Chapter 14

11 1 0
                                    

Dec 1, 2020

14

Kwance yake yana juyi. Maganganun Bilal ne suke mishi yawo, duk idan ya zauna haka kawai sai su dinga dawo mishi. Baisan me yasa Bilal din zai fada mishi su ba

"Tuntuni ya kamata in maka magana Hamma, tun ranar farko da naga hannun Layla cikin naka ya kamata in tuna maka rashin dacewar haka, in tuna maka yanda tasowa gida daya a karkashin kulawar Abbu bai saka halaccin nan a tsakanin ku ba. Ka daina tabata, idan kana son ta ne kayi wani abu a kai ta zama mallakin ka, amman ka daina..."

Bai amsa Bilal din ba sanda yayi mishi maganar, a cikin makaranta ne, shi yayi jarabawar safe, Bilal din kuma yana da ta azahar, haka ma Layla, baisan dalilin su na shigowa makarantar tun wajen sha biyu saura ba. Layla na karasowa wajen yaji ta riko mishi hannu ta baya, kusan rabin jikinta akan nashi, zai iya cewa ta rungume shine ta gefe

"Hamma..."

Ta fadi cike da wani nishadi da baisan dalilin ta nayin shi ba. Kuma a gaban Bilal din ya bambareta daga jikin shi. Ba zai manta da hawaye tabar wajen ba. Bai tuna rana daya da ya cewa Bilal shi yana son Layla ba, maganar ma wata irin dirar mikiya tayi mishi, tana hautsina wani abu a tare da shi da baisan yana a nutse ba. Yana zaman shi lafiya, yana lallaba rashin natsuwar da yake fama da ita a duk rana, Bilal yazo ya kara mishi wani tunani na daban. Ya saka shi yana neman ma'anar alakar da take tsakanin shi da Layla. Bai saba yawan magana ba, rabin da kwata na maganar da yakeyi a rayuwar shi tsakanin shi da kan shine, a iya tunanin shi maganganun suke makalewa.

Kuma bai saba yiwa kan shi karya ba, yasan yanda yake jin Layla da ban da yanda yake jin su Rukayya, da sai yace ita din matsayin kanwa take a wajen shi. Duk da a ranar ne maganganun Bilal suka saka shi tantance hakan. Shi baice yana son ta ba, bai taba tunanin wata soyayya ba, bayajin yana da natsuwar janyo wata duniyar shi da take a hargitse. Me yasa ma Bilal din zai hargitsa mishi lissafi har haka, yanzun yana saka duk lokacin da jikin Layla zai hadu da nashi sai yaji wani irin tashin hankali na daban. Ya kuma rasa ta inda zai fara hanata rike shi ko da shi bai kokarin riketa ba.

Musamman idan Bilal din yana wajen, sai ya kasa hada idanuwa da shi, akwai tarin abubuwa da Bilal yake nuna mishi bai kamata ba, amman yawancin su tun kafin ya fadi ya rigada ya sani, baisan yanda zai ya bari bane ba. Yawan hada jiki da Layla na daya daga cikin abin da ya kasa gano rashin dacewar shi sai da Bilal din ya tunasar da shi, sai dai kamar ko sa yaushe, ya kara kasancewa cikin jerin abinda baisan ta inda zai bari ba. Bilal ya sake mishi magana jiya, shine magana ta biyu akan abu daya

"Nace maka idan son ta kakeyi kayi wani abu a kai ba zaka saurareni ba wannan karin ma ko?"

Batare da ya daga kai ya kalli Bilal din ba ya amsa da

"Ni bance maka son ta nake yi ba"

Kai Bilal ya jinjina yana furta

"Yayi kyau"

Rayyan zai karya idan yace abin baya damun shi, gabaki daya komai ya kara jagule mishi. Shisa jiya yana gama jarabawar shi ya fita daga cikin makarantar bai jira Bilal ko Layla ba. Amman da tunanin ta cike da kan shi ya kwana, yau ma yana gama jarabawa ya gudo gida. Ya san za taita neman shi. Yana ma iya ganinta tazo gidan. Ko motsi yaji cikin gidan sai ya lumshe idanuwan shi yana jiran yaji shigowar ta, har bayan azahar, ko abinci ma ya kasa ci. Har zane ya fara, amman ya kasa samun natsuwa, mikewa yayi ya dauki riga ya saka a jikin shi, dan ya cire yabar singlet ne sanda ya dawo sallar azahar.

Alwala yayi tun daga gida, saboda kar lokacin sallah ya kama shi a inda ba zai samu ruwan leda da zai alwala ba, ba shi bane zai saka ruwa a butar da baisan rabonta da wanki ba ya kuskura bakin shi, ya kuma wanke fuskar shi ya dauki wasu cutukan. Mikar hanyar da zata hada shi da makarantar su yayi, sanda ya shiga kuwa ana kiran sallar la'asar. Dan haka ya wuce masallaci ya gabatar da sallah yana fitowa, hanyar department din su Layla ya tsinci kan shi da nufa. Yasan ta fito daga jarabawa, tun daga nesa kuwa ya hangota da wasu riga da wando da sukayi mishi kama dana kasar indiyawa, sai dai tsakar rigar har kugunta, ya nade kanta da mayafin da ya rufe iya wuyanta.

HausanovelWhere stories live. Discover now