18

5 0 0
                                    

Dec 9, 2020

18

Da wani irin ciwon kai ya sauka, ga alamun zazzabi yanaji. Ya kira wayar Layla yafi sau goma bata daga ba. A ranaku da ba irin na yau ba, kira daya idan yai mata bata daga ba shikenan. Ya san in tazo zata kira shi. Amman yau din wani irin tsoro yake ji da bai san dalilin shi ba, tsoron ma bai kara yawa ba sai da ya kira Bilal shima bai daga ba. Bilal da ko karatu yake sai ya mishi magana zai ajiye waya ya natsar da hankalin shi waje daya. Idan jarabawa akeyi ma, kamar yaro haka zai ce

"Ban wayar nan Bilal..."

Zai saka a key ya ajiye yana fadin

"Na ajiye Allah kuwa Hamma"

Sanin halin shi yake saka Rayyan din kin yarda, sako na shigowa zai sake dauka, shisa yakan mike ya dauki wayar ya ajiye a gefen shi

"Kayi abinda yafi danna wayar muhimmanci"

Yakan fada mishi, ya rasa dadin me suke ji shi da Layla kan danne-dannen wayar nan. Ji yake kamar ya tsaya a hanya ya samu wata motar da zata juya da shi Zaria saboda rashin natsuwar da yake tare da ita.

"Allah Ka san halin da nake ciki, Ka san damuwa ta, Ka san zuciyata ba zata iya daukar wani abin ba. Allah Ka sa lafiyar su"

Shine abinda yake fadi yana maimaitawa, duk inda network zai dawo mishi sai ya gwada lambar Bilal da ta Layla, amman duka tana shiga basa dauka ne. Yana sauka a tashar ya tsaya ya kira Bappa da bugu daya ya daga yana sallamar da bai jira Rayyan din ya amsa ba ya dora da

"Har ka karaso ne? Ka jirani a tashar in zo yanzun"

Rayyan din dan dakuna fuska yayi, saboda Bappa nayi kamar sun san juna, kamar sun saba ba yau bane farkon maganar su

"Eh, ok tam"

Rayyan ya iya cewa yana sauke wayar daga kunnen shi, fita yayi daga tashar zuwa bakin titi. Anan yayi tsaye, masu mashin da napep na ta mishi magana, harya kawo iya wuya, ga shi gari yayi duhu tunda sai bayan Magriba suka sauka.

"Alhaji tafiya ne?"

Wani mai mashin ya fadi a karo na biyu, kamar bai ga ya girgizawa mutane wajen hudu kai cikin alamar a'a ba.

"Sai ka daukeni ka dorani, me yasa dole sai kun sa mutane magana ne?"

Jinjina kai mai mashin din yayi

"Allah ya baka hakuri, daga tambaya"

Wani irin kallo Rayyan ya watsa mishi, dai-dai lokacin da wata mota baqa, kirar Honda Accord DC V6 ta tsaya a gaban shi. Gilashin aka sauke daga bangaren da yake, kafin aka kunna fitilar cikin motar haske na gaurayewa

"Rayyan?"

Bappa ya fadi daga cikin motar, Rayyan din na jinjina mishi kai

"Muje..."

Cewar Bappa, hannu Rayyan yasa yana bude murfin motar ya shiga, batare da yace komai ba ya rufe. Bappa ma baice mishi komai ba yaja motar, hankalin shi sam ba'a kan titi yake ba, shi dai yana garin Bauchi, zaune a cikin motar Bappa da sai kamshi takeyi. Amman hankali da natsuwar shi suna garin Zaria. Baisan anyi parking ba sai da Bappa yace mishi

"Mun zo"

Budewa yayi yana fita, in da duk Bappa ya sa kafar shi nan Rayyan yake mayarwa, ko sunan Hotel din bai duba ba, daga yanayin shi bayan sun shiga ya dan gane ko ina ne, ciki suke shiga sosai har suka karasa daki mai lamba 19, inda Bappa ya zaro mukulli daga aljihun shi yana bude dakin. Da sallama ya shiga, Rayyan na biye da shi, ya mayar da dakin ya rufe, akwai haske gauraye da dakin, babba ne da tanqamemen gado sai tv da take ta aiki, amman babu magana, anyi kasa da ita. Har da kujera doguwa a cikin dakin. Yayi kyau sosai da sosai. Ko ina a gyare tsaf, da alama zaiyi tsada

HausanovelWhere stories live. Discover now