Chapter 8

15 1 0
                                    

Nov 14, 2020

08

Da wani yace mishi zai iya shekara daya a wani gari daban, nesa da Bilal, nesa da Layla da bai taba tunanin kewarta zata danne shi haka ba zai karyata. Dare da yawa ya sha farkawa ko shan ruwa da yakan yawan yi ko kuma wani abu daban ya tsinci kan shi da kasa komawa bacci, saboda kawai yana tunanin Layla. Yana tunanin ko tana kewar shi ko batayi, ranar da zai tafi bata neme shi ba sam, yafi mintina talatin a tsaye kofar daki yaki fitowa yana jira ko zata shigo tayi mishi sallama, amman shiru, sai da ya taka ya sameta har bangaren Mami, duk da bai shiga ba a bakin kofa ya tsaya yana kwala mata kira, ko da ta fito sai ya rasa abinda zaice mata.

Lokutta da dama yakan zabi shiru saboda kalaman shi basu da yawa, baisan yanda zai fadi abinda yakeji ba, baisan me ya kamata yace mata ba, shisa ya zabi

"Tafiya zanyi..."

Kai ta dan daga mishi

"Allah ya tsare... Zaka dinga zuwa kaman Hamma Haris?"

Dan daga mata kafadu yayi, yana rasa amsar da ta dace ya bata, abubuwa ne masu tarin yawa a ran shi, ya motsa labban shi kenan ta dago idanuwanta tana saka zuciyar shi dokawa. Ya kasa sabawa da kalar su, kamar yanda ko kan hanya yaga giccin mage sai yayi da gaske ne baya zurawa da gudu. Sanin da wahala ya kara cewa komai ya sata yin murmushi

"Allah ya saukeka lafiya. Banda fada da mutane"

Baisan murmushi ya kwace mishi ba sai da tace

"Inalillahi... Hamma...murmushi kayi ko wani abune ya fadamun a ido"

Kai kawai ya girgiza wannan karin har zuciyar shi da yake ji cike da wani irin duhu a lokutta da dama yaji murmushin

"Kin rainani ko?"

Dariya tayi mai sauti

"Ni na isa"

Numfashi ya sauke mai nauyin gaske, yana kokarin kallon cikin idanuwan ta wannan karin. Ya rasa kalaman da zaiyi amfani da su wajen misalta asalin abinda yake ji. Dakyar ya iya jan kafafuwan shi ya juya yana tafiya. Sanda ya sake waiwayowa sai yaga bata nan. Abin ya mishi wani iri sosai. Yaso ace ta tsaya, yaso ace ta jira shi harya bace mata, amman batayi hakan ba. Bayan tafiyar shi yanayin yana yawan fado mishi a rai, musamman idan yayi kewarta.

A cikin shekara dayan, kusan idan ba karatu bane yayi mishi zafi, duk watan duniya yana hanyar Kano, kawai ya kula da abu dayane a shekarar game da Ayya. Batason yawan zuwan da yakeyi, da ta ganshi zai ga tsoro a cikin idanuwan ta, har magana tayi mishi wani zuwa

"Rayyan ba zaka natsu waje daya ba ko? Taya zaka fahimci karatu kullum kana hanya?"

Cikin idanuwa ya kalleta, yaso ya fahimci dalilin canzawarta lokaci daya amman ya kasa, yawan magana na saka shi ciwon baki wasu lokuttan, kuma idan maganar tai tsayi zaiji ta fara hau mishi kai, shisa baice mata komai ba, har tayi mitar ta gama. Sai da ya mikene tukunna yace

"Zan gaisheki ne daman"

Yana juyawa

"Allah ya shiryeka..."

Shine kalamanta da yaji kafin ya fice daga dakin. Bai fasa zuwa ba, gajiyar da yayi jiya ita ta hana mishi tafiya gida, da ciwon kai na gaske ya fito daga wajen jarabawar shi ta kare shekarar farko a jami'ar. Amman a daren ya hada kayan shi yana ajiyewa, yaji dadin hakan dan yana dawowa masallaci wanka ya shiga. Lokacin da yaje babu yanda Haris baiyi dashi ba da su zauna tare a gida daya, amman yaki. Shi sun kama gidane anan Layin Kasuwa. Da Rayyan ya tashi sai ya nema a Rufasi.

Gidan nasu daki shidda ne, guda daya Abbu ya biya mishi shi kadai, sanin halin shi. Banda sallama babu wani abu da yake hada shi da wani a cikin gidan, sau dayane da akace wani Emmanuel bashi da lafiya za'aje duba shi ya bisu. Acan ya barosu saboda baisan ya zai zauna ayi hirar da suke tayi da shi ba. Sunayen su ma bai sani ba, Emmanuel din saida yaje asibitin ya gane shi. Lokacin da yaje ya sami da yawansu a gidan, suke fada mishi yanda suke tsara shara da wankin bandaki, idan wannan yayi wannan ma sai yayi.

HausanovelWhere stories live. Discover now