
                                    

Halal veer ❤

Koda tafito daga toilet bataga ladi ba dan haka ta fito parlour tareda kunna tv domin kalan maimaicin shirin da take masifanso na fashion a spice TV"
Bowl din fruit din dake gabanta ta jawo tareda daukan Apple daya wanda suddenly taji tana san ci "
Bite daya ta kaimasa taji ana sallama a kofar dakinta tareda neman izinin shigowa,

Izini tamusu da su shigo inda ladi tafara shigowa domin shaida mata tana tareda  doctor habib "
Koda ta sanar ma da nuayma zuwan doctor habib din shiru tayi tana nazari kan abunda ya kawosa domin idan zata iya tunawa doctor habib likitan masarauta ne "_

Kallonta ta mayar kan ladi tace "baba ladi wane bashida lapia koma ?
Dan murmishin yake tayi tace eh ai mai babban daki ce tace yazo nandin zai dan duba ki,

Shiru tayi na dan mintuna tana jinjina alamarin kafun ta gyara tareda fadin "bakomai shigo dashi"
So take Kawai taga wannan wane sabon abunne kuma "

Da sallama dattijon likittan yashigo tare gaisheta cike da girmamawa ,
Nauyin amsashi tayi dan haka tamayar masa da martani ta hanyar gaisheshi a maimakon amsawa,zuba musu ido tayi tana neman karin bayani ,
Bata gama tsinkewa da alamarinba saida taga ya ciro syringe a cikin jakan da yazo da ita,
Batasa lokacin da ta tsinci kanta da cewa "anya bakuyi batan hanya ba kuwa"

Murmishi doctor habib yayi dan a tunanisa ko tana tsoran allurane dan haka yayi assuring dita da cewa zaibi a hankali after all jini kadan zai diba"

Ai nantake hanjin cikinta yakada tareda wata irin faduwan gaba da ta ziyarceta ,
Jini ?
Mai kuma zaayi da jininta,kar dai asirin masaurata yabiyo ta kanta da har zaazo daukan jininta openly ido naganin ido"

A zabure ta mike tareda fara zazzare idanu cikin in'ina tace m-m-m-ee za-aayi da jinina kuma i don't understand"
Ganin tsoratan da tayine yasaka ladi tadan murmusa tareda cewa ranki ya dade ki kwantar da hankalinki sannan laipinane da ban fada mikiba ,mai babban daki ce tasa yazo ya dauka jinin ki domin zaayi maki gwajin jini"

Shiru nuayma tayi tana nazarin abun,she don't get it at all kaman yaya a auna jininta"
Sanin mai babban dakin bazata cutar da ita bane yasaka ta zauna jiki babu kwari sannan tana gudun kar mai babban dakin taga kaman ta raina umarninta so batareda tasake cewa wani abuba tamika hannunta inda yabi a hankali ya zuga jininta"

Sallama doctor habib yamata tareda fada mata cewa anjima kadan zai bada result ga mai babban daki"

Har suka fita abun bai daina bata mamaki ba amma daga karshe ta dangana hakan amatsayin wata aladarsu wadda bata saniba ta idan mutum ya dawo daga kasar waje sai an auna jininsa anga lapian sa .

Bayan mintina kadan da fitan su ladi tatsinkayi sallaman namiji wanda muryansa kusan daya da adeel ,
Shiru tayi da fari ganin yaki shigowa dan a tunaninta adeel ne da wani sabon salon dan haka ta maida hankalinta kan kallonda take batareda ta bi ta kanshiba "

Kara sallama akai a karo na biyu amma sai wannan lokacin taji ance in-law na shigo ne ko na koma ?
Zama ta gyara da ta tabbatar ba adeel bane sannan ta bada izinin ga mai sallaman kan ya shigo "_
Da faraar sa mai kyau ya shigo tareda zama a kujeran dake dan nesa da ita yace "barka da hutawa auntyn mu "

Tabbas ta gane shi duk da bata taba ganinsa a fili ba sakamakon haduwa da basu tabayi ba amma tasan shi a hoto dan haka cikeda yanayi na wadda kaman ta dade da haduwa dashi tace "abidin yau kai a gari sannu da zuwa"

Dan shafa gemunsa yayi yace "aunt ai ku zaace ma yau ku agari danni na dade a nigeria beside naso kaimuki ziyara uk but nafara running asibitina ,
So to cut it short I'm here with your gift dama ban baki na aureba yanzun gana gama school so --
Ya karashe maganan tareda aje mata dan box a kan hannun kujeran da take "

HALAL VEER √(completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang