Nov 6, 2020
05
*
Kwanakin shi a lissafe suke, yana son makaranta, har kasan ran shi yana son makaranta. Yana kuma son karatu, musamman yanda Allah ya bashi baiwar kwakwalwa, da wahalar gaske ayi abu sau daya a gaban shi bai dauke ba. Kawai abu dayane ya kasa fahimta a shekarun shi goma sha bakwai yanzun a duniya. Duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu nuna suna son abu, lokacin zaiji har ranshi babu abinda ya tsana sama da abin, yana so ya bari, yana so yaso abinda suke so ko dan yanda yake ganin halayen shi sun kasa raba zukatan su da tarin kaunar da sukeyi mishi.
Ya wuce Bilal da aji daya, amman zai iya tuna lokuttan da Bilal din yake daukar nashi litattafan ya duba ko an basu wani aiki da baiyi ba dan ya taya shi. Da gangan zai bar takardun shi babu rubutun komai, kawai dan yanda Abbu ya nuna yana bala'in kaunar su da karatu, bawai dan tambayoyin sun gagare shi amsawa ba. Ba a makaranta kawai hakan ya tsaya mishi ba, duk wani lamari na rayuwa da zamantakewar yau da kullum, kar dai Abbu ko Ayya su nuna ga yanda suke so, dan zaiyi abu daban da wannan din ne. Bai fara kawo sakamako mai kyau ba sai da yazo aji hudu a makaranta, ranar da kalaman Abbu suka tunzura shi
"Nasan asarar kudina kawai nakeyi Rayyan, da ka daina zuwa makarantar nan zaifi mun, amman dai zanci gaba da biya dan in nunawa Yaya Ayuba cewa zancena gaskiya ne, babu abinda zaka iya ganewa indai bangaren makaranta ne"
Daga ranar hatta Malaman shi mamaki sukeyi, irin yanda lokaci daya ya canza haka. Har kaguwa yayi lokacin jarabawa yayi dan ya kawowa Abbu, aikam na biyu yazo a ajin nasu lokacin. Da kan shi yazo ya nunawa Abbu, karba yayi batare daya nuna wani jin dadi a fuskar shi ba
"Dan kayi wannan baya nufin za'a dore"
Shine kalaman Abbu, sune kuma kalaman shi a duk lokacin da zai kawo mishi wani abu daya danganci kokarin da yayi a makaranta. Tunda ko hira baya zama suyi, idan hirar shi tayi tsayi da wani to Bilal ne. Yanzun ma makaranta zasu tafi, harya gama shiryawa tsaf, amman Bilal ko wanka bai fito ba. Takalman shi ya dauko yana fitowa bakin kofa ya ajiye, silipas din da yake ajiye ya zira ma kafafuwan shi da nufin ya shiga bangaren Ayya ya dauko musu ruwa. Shi kayan sanyi ba damun shi sukayi ba, bama yaso sam, da an kawo pure water yake zuwa ya sungomo leda daya yazo dakin su ya ajiye. Ya duba ya kare shisa ya fito.
Yana karyo kwana suna cin karo da Layla da tsayin shi bai hana idanuwanta sauka cikin nashi ba
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ya furta da karfi, zuciyar shi na wani irin dokawa, bayason ganin yarinyar sam, sai yaga kamar mage ce ta gitta mishi, yanzun ma ko ina na jikin shi bari yakeyi, har zuciyar shi.
"Ina kwana"
Ta furta a hankali, duk da tasan ba amsawa zaiyi ba, zuwa yanzun da zata iya hana kanta gaishe da Rayyan ko shiga sabgar shi da ta daina. Amman duk abinda zata shirya ma kanta da ta sauke idanuwanta kan Rayyan din komai yake kwance mata. Kallonta yayi ran shi a bala'in bace
"Dan ubanki ban hanaki zuwa inda nake ba? Mayya ce ke? Sau nawa zan gaya miki idan ina waje ki daina zuwa?"
Rayyan ya furta har lokacin zuciyar shi bata daina dokawa ba. Wasu irin hawayen bakin ciki Layla taji sun taru a cikin idanuwan ta, bashi bane mutum na farko daya kirata da "Mayya" ba, ba kuma shi bane zai zama na karshe, ko Ayya takan fada wasu lokuttan, su kadai ne suke fada a cikin gidan gabaki daya. A waje kuwa da wahalar gaske ka furta kalmar bata fasa maka baki ba, ta karfi da yaji ta zama mafadaciya ta gaske. Kullum saiya mata kashedin zuwa inda yake, amman a haka yake aikenta, a haka yakan sakata aiki, tana iya dawowa daga aiken shi ya hauta da masifar ta daina zuwa inda yake kamar bashi ya kirata ba. Har mamakin shi takeyi, sai kace mai jinnu.
