22

8 0 0
                                    

Dec 17, 2020

22

"Shiru-shiru halina ne Bilal, shisa naka yake mun yawa a kwanakin nan"

Rayyan ya fada mishi, yasan baiyi maganar dan yana jiran amsa ba, ya fadane kawai saboda abinda yake ran shine. In da ya tsammaci amsa ne Bilal din bashi da abin cewa, shiru-shirun da yakeyi ba zabi bane ba, dole ce ta saka mishi. Ya kanji mutane sunyi maganar tsoro, sunyi maganar kwana cikin firgici, yanzun ya gane ma'anonin kalaman su, baccin kirki baya samu sosai. A tsorace yake al'amuran shi, ko kallon shi yaga Rayyan ya cikayi sai yaga kamar yana zargin akwai abu mai girma da yake boye mishi, kamar yana so ya gane cewa yaci amanar shine.

Sanda duk zaiyi waya da Abbu sai zuciyar shi ta doka, muryar Abbu yanzun batayi mishi komai sai kara gigita mishi lissafi. Hirar su da Abbu batayin tsayi, saboda a kagauce yake daya sauke wayar kafin ya fadi abinda baiyi niyya ba. Yana fadama kan shi maganar da Malamai da yawa sukayi a kaine na boye zunubi irin wannan, saboda bayayin komai sai yada rikici da haifar da shakku a zukatan mutane, in dai har ranka zaka tuba saboda Allah, zaka kiyaye sharuddan tuban, to kayi shiru shine mafi alkhairi, Allah ya sirranta zunubinka ne saboda dalilai da dama. Har wa'azin ya lalubo ya saka a wayar shi ko zai saukaka mishi jin nauyin amanar daya ha'inta da yakeyi.

Kwanan shi biyu a asibiti aka sallame shi, duk yanda Rayyan yayi mishi maganar ya huta kafin ya koma makaranta sai ya kasa. In ya zauna baya komai sai tunani, zuwa makarantar na rage mishi tunani, yakan yi kokari sosai wajen mayar da hankalin shi kan lissafin da akeyi. Sai da aka hada sati daya a hakan, kafin ya dauki wayar shi yaga shigowar saqo, ya dauka Aisha ce, dan itace comfort din shi a wannan lokacin, har tausayin damuwar da yakan gani a cikin idanuwanta yakeyi, damuwar da yake da yakinin shine silarta

"Nawan wani abu na damun ka, nasan zaka fada mun inda zaka iya. Amman bana so wallahi, ko menene yake damun ka yana mun ciwo a zuciyata saboda bansan me ya kamata inyi in taimaka maka ba"

Murmushi ya iya yi mata, duk wani abu da zatayi domin shi tana comforting din shine, a lokaci daya kuma tana saka shi jin yanda da duk dakika bai kyauta mata ba itama. Kamar yaci amanar duk tarin kaunar da takeyi mishi. Shisa yake ta wasa da wayar a hannun shi, bai bude ba, jiya ya kasa zuwa ya ganta, ta kira shi da daddare bai daga ba, kuma baibi kiran ba da safiyar ranar, sai ya dauka itace tayi mishi sakon a lokacin, ya fi mintina goma yana tararrabin budewa, sai daya duba yaga sunan Layla sannan wani abu ya tsirga mishi. Tun da akayi abin bai yarda ya sakata a idanuwan shi ba, baisan ta inda zai fara ba.

Jikin shi na rawa ya bude

"Bansan me zance ba Hamma, bansan me zan fada maka ba, har raina ina so in dora laifin komai a kanka ko zan samu sauki, amman na kasa, saboda kana daya daga cikin mazan da suke a rayuwata da nake da tabbacin ba zasu taba cutar dani ba. Har yanzun ina cikin rudani, ban san ko abinda zan fada ya kamata ba, ina so in roke ka, dan Allah karka fada idan kayi niyya, sirrin mu ne mu biyu, kowa zai iya zabar abinda zaiyi da na shi nasani, amman shirun ka shine kariyar karshe da zaka bani. Martabata ce akan layi idan kayi magana, mu manta idan zamu iya, dan Allah ina rokon ka. Ka goge idan ka karanta"

Ya karanta yafi sau goma, yana shirin gogewa ne wani sakon nata ya shigo

"Zamu raba laifin abinda ya faru Hamma, karka dauka duka kai kadai"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da baisan daga inda ta fito ba, duk da bata sauke nauyin da yake ji a kirjin shi ba, ta bude wasu hanyoyi da suka toshe mishi. Ya kasa bata amsa daga lokacin har zuwa yanzun, ya dai goge sakonnin kamar yanda ta bukata. Bashida kwarin gwiwar hada idanuwa da ita, har yanzun idan ya kwanta bai daina addu'ar farkawa ya ga komai ya kasance mafarki ba. Sai dai da duk ranar da zata wuce da yanda gaskiyar komai da ya faru yake kara zauna mishi.

HausanovelWhere stories live. Discover now