Dec 26, 2020.
25
Maganganun Ayya ne suke mishi yawo, kafin ya zare hannun shi daga cikin nata, yana kallon Layla da jin an kira sunan shi ya sakata bude fuskarta, idanuwanta har sun kumbura saboda kukan da takeyi. Tana jin su, bata san kalar tunanin da ya kamata tayi ba, duniyar duka take ji ta hade mata waje daya. Ta rasa da wanne zata fara, tashin hankalin abinda yake faruwa da ita karon kanta, halin da su Mami suke ciki, Abbu da take ganin ba zuciyar shi kawai ta taba ba, harda Martabar shi, ko kuwa Rayyan da take ji suna lakabama laifin da ba nashi ba?
Ko yanzun da yazo yake kallon ta, yake neman amsa a cikin idanuwanta, a hankali take ganin yanda komai yake shirin canzawa a tsakanin su. Duk a cikin abinda yake faruwa shi tafi ji, shi tafi tunani, in zai rike hannunta, ya kasance da ita, hargitsin zai mata sauki, amman tana ganin yanda wasu katangu suke fara ginuwa a tsakanin su, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata, tana runtsa idanuwanta ta bude su a kan Rayyan. Dan kallon ta yakeyi, wannan karin ta cikin idanuwanta yake son tabbatar da gaskiyar abinda kunnuwan shi suka jiye mishi kafin yasan matsayin kalaman a zuciyar shi, kamar ciki yaji ance tana da shi, kamar ji yayi ana kiran cikin da yake jikinta da nashi.
"Hamma..."
Labbanta suka motsa, muryarta sam bata fito ba, amman shi yajita a cikin kan shi, yaji ta a cikin zuciyar shi inda wani abu yake bubbudewa da ciwo na gaske
"Rayyan..."
Yaji muryar Ayya da take kallon shi cikin tashin hankali, saboda shirun shi yana nufin abubuwa da dama, shirun shi yana nufin daukar laifin da ake so a makala mishi, bata san lokacin da ta kama hannun shi tana jijjigashi ba
"Kana da matsala kala-kala tun tasowar ka. Rayyan ka bude bakin ka kace mun ba kayi ba, ka fada kowa yaji wannan matsalar ba taka bace ba"
Wani abu yake ji tokare da makoshin shi, amman baisan ta yanda zaiyi ya hadiye shi ba, bakin shi ya kafe kamar ya kwana biyu bai sha ruwa ba. Baisan yanda akayi jikin shi baya rawa ba, saboda gabaki daya zuciyar shi jijjiga takeyi tana rarrabuwa sashi-sashi.
"Ciki aka ce... Rayyan ciki. Ciki ake magana a kai ba abu na wasa ba"
Ayya ta karasa muryarta na karyewa, idanuwanta sun fara cikowa da hawaye saboda tashin hankali. Dan daya fito daga cikinta ba zaiyi wannan barnar ba
"Rayyan"
Ta kira cike da roko wannan karin, hawayenta na zubowa, kallonta yayi cikin ido, abinda yakan dade baiyi ba, kafin ya kama hannunta da yake damke da nashi ya sauke. Kan Layla ya sake sauke idanuwan shi da suke cike da tarin tambayoyin da baisan ta inda zai fara yi mata su ba, guda daya yake so tayi duk yanda zatayi ta amsa mishi duk da bai furta a fili ba, da dukkan muryar zuciyar shi yake tambayar
"Ciki gare ki? Cikine a jikin shi?"
Bata san ya akayi ba, amman ta fahimci neman tabbaci Rayyan yakeyi, kai ta dan daga mishi a hankali, wasu hawaye na zubo mata. Hawayen da suka hana ta fara ganin wani yanayi da bata da kalmar fassara shi cikin idanuwan Rayyan din, kafin ya dauke idanuwan shi daga cikin nata. Numfashi yake fitarwa a hankali a hankali saboda yanda yake ji kamar baya shiga inda ya kamata, kamar yau akwai abubuwan da suke cunkushe mishi hanyar shiga da ficen iska. Juyawa yayi da nufin barin wajen ko zai samu maganar ta natsa mishi da kyau, ko zai tattara hankalin shi wajen gane girman da maganar take da shi, karfin da yake tare da maganganun da yake barazana da dan zaman lafiyar daya fara samu a duniyar shi.
"Rayyan..."
Wannan karin muryar Abbu ta tsayar da shi cak, tana kuma saka shi juyowa ya kalli Abbu din ido cikin ido
"Ka ce baka taba mun amana ta ba, ka bude bakin ka kayi mun magana"
Wani numfashi Rayyan yaja a wahalce, bashi bane ba, ko zai taba Layla, ba zai taba zama ta wannan fannin ba. Ko kwayoyi yasha ba zai taba ta haka ba. Saboda tunanin abinda yake faruwa yanzun, saboda yanda mutanen da suka fi komai muhimmanci a rayuwarta ne zasu fara dora ayar tambaya akan ta, kafin mutanen da basu taba bada gudummuwar komai wajen tarbiya, ci, sha da sutturarta ba su fara zagayawa da maganganu kala-kala akanta, akan Martabar gidan su. Shisa bayason mutane, wannan halin shine, ko kadan baya son su. Mutanen da yake so basu da yawa, saboda matsalolin da suke tattare da mutane yawa gare su.
