Jan 1, 2021.
27
Ko sallamar Abbu daya dawo daga masallaci kan shi tsaye ya nufo bangaren ta bataji ba. Zuciyar shi na wata irin dokawa ganin ta rike da Rayyan din
"Rayyan..."
Ya kira muryar shi na fitowa yar karama saboda tsoron da yake ciki.
"Me ya same shi? Me ya faru?"
Saboda ya ga fitar Rayyan din daga dakin shi, kuma lafiya kalau ya gan shi. Baisan me yake a kwance haka kamar gawa ba. Ayya da sai lokacin hawaye masu zafin gaske suka zubo mata ta dago tana kallon Abbu, bakinta take so ta bude tayi magana amman ta kasa, saboda zafin da zuciyarta takeyi. Ta dauka raba soyayyar Abbu shine abu mafi daci da zata dandana a zaman duniyarta gabaki daya. Saboda Abbu ne komai nata, sai yanzun da take tunanin inda Bilal ya nufa a cikin duniyar da babu aminci, a rayuwar da naka ma da wahala ya taimaka maka balle wanda baka sani ba.
Kafafuwan Abbu har rawa yake sanda ya kara bandaki ya dibo ruwa ya dawo. Da kan shi ya tsugunna yana dibar ruwan a hannun shi ya shafama Rayyan a fuskar shi, sai da yayi hakan kusan sau biyar sannan Rayyan din yaja wani irin numfashi mai nauyi yana mikewa gabaki daya
"Bilal"
Ya kira daga lungun zuciyar shi yana kallon Abbu
"Abbu tafiya yayi... Bilal tafiya yayi"
Cike da rashin fahimta Abbu yake kallon Rayyan din, kafin ya maida duban shi kan Ayya da ta saka fuskarta cikin tafukan hannunta tana wani irin kuka marar sauti, bayani yake so wani yayi mishi yanda zai fahimta. Dube-dube Rayyan yayi yana dauko takardar da Bilal ya bar mishi da take can gefe ya mikawa Abbu, sai da ya karanta babu adadi kafin kalaman su zauna mishi. Baiyi magana ba ya mike tsaye, aljihun shi ya laluba yana zaro wayar shi da sabo ya saka shi daukarta ya zira bayan yayi alwala zai fita masallaci.
Jikin shi babu inda baya bari, dakyar ya iya saka lambobin sirri ya bude wayar. Sakkoni ya gani da hannun shi ya dangwalo batare da yayi niyya ba. Ganin sakon Bilal a sama ya saka shi saurin budewa:
"Kayi hakuri Abbu, ka yafe mun dan Allah, watakila zan samu sauki a duk inda rayuwa zata jefani. Ka yafe mun ban rike amanar da ka bani ba, ban kula da Layla yanda nai maka alkawari ba. Nagode da karbata da kayi, nagode da yanda ban taba jin maraici a karkashin kulawar ka ba. Ina fatan nisan da zanyi ya saukaka muku komai"
Sosai Abbu yake jin kan shi na sarawa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya furta yana saka Rayyan saurin fadin
"Menene Abbu? Ya fada maka inda yaje?"
Ya karasa yana mika hannu ya karbi wayar da Abbu ya miko mishi, karanta sakon yakeyi wani abu na tattarowa yayi mishi tsaye a kirjin shi, dago idanuwa yayi yana kallon Abbu cike da wani yanayi
"Amana ka bashi Abbu? Me yasa?"
Saboda bai ga dalilin da zai sa Abbu yace ya bashi amanar Layla ba, sun san yanda Bilal yake, su dukan su kowa yasan raunin Bilal,yanda bashi da wani aiki sai kula da kowa, furta kalaman ba zaiyi komai ba sai dora ma Bilal din wani nauyi da Rayyan bayajin Abbu ya fahimta
"Abbu ko bakace ba, ko baka furta da bakin ka ba Bilal zai kula da ita da duka zuciyar shi, me yasa ka dora mishi nauyin nan? Kaga ya tafi, saboda yana tunanin ya kasa sauke nauyin amanar daka bashi ya tafi... Kasa ya barni"
Yanda Rayyan din yake magana kamar ba a cikin hayyacin shi yake ba, wanda zai dora ma alhakin tafiyar Bilal yake nema, bai sami kowa ba sai Abbu a yanzun. Dube-dube yakeyi ganin Abbu ya sadda kan shi kasa ya kasa cewa komai, har saida ya hango wayar Ayya sannan.
Idan Bilal ya turoma Abbu sako, tabbas itama yasan ya tura mata, watakila ya fada mata inda zashi ita. Yana dauka yaga ko password babu ita, dan haka kanshi tsaye wajen sakkoni ya shiga, ya kuwa ga Bilal din ya turo mata itama: