Jan 12, 2021.
30
Dan ware idanuwa Bappa yayi, yana sake kallon farantin da yake gaban Rayyan a ajiye
"Meye wannan Rayyan?"
Ya bukata, Rayyan din na dan juya idanuwan shi, yasan sarai Bappa ya gane plantain ce, tunda suka kwaso ta da dankalin turawa, sau biyu yaga Bappa ya soya. Abin a ido kamar ba zai wahala ba, sai da yazo tun daga yankawar ya gane aikin ba karami bane ba, da yake man yayi zafi sosai sanda ya zuba kafin ya juya wata, wata ta kusan konewa, gabaki daya sunyi baki, har cikin makoshin shi yana jin daci-dacin da sukayi. Sai dai yunwa yake ji da yake ranar ta zo musu a karshen mako, Bappa din kuma ya fita, yana jin kwiyar zuwa ya siyo wani abu.
"Da me yayi maka kama?"
Rayyan ya amsa tambayar Bappa din da wata tambayar, yana sake saka cokali mai yatsu ya caki guda biyu ya saka a bakin shi yana taunawa kamar babu dacin da Bappa yasan zatayi, dariya Bappa yayi
"Ka tashi mu fita, nima ba abinda naci"
Kafada Rayyan ya makale, bayajin zuwa ko ina
"Me yasa bakayo mana take away ba? Dole sai ka dawo ka fitar da ni"
Tunanin ne bai zo ma Bappa ba sam, saboda yasan halin Rayyan din, bakomai na waje yake ci ba, idan suka fita tare saiya zaba da kan shi, ba'a cika yi mishi gwaninta ba.
"Ka tashi dan Allah, ba kana maganar waya ba? Sai mu biya ka duba"
Dan jim Rayyan din yayi, da gaske yana son siyan babbar waya. Saboda yanzun sukanyi kwanaki har biyu ko fiye da hakan ma tunda ya dawo basuyi waya da Layla ba. Sukan yi musayar text dai, ta cikin su yakan fahimci kamar yanzun tana rasa abinda zatace mishi, idan suka gaisa sai ya jima yana kallon wayar yana jiran yaga amsarta, sai yake tsintar kan shi da tunanin ko tana lafiya ko akasin hakan. Idan ya kira ma wasu lokuttan bata dagawa, ba ko yaushe take biyo kiran ba sai dai idan ya sake gajiya ya kara kiranta.
Yasan zai iya zuwa gida idan yana so, Bappa da wahala yayi kwana biyar bai shiga Kano ba, yawon shi har mamaki yake bama Rayyan din, gidane bayason zuwa, tunanin ya shiga dakinsu babu Bilal yana mishi wani iri. Duk da akwai damuwar da ta daga a kirjin shi baya nufin baya kewar Bilal din, ba kuma ya nufin tafiyar da Bilal yayi bata mishi ciwo, yana dannewa ne
"Zaiyi sauki, In shaa Allah komai zaiyi sauki"
Bappa kan yawaita fada mishi haka kawai idan yaga yayi shiru yana kallon bango. Baya amsawa, baya tunanin Bappa nayin maganar ne dan yana jiran ya amsa mishi. Kawai yanayine saboda yasa shi yaji kamar wani ya damu, kamar yana kula da yanayin shi. Kuma yanaji din, har cikin zuciyar shi yanajin kulawar Bappa da baiyi tunanin wani bayan Bilal da Layla zasu gwada mishi ita ba. Su Ayya iyayene, bayajin akwai zabi a tasu kulawar, kamar da haihuwar shi da yanda kula da shi ya zame musu tilas ko da basa son hakan, ko da ta takaitaccen lokaci ce.
Watakila Bilal na kula da shi saboda su din yan uwane, Layla kuma dan tana son shi. Kusan suma zaice basu da zabi, amman Bappa na da zabi, sai ya zabi kula da shi, ya zabi yi mishi karamci duk da shi din bashida wani abu da zai iya mayarwa Bappa da shi
"Zama da kai ba abu bane mai sauki Hamma"
Bilal ya taba fada mishi da sukayi wani rikici, kuma yasan gaskiya ya fada. Amman Bappa na zaune da shi kamar hakan abune mai sauki. Bappa ya bashi abinda bai taba tunanin zai samu ba a rayuwar shi, ya bashi abota. Satin su biyu da dawowa Kaduna aka koma makaranta, da yake akwai kanin Bappa a ABU din shisa ma Rayyan yasan an koma. Rana daya ya tambaya a wajen da suke serving aka kuma bashi, da yacewa Bappa zaije Zaria da mamaki ya kalle shi
"Me yasa yau? Ka bari sai weekend mana mu shiga tare"
Kai Rayyan ya girgiza mishi
"Akwai abinda zanyi yau din shisa"
