Chapter 2

26 1 0
                                    

Nov 1, 2020

2

May 1985, Kano.

Da gaskiyar iyaye da kance kukan yaro yafi komai daga hankali, har kasan ranta take jin kukan Rayyan, a gaggauce ta karasa wankan, sabonta ne sai ta saka hijabi idan ta daura zani sannan take fitowa daga wanka, kamar yanda takan shiga da ita. Amman yanzun kam haka ta fito, hijabin ma a bandakin ta baro ta. Ganin ta lallaba Rayyan din yayi bacci shisa ta lallaba tadan watsa ruwan ta fito, ashe ba nisa baccin yayi ba. Tana daga labulen gabanta nayin wata irin mummunar faduwa ganin Maryama data mika hannu tana shirin daukar Rayyan

"Me kike kokarin shafa mishi?"

Ta furta tana karasawa da sauri ta hankade Maryama da take tsaye. Sallar la'asar ta idar, tana zaune tana jan casbi kamar yanda takan wuni tanayi, ko karanta wani littafin da take tunanin zai amfani rayuwarta tunda ta shigo gidan. Da yake da ta gama firamare tayi makarantar kwana har aji uku, da maganar auren su da Ahmadi a kanta ma ta karasa aji ukkun. Bata tsammaci tarbar kwarai a wajen Maimuna ba, amman tayi mamakin kalar kiyayyar da take nuna mata kamar itace mace ta farko data fara shiga gidan aure a matsayin mace ta biyu. Ba zata manta ranar da aka shiga da ita dakin Maimuna watanni ukku da suka shige dan karrama Maimuna a matsayinta na uwargida kamar yanda tsarin al'ada yake.

Sam bata ga fuskar Maimuna ba tunda kanta a rufe yake kasancewarta amarya. Kalaman Iya Asabe da take fadin

"Wanda duk yake a dakin nan yasan halin da kike ciki, dan kishiyar nan anyi mana, wasun mu fiye da daya. Sai anyi hakuri, ko da babu tsira mai nisa tsakanin ki da Maryama kanwa ce a wajenki a gidan aure. Saboda haka ga amanar ta..."

Iya Asabe bata karasa maganarta ba Maimunar ta katse ta da fadin

"Iya ki takaita kalamanki, indai amanar Maryama ce ban dauka ba, karku doramun nauyin da ba zan sauke ba..."

Daga inda Maryama take zaune tana jin salallamin da duk wanda yake cikin dakin yakeyi cike da mamaki

"Inda amana ba zaku rako Maryama dakina ba wallahi, ba zaku dauketa ku liqawa Ahmadi ba..."

Ba zata manta yanda taji takun tafiya ana barin dakin daya baya daya ba. Har Iya ta kamata suka fice saboda yanda Maimuna sam taki sauraren nasihar da Iya taso tayi mata, tana barinta da furta

"Allah ya saukaka"

Kafin su fita daga dakin. Maimuna bata canza kalamanta ba ko bayan da Ahmadi ya hadasu da sunan yi musu nasiha

"Ka dauki matarka ku fitar mun daga daki Ahmadi, ku fita ba sai kun haskamun yanda zaku kasance da juna tsayin daren yau ba, wallahi hakurina yana gab da karewa..."

Maimunar ta karasa maganar da rawar Murya alamar kukan da take kokarin tarbewa. Ita kam zatace firgicin da ta tsinci kanta ya girmi wanda kowacce mace take tare dashi a darenta na farko. Daga ranar kuwa har yau babu wata magana ta arziqi data hadata da Maimuna, banda mugayen kallo da takan watsa mata duk idan ta wuce, tana jin labaran kishi, amman na Maimuna daban ne, ga yan uwanta da taga alama wajen zaman jegon Rayyan suna tayata.

Ba tsoron biye rigimar da Maimuna takan takaleta da ita a duk rana takeyi ba, kalaman Ahmadi ne suke tausarta

"Da bana sonki ba zan aureki ba Maryama, kamar yanda kauna ce tasani auren Maimuna kema haka. Idan ina da mutunci a idanuwanki zaki tayani kaucewa rigima da Maimuna, dan Allah ki kauda kai daga lamurranta, ki tayani wanzar da zaman lafiya a tsakanin ku gwargwadon iyawarki"

Tun kafin zama karkashin inuwar aure ya hadata da Ahmadi ta tabbatar da nagartar shi. Ta dauka tasan soyayya a iya tsayin lokacin da suka dauka kafin auren su, sai yanzun take ganin banbanci. Yanda Ahmadi yake kula da ita, yake gudun duk wani abu da zai sosa ranta ya kara daga daraja da matsayin shi a zuciyarta. Saboda shi zata cigaba da kauda kai daga halayen Maimuna har Allah ya fahimtar da ita cewa su dukansu zaman aure sukeyi, kuma ita da niyyar mutu ka raba ta shigo gidan, babu inda zata tafi.

HausanovelWhere stories live. Discover now