Dec 26, 2020.
24
Can nesa Layla take jin duk wata magana da sukeyi, ba zata ce ga abinda ya dinga faruwa ba, daga asibiti, zuwan Abbu, dawowar su gida, banda sautin kukan Mami babu abinda take ji, dan yanzun haka da suke a tsakar gidan ta samu wajene ta zauna a kasa, gefen Mami da ta kasa shiga daki ta durkushe a wajen. Kuka takeyi kamar ranta zai fita, dan har yanzun ta rasa ta inda zata fara yiwa Abbu bayani, sanda yazo asibitin ta farfado, dan haka suka dawo gida, ita da shi a mota daya, sai Jabir daya kama hannun Layla yana sakata a motar da suka zo suka taho.
"Wai dan Allah wani a cikin ku ya bude baki yayi mun magana, tun dazun na tambaye ku abinda ya faru"
Abbu yake maganar da wani yanayi a muryar shi, hankalin shi a tashe ya same su asibiti, sai dai lokacin harma sun fito, tun daga can kuma Mami take kuka, sau daya ya tambayeta abinda ya faru, da bata amsa ba sai yayi shiru saboda bayason su fada mishi abinda zai saka shi kasa yin tuqin su iso gida.
"Layla me ya faru? Wani abin suka ce ya same ki?"
Ya karasa tambayar yana kallon Layla da ta dago idanuwanta tana saka su cikin na shi, bata san me zata ce mishi ba, saboda har yanzun wani irin shiru take ji cikin kanta. Kafin jikinta gabaki daya ya dauki bari, zuciyarta na soma dokawa, girman abinda yake faruwa da ita yana danneta, so take ta bude bakinta, ba ta dan ta bawa Abbu amsa ba, sai dan ta kira sunan Allah, ta furta kalmar
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ko zata samu sauki, ko Allah zai kawo mata dauki abinda yake faruwa ya zama mafarki, amman ta kasa, Abbu kallon shi ya mayar kan Jabir da karo na farko a duniya yake son kasancewa ko ma ina ne da cikin gidan, banda fuskantar abin nan da yake faruwa da su
"Abbu karka tambayeni, dan Allah karka sa in fara fada maka"
Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, zuciyar shi zafi takeyi, so yake yabar wajen, amman ya kasa, ba kukan Mami bane baya ci mishi rai, tunanin halin da Abbu zai shiga ne yake hautsina mishi lissafi.
"Ciki gare ta, cikine a jikin Layla... Ahmadi ciki"
Mami ta karasa tana jin kamar ana zare mata rai, ya kusan mintina biyu maganganunta na yawata mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, so yake ya ga shin shi kadai ne yake ganin wani duhu-duhu ko kuma garin ne gabaki daya ranar da ake kwallawa ta lumshe, amman da ya bude wannan karin ma duhun ya sake gani, kamar a cikin duhun wani abu na jujjuya mishi. Ba dan Bilal daya fito daga bangaren Ayya da kofi a hannun shi ba, ya hango su ya fara karasowa in da yake ganin kamar Abbu na shirin faduwa, yanayin da ya saka shi yin jifa da kofin zobon da yake rike da shi ya karasa ya tallafe shi yana taimaka mishi ya tsaya kan kafafuwan shi, tabbas da zancen ya bambanta
"Subhanallah, Abbu..."
Bilal ya kira zuciyar shi na wani tsalle cike da tashin hankali, Abbu kuwa kafadar Bilal ya dafa yana samu ya tsugunna saboda kafafuwan shi da suke rawa, kokawa yake da numfashin shi saboda tashin hankali, baiga ta yanda Mami zata ce mishi Layla na dauke da ciki ba. Kirjin shi na zafi yake kallon Mami
"Maryama ki fadamun abinda zuciyata zata iya dauka... Dan girman Allah, rokon ki nakeyi"
Hannu ta saka tana share hawayen da suke sake zubo mata, ta bude bakinta yafi sau biyar tana rasa kalaman fadi, haka kawai Bilal ya tsinci kan shi da shiga tashin hankali, bai san me yake faruwa ba, amman zuciyar shi duk ta gama birkicewa, hannun shi yaji Abbu ya kamo
"Bilal kaji me tace? Wai Layla ce take dauke da ciki, yata Bilal, yarinyata, amana ta"
Runtsa idanuwan shi Bilal yayi, ya bude su a cikin na Layla da take kallon shi, duniyar na karasa hautsine musu a lokaci daya. Kai ta girgiza mishi a hankali tana neman hawayen da zasu sama mata sauki ko yayane. Amman ta rasa su, sunki fitowa. Tsaye Bilal yake a waje daya, amman duniyar duka juyawa takeyi da shi, kamar wanda aka dauka ana zagayen cikar shekara haka yake jin shi, so yake wani ya taba shi ko zai daina jujjuyawa haka, kamar an amsa rokon shi yaji hannuwan Ayya akan kafadar shi, hannun da yake da yakinin zai gane shi a cikin dubban hannaye.
