chapter 51

245 16 0
                                    

Halal veer❤

Yana fitowa daga cikin filin jirgi ya hangi abid wanda yana ganinsa ya karaso fuska dauke da murmushi ya karba akwatinsa kafun yabasa side hug
"Welcome back bro ,how was it"

Dan shafa gefen fuska adeel yayi kafun yace"
It was a success".
Yanada tambayoyi dayake san yayi masa amma sai yabama zuciyansa hakurin ta jure su shiga mota "
Cikeda nutsuwa abid yafara tuka motan shikansa yasan yayan nasa nada tambayoyi da yawa"

Mai yasa nuayma bata daukan wayana"
Ya tsinci kansa da tambayan kaninnasa duk da yasan wannan tambaya sounds smh tunda abid ba a jaka yaka yawo da ita ba"

Sniffing yayi kafun yace "well you deserve to know ,dama ammi ta hana na fada maka abunda ya faru amma right now as we are talking nuayma tana asibiti tho Dr lakum yace a gobe ma zasu iya sallamanta'

Asibiti?
Ya tambaya cikeda tashin hankali,
Mai ya same ta?
Mai take a asibiti?
What happened and why didn't anyone informed me?

As I told you ammi ce ta hana sabida we have got to the bottom of it ,wannan yaron ne sayeed ya buga mata gora akai a hanyanta na zuwa gun ammi,amma dad ya masa hukunci daidai dashi yaturasa palace prison ,
Wai yana ikirarin kan cewa ita taja aka kulle masa mahaifiya "

Dukan gefe kujeran adeel yayi tareda furta "Goddamit"
Shikenan abunda akai masa?
How wish ina kasar nan da wallahi sai yagane shayi ruwa ne dan da sai nayi kasa kasa dashi yarda gobe idan ance masa ga kwaya ma bazai sha ba '
Dafe goshinsa yayi kafun yace "take me to the hospital"

Koda suka isa asibitin tana tareda nusayr suna hira wadda ga dukkan alamu suna jin dadin hirar sakamakon yarda suke darawa ,
Da sarsarfa ya karsa gareta tareda manna ta akirjinsa ,
Ganin abid da nusayr ne kadai yahanata turesa tareda kwada masa mari zazzafa"

Gyaran murya nusayr yayi "
Da sauri ya saketa tareda dan shafa Kansa yace sirikina sannu da kokari "
Kada kai nusayr yayi yace "yauwa sirikina naga alamun baka kula dani bane shiyasa nayi gyaran murya ko asan dani mu gaisa "
Dariya abid yayi tareda mika ma nusayr din hannu suka gaisa ,
Atare suka tashi suka fita wanda hakan yabama adeel daman zama a kujeran da nusayr yatashi wadda take daf da ita ,hannunta yakama yayi kissing kafun yace"
Hayati I was scared and I miss you so dearly ,how's our baby"

DA zafin nama ta kwace hannunta tareda hade rai "
Don't you ever dare call me hayati again sabida I am not your life ,you better get that stick to your head and secondly stop dreaming about holding this baby or what so ever, kayi kokari wajen taking advantage nawa lokacin da memory na ya dauke amma not again honey,
Wannan chance din ya karemaka so just get my fucking divorce letter kafun nabar gurin nan and yanzunnan kafitamun anan banisan ganinka_
You're a cheat"

Wata irin uwar zuface tafara keto masa lokaci daya"hakan yana nufin nuayma ta tuna memory dinta like for real?
Tirkashi "
Ana wata ga wata "
Jiki a sabule yatashi ya fita a dakin domin yasan babu abunda zai fada mata ta saurareshi duk zakin harshen sa "

Abid na ganinsa yayi ma nusayr sallama tareda isa gareshi ,
Saurin kauda kai yayi ya goge kwallar da yake kar abid ya gani"
"Bro harka fito kenan"
Muryan abid ya ziyarcesa "
Gaba yayi tareda cewa "eh mutafi gida i need to shower naga she's okay na dawo anjima"

He ain't getting it sabida tabbas yaji muryan yayan nasa kaman wanda kuka ke shirin kwacewa amma bai tsaya dogon bincike ba yabi bayansa domin zartar da umarninsa .

**********
Bayan kwana biyu

Yau yakasance ranar da zaa sallami nuayma amma fafur adeel yaki zuwa domin shi tsoran ma haduwa yake da ita shiyasa tun ranar da yaje bai kara komawa ba wanda hakan ba karamin damunsa yayi ba".

Tayi tayi tabi ummi da tazo amma ummi taki tace ta zauna gidan ta kamar yarda tayi the first time ,babu yarda ta iya dole ta hakura tabi su abid'_
Bataji motsinsa ba ko alamunsa wanda hakan ya tabbatar mata da cewa haduwa da itane bayaso sabida yana gudanma maganan saki amma ita babu komai zataje har inda yake"

Wanka kawai tayi ta sake kaya sannan ta nufa dakinsa dan yau duk balai sai ya sake ta dan zata tada masa hankaline wanda dole zai saka ya aikata gidansu don ta kudiri niyan yau gidansu ta kwan,
Taci saa kuwa tana murda handle din dakinsa  ya bude "

Kwance ta tarar dashi yana kallan fankan da ke juyawa a sama ,wani tausayinsa da kaunarsa taji lokaci daya ya kunno kai cikin zuciyarta amma shaidanin da ke hura mata wutar fitina lokaci daya ya goge komai,

Baiji shigowarta ba saidai tsayuwarta da yaji a kansa ,
Mikewa yayi zaune fuskansa dauke da faraa ya kamo hannunta domin zaunar da ita ,
Da karfi ta kwace hannunta tareda matsawa daga kusa dashi da sauri kamar wadda wuta ta taba ,
Cikeda fitina ta fara magana "
Kaga adeel bawai nazo ne muyi wani dogon surutu bane ba ,nazo ne ka mun abunda nake so maana ka sakeni.

Kai wallahi sai kasakeni ko kanaso ko bakaso ni bazan zauna dakaiba sanan ciki idan har zaa iya cirewa a mayar maka jikinka muje asibiti ayi ahakan amma wallahi sai ka sakeni "

Gyara zamansa yayi tareda jin wani chargi mai girma akansa ,
Kara juya abubuwan datake fada yayi akansa da yarda take rantsuwar sai ya saketa,
Yasani cewa yayi mata laipi amma tayi tsauri dayawa gani yake kamar an chanza masa matarsa musamman idan ya tuna zaman da yayi da itana soyayya cikin kwanakin kamar kar ya kare"

Dakai nakefa kamun shiru idan har kacika namijine kai ka sakeni mana wannan wane irin balai ne da maita kasakeni ni kadaice mace a duniya ne ,i don't like you Adeel DA wane word zanfada maka ka fahimci mai nake nufi for crying out loud huh ?
KO saina saka iyayenka cikin maganan sun kwatar mun hakkina tukkuna zaka fahimci bana sanka yanzun"

Da kyar ya bude bakinsa yace
Baxan sakeki ba nuayma ".

************
Nuayma menene damuwankine?
He is your legal husband for God sake🤨
Akwai masu so inke baki so🙄
Yeye girl.

Chu chu❤

HALAL VEER √(completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora