chapter 50

245 13 0
                                    

Halal Veer

Zaman gidan taji ya isheta sakamakon bawa ladi hutu da adeel yayi atleast datana nan zasu dan yi hira ,
Shiryawa tayi ta dauki malullubi dan zuwa sashen Fulani tasan kewan zai ragu koda hira ne tayi taji dadi ,

Bayi masu gyaran gida ta iske a harabar gidan ,a tare suka zube domin kwasan gaisuwa ,baban abunda ta tsana kenan,
Amsasu tayi tareda yin gaba abunta "

Tana kokarin fita a gidan wani dakare yakaraso cikeda girmamawa yace "ranki shi dade kafun yarima yabar garinan ya gargademu sosai akan duk inda zakije mu baki tsaro ,
Kallonsa tayi ta dafe goshinta in frustration itafa last thing abunda ta tsana shine takura"

"Katafi banisa zanyiba "ta umarcesa"
Ranki shidade kimin afuwa "
Ya kara nacewa "
Cikeda fushi tace "inace nidai nace maka katafi ko"i don't need any bodyguard nan da nan din da zanje,?
Gaba tayi tana cewa "Allah ya taimakeka naga ka biyoni kagani"

Baiyyi gangancin binta dinba dubada bai taba ganinta tayi irin wannan fushin da kowa ba "

Tsaki tayi lokacin da ta tabatar baya binta kafun ta dauki hanyar da zata sada ta da sashen fulani"

Kamar daga nesa ya hangi gilmawarta "ai baiyyi wata wata ba ya dauki kokaran da bafaden da ya aika ya aje yayi gareta a sukwane ,
Koda ya isa gareta saida yasaka hannu ya tabata tukkuna,
A zabure ta juyo amma kafun ta furta wani abu koma ya antaya mata gora a tsakiyar kai"
Yana ganin ta zube a kasa sumammiya ya arta a nakare "

Wata kuyangar fulani da abun yafaru akan idanuntane ta kwasa da gudu tayi gun fulani domin sanar da ita abunda idanunta ya gane mata "
A take Fulani ta fito hankalinta a tashe tana kiran sunan nuayma wadda ke sheme a kasa bata ko motsi"
DA gaggawa tasaka akira mata abidin wanda ta baro a uwar dakinta yana bacci .
Koda yafito yaga nuayma kwance a kasa kanta na jini bai tsaya wani neman karin bayaniba ya kwasheta domin kaita asibiti da gaggawa .

***
Zagaye kawai fulani da abid suke a kofar dakin da aka kwantar da ita inda likita kuma ke duba lapiar kanta kafun afara mata aiki domin badaban su din bane bama babu yarda zaayi yatabata har sai anje anyi hoton kanta amma kasancewar mai asibitin kankat ya kawota da kansa babu yarda zaayi yace sai anbi wasu procedures"

Kallon abid fulani tayi da damuwa tace abid bazaka shiga kaduba halin da take cikiba kuwa "
Kama hannunta yayi cikeda karfin hali yace "ammi just calm down okay "
Wannan ba bangarena bane amma i trust doctor lakum insha Allahu komai zaizo da daidai ,
Amma tukkunna ma ammi who did this "

Share kwallan da ta taru a idanunta tayi tace wanene fa idan ba wannan yaron ba sayeed ,kasan babu mai aikata wannan danyan aikin idanu na ganin ido idan bashi ba ni yanzu damuwata daya bansan mai za'a fadawa adeel ba ,but promise me bazaka fadamasa ba tunda ba dadewa zaiyyi ba zaidawo kar mu raba mashi hankali biyu "
Kada mata kai yayi alaman to kafun ya mike yana ayyana maima zaiyyiwa sayeed idan ya rikeshi "
Kaman fulani tasan tunanin mai yake tace"abid nasan halin zuciyarka to na rokeka karkaje ka tsare yaronnan kabari babanku zai dauki mataki da kanshi dan already nasaka aje a fada mashi ,banisan abunda zai hadaka dashi komai kan kantarsa '

Dunkule hannusa yayi tareda cije baki ,bahaka yasoba baiso ammi tasaka baki cikin abunnan ba da wallahi yau mai kwatar sayeed a cikin gidannan sai ya shirya "
Kada mata kai kawai yayi kafun yasamu guri ya zauna tareda dafe Kansa.

Jim kadan dr lakum yafito daga dakin tareda mika ma abid hannu"
" success bro, but tayi narrow escape fa domin saura kadan yataba brain dinta amma all thanks to the Almighty komai yayi dai dai sannan zata iya tashi a kowanne lokaci,
Man to man hug abid yabashi kafun yafara masa godia domin da ace wani abu yasamu nuayma yasan definitely his brother won't survive it .

