Oct 17, 2020
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: Calmlubna@gmail.com
Wattpad: Lubna Sufyan*MARTABAR MU*
*LubnaSufyan*_Free page_
1
January 1985, Kano Nigeria.
Tsaye yake bakin kofar gidan shi da yake haya anan unguwar Fagge, gidan da shine na biyu da ya kama duk a cikin unguwar a shekaru kusan hudu da auren shi saboda halin matar shi Maimuna. Halin da yanzun ya saka shi zullumin shiga cikin gidan, ko da wasa bai hasaso rana irin wannan zata zo mishi a rayuwar auren shi ba, ranar da zai tsaye a kofar gidan shi yana tattaro duk wani kwarin gwiwar da zai iya wajen shiga gidan. Dakyar ya iya sauke numfashi yana taka cikin soron hadi da shiga cikin gidan da sallamar da yasan ba lallai bane ta amsa.
A zaune ya sameta kan kujera a tsakar gidan tana yanka alayyahu. Jikinta sanye da atamfa mai zanen tabarma da ta karbi farar fatarta, bakin nan dauke da janbakinta ja da a lokacin ko baka maya saka shi ba sai yai kwanaki biyu kan labbanka da alamun shi. Tayi mishi wani irin kyau, duk da cikin jikinta yasa kuraje fitowa a fuskarta. Ahmadi ya kasance cikin jerin mazan da kance
"Farar mace ko da mayya ce..."
Indai zasu samu suna so, tun bayan mallakar hankalin shi daya dora idanuwan shi akan Maimuna yasan tana cikin jerin matan da yake son kasancewa da ita har karshen rayuwar shi. Shisa baiyi nauyin bakin fadin yana son ta ba, da yake ahalin Dikko gabaki daya abune mai wahala daga mazan su har matan su ace gashi yau sun fita daga gida sun auro bare. Koya ka shiga gida ka duba miji da mata sai ka samu wata halartacciyar alaka ta jini a tsakanin su. Ita kanta Maimuna din da shi Ahmadi dan mace da yar namiji suke, iyayen nasu ma in aka duba duka cikin ahalin Dikkon ne, ta bangaren mahaifiyar shi abokiyar wasa ce, ta bangaren mahaifin Ahmadi kuma Maimuna 'ya ce a wajen shi.
Da yake su din boko ta shige su, sai aka dinga jinjina karancin shekarun Ahmadi duk da bayan karatun da yake shekarar shi ta karshe lokacin yana da tsayayyen hanyar samun shi ta kasuwancin takalma na manya da yara da Babban Yayan shi Ayuba ya saka shi a hanyar yi tunda kasuwanci ne silar arziqi kuma abin tinqaho ga ahalin Dikko gabaki daya. Ko da aikin gwamnati ka sami wani namiji nayi inka duba sai kaga ya hada da kasuwanci ko yayane. Hakan yasa ba'aqi bashi auren Maimuna ba. Amman surutun ya kara samo asali da Yayan Ahmadi wato Bala da yake nashi kasuwanci a asalin tsatson su wato jihar Katsina da bai ko da maganar aure ba.
Amman wata goma cif bayan auren Ahmadi da Maimuna kowa ya fara sambarka, ba'a maganar komai sai albarka da take cikin auren wuri, gasu yanzun da dansu da yaci sunan Mahaifin Ahmadi din wato Mutaqqa suke kiran shi da Khalifa. Lokacin ne kuma Ahmadi ya kammala karatun shi da yake a bangaren lissafi inda aka tura shi yin bautar kasa a jihar Katsina. Ga albarkar kyautatawa iyali da yake gani ta wajen nasara kan duk wani al'amari da zai saka a gaba.
Da yake Maimuna tana cikin matan da suke haihuwar da Hausawa kan kira gwarne, cikin yarinyarta ta biyu Zubaida ya shigane ko watanni takwas cikakku Khalifa baiyi ba, wayewar da suke da ita yasa suka dauki shawarwarin likita, Khalifa da lafiyar shi dimir har aka yaye shi. Yanzun ma tana shayar da Zubaida lokacin da ta sami ciki na ukku da yake a jikinta a yanzun. Da tsohon cikin Zubaida dole suka tashi daga gidan yawan da yake haya saboda rikicin da aka kwasa tsakanin Maimuna da daya daga cikin yan hayar.
Sai bayan auren su ya fahimci ita din bamai hakuri bace ba, akan magana kalilan ma bakinta baya shiru. Dole ya samu wannan gidan mai daki biyu da suke a ciki yanzun suke zamansu su kadai, daman saboda tunanin bautar kasar da zai tafi da zaman kadaici da bashi da dadi shisa ya kama cikin mutane. Yanzun ma dai komai ya kusan zuwa karshe tunda tun kafin auren shi da Maimuna yana da filin shi da Yaya Ayuba yasa ya siya kusa da gidan shi. A cewar shi su kadaine maza da suke gari daya cikin yaran Alhaji Mutaqqa, shi Bala yana Katsina, kuma acan yake zaune da matar shi bayan auren shi. Ya kamata ace suna kusa da juna.