14 Dec, 2020
21
Su Ayya basu isa Zaria ba sai wajen bakwai da rabi, dan ma yau a karo na farko ta ga Abbu ya taka mota sosai. Wajen su Rayyan suka fara biyawa saboda Ayya, maganar farko da Abba ya fara bayan sun shiga dakin shine
"Me yasa zaku kawo shi wannan asibitin? Baku san na makaranta yafi kowanne kyau a Zaria ba? Kuma sai yafi samun kulawa fiye da ko Ina"
Kallon shi Rayyan yayi kafin ya sauke kan shi, saboda shi dai asibiti yasan Bilal yana bukata, ko da asibitin kauye aka kaisu a daren jiya in dai zasu iya bawa Bilal din wani taimako a halin da yake ciki zai barsu. Bai iya magana ba saboda kan shi da yayi bala'in nauyi, ga ganin Abbu ya kara mishi nauyin kan da yake ji ba kadan ba. Ayya kam bata bi takan Rayyan ba, kujera ta ja ta zauna kusa da Bilal tana tunanin a fadin duniya wanne ciwone zai kwantar mata da yaro haka
"Bilal..."
Ta kira da wani irin yanayi a muryarta dan tun suna hanya take tarbe hawaye, Abbu na kallon yanda lokaci zuwa lokaci take kai hannu tana goge gefen idanuwanta, gabaki daya hankalinta a tashe yake
"Me suka ce yana damun shi?"
Abbu ya sake fadi zuciyar shi na kara shiga cikin wani hali, dan shima bai taba ganin Bilal din ya kwanta ba
"Bashi da lafiya Abbu"
Rayyan ya furta dakyar, kyale shi Abbu yayi, duk da shikam daya ga Bilal din a zaune, zaije yayi magana a basu sallama su tafi asibitin makaranta gabaki dayan su. Amman a kwance yake da alamar bacci yakeyi. Mami ba damuwa da Bilal bane batayi ba, amman sun gan shi, ya kamata su karasa su duba Layla itama tunda tasan da wahalar gaske daga Rayyan har Ayya subar gefen Bilal din
"Bacci yake?"
Ayya ta tambaya tana kallon Rayyan da ya dan daga mata kai kawai. Gabaki daya zaman Abbu a dakin ya takura mishi, kan shi harya fara dawowa da ciwo. Wani abu yake tsikarin shi daya fita yabar dakin har sai Abbu ya tafi, amman saboda Bilal ba zai iya matsawa ko nan da can ba. Mami bata ce komai ba, saboda duk wata tambaya da zatayi su Ayya sun rigada sunyi. Rayyan din ba gaishe da su yake ba sai ta kama, zata iya haduwa da shi ya sadda kan shi kasa, ko yayi tsaye in da yake kan nashi a kasa har saita wuce sannan ya tafi inda zaije shima.
Kuma tun ranar da ta gansu da Layla sai ta kula kamar ya kara nisanta da ita. Ba abin bane ya dameta, amman batason kowa ya kullace ta, Ayya ma dan babu yanda zatayi ne shisa suke wannan zaman doya da manjan. Amman iya soyayyar da zata iya nuna musu a lokacin shine a tsawatar musu. Idan basu fahimceta yanzun ba, wata rana zasu fahimce ta.
"Maimuna kina nan ne? Mu dubo Layla?"
Dan juyawa Ayya tayi ta kalli Abbu, sannan ta sake mayar da dubanta kan Bilal. Bata zaton akwai wani abu da zai faru wanda zai saka zuciyarta taso Layla, yarinyar batayi mata ba tun daga ranar farko da ta dora idanuwanta a kanta. Ta kara girmama tsanar da take mata daga lokacin da Bilal ya fara raba lokuttan shi tare da yarinyar da kuma Mami, har yana shiga bangaren su. Sai kuma take kara ganin yanda Rayyan yake bata lokacin shi cikin yanayin da ko ita bata samun shi. Babu wani abu da zai sa taji yarinyar a ranta, bata sonta, in zata iya nisantata da duka yaranta zatayi. Amman rashin lafiya ce, batama san dan ance Layla bata da lafiya zataji wani abu ba.
Ganin yanda take tunani yasa Abbu fadin
"Ki zauna tare da Bilal din muje mu dawo"
Kai ta jinjina ma Abbu da ya saka hannu a aljihun shi, dubu hamsin ce ya cire ya taho da ita ko da zasu bukaci wani abin, talatin ya kirga ya bawa Ayya da fadin
"Ko da za'a bukaci wani abu"
Zuciyar shi a jagule take, ba zai kara jagula yanayinta ba ta hanyar bawa Rayyan kudin da yasan da wahala ya motsa daga inda yake ballantana ya saka hannu ya karba, sai yaga Rayyan yake tuna yanda yake son sakawa a tayashi a addu'a akan matsalar Rayyan din, ko da Nasiru ne yayiwa zancen, amman kamar wanda ake shafarwa kwakwalwa sai ya shirirance, sai ya sake ganin Rayyan din tunanin maganar ya dawo mishi, numfashi mai nauyi ya sauke yana juyawa, Mami na fadin