chapter 45

290 20 2
                                    

Halal veer❤
Cikeda rudani ya kalleta yana kada kai yace "nuayma no"
Please no"_
Kar ki min haka,nasani i did you bad amma babu ruwan abunda ke cikinki dan Allah kar laipina ya shafi babyn mu"

Wani side smirk tayi tace aw yau kuma sabida abunda kakeso for a long time a jikina ya bayyana shine zaka na wani nuna farin cikinka desperately?

Tsk tsk little prince kayi murna da farin ciki a banza dan haka shawara daya zan baka ba biyu ba shine ka ma yi kamar bakaji cewa inada cikiba ,
Kai ba kai kadai ba har wadanda suka mun katsalandan a rayuwa yakamata su sa a ransu cewa nuayma batazo da ciki gidannan ba domin wannan ciki da kake gani sunansa zubabbe "

Wani zaro idanu yayi lokacin da tafadi hakan inda itakuma ta daga masa gira daya tareda sake fadin "yes zubabbe domin am aborting this child,
Idan na haifa jininkama sunana yar iska kenan"
Kai dan Allah a tunaninka farin ciki zanyi sabida ina dauke da cikinka?
Gangan ma kenan"

Hannunta tasaka guda daya tana tapping kirjinsa tace "keep on dreaming spark "
Keep on dreaming "

Jakanta ta dauka har ta kai bakin kofa ta juyo tace oopz na manta zanje gida duk da i told you amma wai kasake sani kar na fita malaiku suyita tsine mun "
Da haka ta sakai tafita tareda barinshi kaman dolo a gurin
Lokaci daya kuma abunda ta fada suka fara dawo masa ,kada kansa yayi cikeda rudewa yace no she can't do this to me , bai masan unknown hawaye sun fara fitar masaba ,
Bai kara gigicewaba sai da yaji karar fitar motarta ,

Car key dinsa ya fincika tareda fita da gudu gudu dan take mata baya domin gani yake idan ta fita zataje ta cire masa cikinsa ne wanda idan duka duniya zata hadu bazai yarda ba "
Yayi saa kuwa yana fita ya hango ta tana hawa babban titi ,binta ya farayi abaya wanda saida yazamana mota biyu ke a tsakaninsu amma yanayin gudun da takeyi shine abunda yake kara bashi tsoro ."

..........tunda ta hau kan babban titi ta taka kan motan amma abun mamaki motan yafara mata wasu funny abubuwa wanda ta kasa gane kansu ,
Yes funny abubuwa domin a iya shekarun da tayi tana tukin mota tasan zaiyi wuya mota ta bata kashi saidai in wani ikon Allah,

Gani tayi funny thing yana kokarin zama gaskiya so a take tafara kokarin taka burki dan tayi duk yarda zatayi motan yayi slowing down yaki and wani abun mamaki shine burkin motar ya bace ,
Tirkashi ita dai tasan tana hawa maserati din ummi kuma lapia lau akwai burki to whats wrong with this ?
Motar dake gabanta taga ta nufar ma haikan da nakin dan haka ta kama sitiyarin motar domin kaucewa motar wanda hakan yayi dai dai da kwace mata da motar tayi tareda yin kiss da wata katuwar katangar makaranta"
A take balloon ya fito amma a banza dan tariga ta bugi kanta da karfi inda da taimakon glass din motan da ya fallatsa cikin motan wanda ya haifar mata da zubar jini"

Kaman a marfarki taji ihunsa inda a take kuma komai ya koma mata blank and black..

*****************************************
Sarkin yaki ka tabbatar wannan yaron naka da ka kawo yayi aikinsa yarda ya kamata"?

Washe baki mutumin da aka kira da sarkin yaki yayi tareda kamo hannun yaron nasa da aka ambata yace "ranki shidade na yarda da aikin zaki dari bisa dari domin ba yau yafara mun aikiba daga kisa zuwa kan duk wani kazamin aiki dan haka kar kiji wani wai ko dar aikinki kaman anyi angamane"

Juyowa tayi daga bayan da ta basu tace yayi kyau zan tura maka kudi a account dinka sai ka sallameshi sannan kasani wannan abun yazama daga ni sai kai sai shi wannan zakin ,
Kar ka kuskura naji sunan gwaggo amarya ya fita abakin kowa sabida idan hakan yafaru zaka mutune kuma mutuwa mai tsanananin radadi"

Alamun zip yayi da hanunsa a bakinsa inda itakuma ta kada kai tareda fadin zaka iya tafiya "
Suna kokarin fita Abba yana shigowa kallon kallo sukabi da juna kafun suka matsa masa yashigo.
Kallon mahaifiyar tasa yayi yace mai wannan tsohon shuumin kuma yake a nan,
Hade rai tayi dan kar ya fahimci wani abu tace kace kome zanyi yanzu sai nafada maka tunda kaine ubana to taimakon da muke ma marayu duk shekara yazo mu tattauna akai"

HALAL VEER √(completed)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora