19

7 0 0
                                    

Dec 12, 2020

19

Har ta sauka daga cikin napep din jinta take kamar a wata duniya ta daban. Tayi gaba yayi mata magana

"Hajiya kudin"

Jakarta ta bude, bata san nawa bace ta dauko ta miqa mishi, tayi juya ya sake cewa

"Ga canjin, ko kin barmun?"

Hannu tasa ta karba tana zuba su cikin jakar da ko zageta batayi ba. Ta sha jin kalmar tsiraici, ta dauka tasan ma'anar kalmar, a da ta dauka tsiraici shine ka rabu da tufafin jikin ka, sai yau ta fahimci akwai tsiraicin daya girmi rabuwa da tufafi. Akwai suttura da ba kaya bane kawai yake saka jinta a ranka, haduwa take da mutane a hanyar hostel din, musamman da ta shiga, sai ta tsinci kanta da jan mayafinta tana kara gyara shi, babu inda yake bude a jikinta, amman jinta take kamar bata saka komai ba, kamar kowa na ganin duk wani tsiraici da yake tare da ita.

A daddafe ta karasa dakin su, babu kowa sai Anisa da take zaune akan gadon Layla din, da yake nata saman na Layla ne, in ba lokacin baccinta yayi ba anan suke zaman su, wasu ranakun ma in tayi bacci Layla bata tashin ta. Yau ita batayi lakca ba sai karfe sha biyu na rana. Tana dawowa ruwa ta kara watsawa ta samu waje ta kame ta dauki waya tana dannawa, da yake taci abinci a restaurant, yayarta ta turo mata banner din Zahra Tabiu. Su kan siyi Donut dinta sosai, matar karshe ce, taje gidan Yayar tata ne ta samu Donut, duk a tunaninta na Zahra Tabiu ne, ko da ta fada mata ita tayi sam bata yarda ba, sai da ta kwana taga tayi a gabanta

"Inalillahi... Anty yaushe kika koya? Ina kika koya?"

Murmushi Antyn tayi

"Zahra Tabiu dince fa ta koya kwanaki, kin san nayi saving lambarta saboda siyen Donut, to shine naga tana talla zata koya yanda akeyi online, dubu biyar"

Ware idanuwa Anisa tayi, zatayi abubuwa da yawa da dubu biyar

"Kuma har kika iya haka?"

Tayi maganar cikin rashin yarda, dariya Antyn tayi mata

"Akwai videos haka, sosai ake ganewa, dan su Ammar sun fasa mun screen din waccen wayar dana nuna miki, kiyi joining in zata sakeyi"

Batayin ba ko da Anty ta turo mata, amman duk wani Donut da zata siya sai taji kamar bai kai na Zahra Tabiu ba, shine da safe da ta tashi taga Anty ta turo mata banner din, ta zabtare rabin kudin koyarwar daga dubu biyar zuwa dubu biyu da dari biyar. Gara dai ta koya ta huta, in ta koma gida ta dinga cin kudin Yayyenta, tana da kwalayen Donut Fairy data siya, in sun ce tayi musu order sai ta karbe kudin tayi a gida ta saka a kwalin, in sun cinye tabi ta kwashe. Lambar wayar take dubawa ko iri daya ce da wadda take da ita +234 806 515 6303. Ta gama dubawa kenan ta ga ita din dai ce, sai ga Layla ta shigo dakin kamar an korota. Kallo daya Anisa tayi mata tace

"Layla?"

Tana sauko da kafafuwanta daga kan gadon, tsaye Layla tayi bakin kofar, so take wani abu da zai nuna mata mafarki takeyi ya faru, kamar ace Anisa ta girgizata tana tashinta yanda ta saba da fadin

"Ke banza takwas saura"

A ranakun da suke komawa sallar asuba bayan sun makara. Amman kallon da Anisa takeyi mata ya tabbatar mata da cewa ba mafarki takeyi ba, idonta biyu. Ta dai kasa karasawa cikin dakin ne, kafafuwanta take ji sunyi wani irin sanyi. Ganin haka yasa Anisa ajiye wayar tana saukowa daga kan gadon tazo ta kamata

"Layla? Lafiya?"

Kai ta girgiza ma Anisa da ta kamata tana janta zuwa kan gadon, sai da ta zauna sannan jikinta ya fara bari

"Dan Allah menene? Me ya faru? Ko wani ne ya rasu?"

Anisa ta karasa muryarta na karyewa. Gabaki daya yanayin Layla ya gama daga mata hankali, ta san yanda mutuwa take, Yayanta ya taba rasuwa, ta kuma ga kalar hargitsin da kowa ya shiga, yanayin Layla ya nuna cewa tana cikin matsananci shock da ba labari bane me kyau yake haifarwa. Shisa gabaki daya hankalinta ya tashi

HausanovelWhere stories live. Discover now