Nov 26, 2020
12
Kan shi ciwo yake kamar zai rabe gida biyu. Dan bai iya takawa gida ba, sai da ya hau mashin. Da yake ba surutu yake son yi ba, canjin dari da ya baiwa mai mashin dinma da hannu yayi mishi alama daya tafi
"Allah yasa kar in ga kowa, Allah yasa kar kowa ya ganni"
Rayyan ya furta a cikin kan shi. Bayason mutane, baya kuma son 'yan cikin gidan da suke haya fiye da sauran mutane, saboda suna saka shi yanayin magana a lokuttan da ko kadan bayason yi. Gashi yanzun Bilal yace ya dinga yiwa mutane murmushi idan sun mishi magana, baisan ya zai fara ba, motsa labban shi kawai yakeyi wasu lokuttan, tunda bayajin yin fara'a sam-sam. Ya gaisa dasu, baisan kirkin me Bilal yake so ya dinga musu ba
"Ko rashin lafiya ta kamaka ba fata nake ba, su dinne mutanen farko da zasu taimaka maka tunda kuna gida, kasan abubuwan nan, kasan hakkin makota Hamma"
Bilal din ya fada mishi
"Bana son su"
Shine amsar daya baiwa Bilal din
"Su ma na tabbata ba son ka sukeyi ba. Ka dinga murmushi dan Allah in zaka gaisa da mutane, ka dan saki fuska ba kamar an maka dole ba"
Bilal saiya dinga mishi magana kamar baisan dolen akayi mishi yake gaisawa da su ba. Hakkin musulunci kawai yake saukewa. Kamar barawo haka yake sanda wajen shiga gidan, sam baya so wani ya gan shi. Kusan da gudu ya karasa dakin su yana daga labulen ya shiga da sauri
"Subhanallah..."
Bilal da yake zaune ya bude kular abinci ya fadi, dan sosai Rayyan din ya bashi tsoro
"Assalamu alaikum..."
Cewar Rayyan, amsawa Bilal din yayi yana girgiza kai kawai. Taliya ce da miya sai soyayyen dankalin turawa, rabon su da dora tukunya a wuta harya manta, sai dai ko in sunyi marmarin shan shayi zasu dafa, amman Aysha na musu kokari matuka ta fannin abinci tunda tazo makarantar. Bilal baiyi mishi tayin abinci ba, tunda yasan sai yayi wanka, aikam ficewa daga dakin Rayyan yayi. Sai bayan yayo wankan ya dawo ya sake kayane ya zauna yana mayar da numfashi Bilal yace
"Abinci fa?"
Kai Rayyan din ya girgiza mishi
"Babu abinda kaci fa duk yau"
Tunda tare suka fita, kuma yasan babu abinda Rayyan din zaici a waje banda biskit, idan ya samu kalar wanda yakeci din kenan.
"Zanci sai anjima"
Rayyan ya furta yana kwanciya kan katifar da yake zaune a gefe, sai yaji wani dadi a ran shi daya kwanta din, kamar gajiyar daya kwaso ta dan sake shi. Wayar shi da Bilal ya janyone yaga yau din Alhamis, numfashi ya sauke
"Azumi kakeyi ko?"
Ya tambaya
"Me yasa baka gajiya da surutu? Dan Allah ka kyaleni ni"
Rayyan yayi maganar cikin alamar gajiya. Murmushi kawai Bilal din yayi. Bai taba gane azumin alhamis da litinin baya wuce Rayyan ba sai wannan dawowar da sukayi. Sai yake tuna ranakun da Rayyan din zai wuni baici komai ba, duk surutun da zai mishi. Sai sun dawo sallar Magriba tukunna, ko in yayo alwala ya shigo daki an kira, Bilal zai ga ya sha ruwa, ko yaci dabino. To bai taba kawo komai a ran shi ba, tunda Rayyan na da shan ruwa, kuma dabino kamar biskit ne a wajen shi, da wahala ka raba jakar shi da su, ko cikin kayan shi ka duba zaka samu.
Zurfin ciki irin na Rayyan baya gajiya da bashi mamaki, shima ranar alhamis din daya san azumi Rayyan yakeyi, alhamis din kuma daya tabbatar da abinda ya dade da sani, wajen Rayyan din yaje daga nasu bangaren, ya same shi a can karkashin wata bishiya, inda yake shimfida darduma ya zauna idan basu da darasi ba kuma yason komawa gida. Tunda wani lokaci ko baiyi niyya ba idan ya zauna cikin aji sai an sami wani mayen yayi mishi magana. Ko mintina biyar da isa baiyi ba sai ga Layla da tun daga nesa take fadin
