Chapter 11

11 1 0
                                    

Nov 23, 2020

11

Kallon Abbu takeyi, bakin shi motsi yakeyi, da alama magana yakeyi, sautin maganar tashi ce bata karasawa kunnuwanta. Sosai take kallon shi tana kokarin fahimtar sauran zantukan da yakeyi tunda ta daina ganewa daga

"....Tare da Layla zasu koma Zaria, itama ta sami gurbin karatu acan..."

Duk abinda ya fada kafin wannan kalaman batajin suna da wani muhimmanci a wajenta, abinda yake fada bayansu kuwa bata ma ji ba sam-sam. Ko bayan nashi bakin ya daina motsi, ta bude nata yafi sau biyar tana rufewa cikin rashin sanin abinda ya kamata ta fadi. Tashin hankali take ciki, irin wanda bata taba hangowa ba, a gaban idanuwanta abinda take tunani ba matsala bane yake zame mata katuwar matsala.

Wanne irin Malami ne wannan mai zafi Mami take da shi, zuwa yanzun Ayya zata iya rantsewa duk wani sirri nata a hannun Mami yake. In ba haka ba, babu yanda za'ayi data like wata kofar sai Mami ta sake huda mata wata. Duka yaushe ta samu kan Rayyan din haka, yaushe ta samu harya dauki waya ya kirata. Wannan zuwan ne har sau biyu da kan shi ya sameta yana gaisheta. Kuma ita da idanuwanta bata ganshi tare da Layla ba, har wani bacci takeyi mai cike da natsuwa a tsayin hutun nan da su Rayyan din sukayi.

Saboda tana ganin duk kudadenta da ta bawa Malam basu tashi a banza ba, aiki yaci. Ashe tana bacci Mami nacan tana wargaza mata abinda ta kashe maqudan kudi wajen ganin ta kulla. Ta rasa kalar bala'in nan, ta kuma rasa yanda zatayi da karan tsaye da Mami tayi mata a makoshi.

"Layla naji kace zataje Zaria... Ahmadi Layla..."

Cewar Ayya tana kallon shi kamar wadda bata cikin hayyacinta, wannan rikicin da yake gani cikin idanuwanta shi yake gudu yasa bai fada mata maganar tafiyar Layla Zaria ba. Wani zaiyi tunanin yana tsoron rikicin Ayya ne, kuma ba haka bane ba, yana gudun abinda zai bata mata rai sosai da sosai. Saboda yasan matar shi, kusan tare da juna suka mallaki hankalin su, babu kalar rikici da shirmen ta da baigani ba tun kuruciya. Ta rigada ta sakama kanta tunanin cewa Mami na bibiyarta, abinda duk zai fada mata kuwa ba sauraren shi zatayi ba, ya sani.

In ba ranar da Allah ya nuna mata tagani da idanuwanta cewa Mami bata bibiyarta ba, ba zata taba cire wannan tunanin daga ranta ba. Shisa ya kasa samun kwarin gwiwar fada mata Layla zataje Zaria. Yasan tunanin farko da zata fara bana cewa Layla da kanta ta zabi Zaria bane, sam Ayya ba zatayi wannan tunanin ba, idan yace mata bada son ran Mami za'ayi tafiyar ba zai ja musu wata matsalar, kishin shi zaisa ta dauka yana kokarin goyon bayan Mami ne, yanzun dole ya nuna mata yana tare da ita dari bisa dari ko dan a samu zaman lafiya

"Eh, ta samu gurbin karatu a can, tana son karantar bangaren yaren turanci"

Abbu yai maganar cikin taushin murya, kallon shin dai Ayya takeyi, kafin wata dariyar ta kwace mata

"Idan dole ya zame mata sai tabar gari zatayi karatu, duk garuruwan da suke cikin Najeriya sai Zaria? Kuma kana kallo kabarta? Me yasa sai Zaria idan ba Rayyan take son tabi can din ba. Na rokeka, Ahmadi na rokeka daka raba Maryama da yarana, na kara rokon ka daka ja nata kunne ta kyalemun ahalina amman kayi biris dani"

Ayya take fadi tana haki saboda bacin rai

"Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Maimuna"

Wani irin kallo ta watsa mishi

"Gayamun kake in kwantar da hankalina? Ka damu da kwanciyar hankalin nawa ne? Ka damu dashi? Da ka damu da kwanciyar hankalina da baka bar Layla ta bimun yaro har Zaria ba... Wallahi sam abin nan ba zai yiwu ba..."

Ayya ta karasa muryarta ba karyewa saboda wasu hawayen bakin ciki da taji sun cika mata idanuwa, hannunta Abbu ya kamo cikin sigar lallashi, ta fisge tana mikewa

HausanovelWhere stories live. Discover now