****

Wani amsawa taji kanta yayi lokacin datayi kokarin bude idanunta ,
Batayi kasa a gwiwa ba ta budesu a hankali dan ganin inda take ,
Kaman déjà vu haka abun yafara dawo mata,
Kokarin tashi zaune tayi amma takasa jin wani nauyi da kanta yayi"

Don't stress your self nuayma bari na taimaka miki"
Ta tsinci muryar fulani"
Kamota fulani tayi tareda dagata ta zaunar "
Sannu "tafada cikeda kulawa *

Dafe kai nuayma tayi kana ta kada kai alamun yauwa"
A hankali abubuwa da dama suka fara dawo mata tundaga ranar accident dinta har izuwa yanzu da ta dauka hanyar zuwa gurin fulani,
Take abubuwa suka fara hadewa a kanta ,
Babu Kalmar da ta ke mata yawo akai kaman ruwa face "

"Bantaba tunanin zakaci bet din auran nuayma ba"
Lokaci daya komai dayafaru ya dawo mata ,wani ihu tasaka sakamakon jin kanta datayi kaman zai fashe daganan batasake sanin meke faruwa ba,

Hankalin fulani sosai ya kara tashi inda babu shiri tafara kiran numbern abid wanda bai dade da fita ba adakin,
Koda tagama fada masa abinda ya faru baiyi kasa a gwiwa ba wajen zuwa ga dr lakum dan sanar dashi abunda ke faruwa ,

Da gudu gudu suka isa gareta domin sake duba lapiar kanta ,wannan karan fulanice kadai tabar dakin amma abidin yakiya,

Bayan sungama bincike da komai ne dr lakum ya saka mata drip din da yayi ma alluran da zai rage mata zafin ciwan kan. nema suje office dinshi yayi domin suyi magana"

Cire glasses dinsa yayi yace Dr abidin karka wani damu she's okay "
Tasamu problem din traumatic amnesia right?
Da sauri abid ya gada masa kai yana san jin karin bayani da gaggawa ,
Cigaba Dr lakum yayi "
So masha Allah tayi regaining memories dinta due to dukan da aka mata aka yau but yanzun zatayi ta famane da migraine  ,the photophobia "and visual disturbance sabida ta daku a kaine ba sau daya ba amma insha Allah that wont be a problem sabida zan dorata akan magunguna and insha Allahu with time zata bari"

Godia yayi ta masa kafun ya koma gun fulani domin shaida mata duk abunda dayake akwai "

******
Tunda suka sauka garin yaji komai baya masa dadi musamman dayakira numbern nuayma ba'a dauka ,
Bai takuraba yayi wanka yaci abinci ya kwanta yadan samu hutu domin washe gari akwai zazzafan wasa dole yana bukata "

Washegari tunda aka fara wasa yake jinsa gashinan dai domin ko kwallo daya bai saka a raga ba inda Allah ya taimaki yan team dinsu daya shine da saif a cikin wasan dan haka wadanchan team din suka ja suma suka ja amma a draw ake har aka tafi half time "_

Dukan kafadansa saif yayi lokacin da yazo inda yake ya dauka ruwa"
Zama yayi ya balle murfin goran yasha fiye da rabi kafin ya kallesa "
What's wrong with you man?

Shafa kansa yayi tare da dan karamin tsaki yace i also don't get it man ,gaba daya hankalina yayi gida domin jikina yana bani wani abu ba lapia ba ,
Nakira nuayma jiya bata dauka ba and yau da safe kafun mu fara wasannan still nakira bata dauka ba ,i called abid shima bai daukaba Ammi kawai nasamu amma tace mun komai lapia lau amma i don't know why nakasa yarda "

Dafashi saif yayi yace"look man tunda kaji ammi tace maka babu komai to babu komai dinne lets just focus akan wasan nan kasan bakaramin mahimmanchi yake dashi ba kasani,kadaina bama kanka negative thoughts .
Gada masa kai yayi in assurance kafun suka tashi domin komawa filin wasan..

...Sungama wasa cikeda nasara sakamakon maganganun saif da ya dauka "
Sosai coach dinsu yayi farin ciki da sakamakon ,
Gagarimin party yayi organizing wanda zaayi a daren ranar amma fafur adeel ya makale kafada tareda cewa shifa yanada urgent  Family issue Da yake bukatansa "

Duk yarda suka so yazauna din babu yadda suka iya sanin halin adeel idan ya kafe akan abu so haka nan suka barshi ya tafi badan sun so ba.

CHUCHU

HALAL VEER √(completed)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz