Chapter 4

8 1 0
                                    

Nov 1, 2020

04

1993, Kano.

Zata iya cewa tunda Ahmadi yabarta tafiyar nan take shiri, kusan sati daya kenan. Sau daya ta taba tafiya mai nisan awa biyu. Wani lokaci ko da irin hakane, Ahmadi baya barinta

"Tsoro ya miki yawa Maryama... Shisa banason kina nisa ke kadai"

Yakan ce, kuma da gaskene, har tsiya akeyi mata a gida wasu lokuttan, ace da tazo a karkara ba zatayi kyawun gani ba. Dariya kawai takanyi ta kyale su, sau daya kafafuwanta suka taka kauyen Kankia da yake a jihar Katsina, shima rasuwa Mannira ce, matar Yayanta Deeni. Zata tuna yanda aka kai ruwa rana kafin a barshi auren Mannira, na daya bata kasance daga danginsu kamar yanda suka saba ba, duk da yanzun wasu na bijirewa auren dangin. Amman rabon tilar yarinyar su Laila ne kawai ya saka shi kafewa da watsi da maganganun da kowa yakeyi na yaren Mannira

"Ka rasa wa zaka jajibo kana zaune lafiya da matarka sai banufiya, salon duk tazo yanda ta lashe maka kurwa ta lashe kurwar sauran yaran ko?"

Maryama ta tuna maganganun Mahaifiyar su lokacin da yazo mata da zancen auren Mannirar, kowa a dangi da abinda yake fadi, mahaifin sune kawai ya bashi goyon baya, sosai ya dinga fada

"Nayi bincike, iyayen yarinyar nan mutanen kirkine, suna zaune da kowa lafiya. Ita ma nagartacciya ce, addinin musulunci dai shi muke bi, kuma a sharuddan da aka kafa mana na neman aure, bamuda wani dalili na hana shi aurenta"

Hakan yasa dole kowa ya hakura, amman badan anaso ba, yanda yan uwa suka daga hankalin su akan auren Deeni da Mannira, ko matar shi da zai hada zama da Mannirar bata tunanin ta damu haka, ko ita da suka zauna da Deenie suna zancen ta jinjina al'amarin matuka

"Ni banki ka kara aure ba Yaya, da ba'a karawa nima da ina gidan wani ba Ahmadi ba, amman banufiya fa, ka dai kara duba lamarin"

Dan yanda sukayi kaurin suna wajen shaidar da akeyi musu ta maita da tsafi na sanyaya jikinta

"Duk musuluncin banufe sai yayi tsafi"

Haka takanji ana fadi, tana kaunar Deeni har ranta, bata son abinda zaizo ya cutar dashi sam.

"Ke dai kiyimun fatan alkhairi kawai"

Deeni ya fadi yana dariya, sai gashi daga baya kowa na yabon kirkinta. Cikin kankanin lokaci ta shiga zukatan jama'a. Maryama da kowa sun alakanta hakan bayan rasuwar Mannira mintina kadan bayan haihuwar 'yarta mace. Mutuwar ta daki Deeni ba kadan ba, har akayi jana'iza baisan inda kan shi yake ba. Kowa ya budi baki ca yakeyi rabone kawai ya hada kaddarar Mannira da Deeni, shisa duk yanda akaso hana shi aurenta yaki ji, ashe ma zaman nasu bamai tsayi bane, tunda duka watannin su sha hudu. To lokacin ne tafiyar da tayi mai tsayi, shekaru kusan biyu kenan da suka wuce.

Lokaci zuwa lokaci takan yi tunanin yarinyar, saboda tun a wajen rasuwa kowa ya kalleta sai yayi magana kan kalar idanuwanta. Tasan ba kasafai ake samun irin idanuwan a cikin mutane ba, musamman anan yankin Najeriya. Amman sai take ganin gara idanuwan yarinyar da taci suna Layla akan na wani bawan Allah data taba gani, har gobe ko ita kadai ta tuna sai tsikar jikinta ta tashi, saboda sak kalar idanuwan miciji, sai da tayi zaton ko tayi gamo ne. Ahmadi yaita mata dariya, yake cewa a wajen aikin su akwai wani bature nashi idanuwan kalar ganye, koraye ne sosai. To ita kam gara mata bature, wannan ba abin mamaki bane, amman a jikin bakar fata, dole abin ya girgizata.

Shisa da taga Layla ta kara jinjina ma Ikon Allah, dan Shi ya banbanta halitta a tsakanin mutane, bata da kalar da zata misalta idanuwan Layla dashi, ko kyanwa kowacce da kalar nata idanuwan. Amman tabbas ta wata kyanwa kawai ta taba gani da kalar idanuwan yarinyar. Kalar surutun da akeyi tun a wajen rasuwar Mannira, sam Maryama ba zaci za'ayi bakwai yarinyar bata bi mahaifiyarta ba. Tun tana tsammanin bayan dawowar su labarin rasuwar Layla zai iso musu harta daina.

HausanovelWhere stories live. Discover now