34

24 1 0
                                    

Jan 30, 2021.

34

"Ayya..."

Bilal ya kira yana sa ta raba idanuwanta da inda yake tsaye tana kallon Rayyan daya daga mata kai yana tabbatar mata da yaji kiran, ba kunnuwanta bane kawai suka ji cewa Bilal ba tsaye kawai yake a cikin dakin ba, har magana yakeyi. Hankalinta ta sake mayarwa kan shi tana ganin yanda yake takawa yana karasawa inda take kamar wanda yake koyon tafiya, da duk takun da zaiyi da yanda zuciyarta take kara dokawa a cikin kirjinta da wani irin tsoro, sai dai kamar jira kawai yake ya karasa inda take kafafuwan shi su kasa daukar shi dan anan gabanta ya durkushe. Yayi kuka mai yawa bayan da ya tafi, amman baiji kalar kukan da yake tattarowa daga duk wani lungu na zuciyar shi daya taba yin ciwo ba irin yanzun.

Dan wani irin gunji ya saki mai tsuma zuciya yana rike kafafuwan Ayya da itama taji sunyi mata wani sanyi, Huda ta ture gefe, ba tsugunna tayi ba, zama tayi akan kafafuwan ta kamar mai zaman sallah tana kallon Bilal, ya sha bamban da fatalwin da take gani a fina-finai, jikin su baiyi kalar na shi ba, batajin kuma ana iya jiyo hucin numfashin su, a hankali ta daga hannunta da kafin ta kai shi fuskar Bilal ya kama shi da duka nashi biyun. Ko da fatalwa ne shi na danta ne, Bilal ne. Hannun shi na shine, hannu ne daya saba kama nata tun kafin yakai girman haka.

Duk da yanzun girman bai canza yanayin shi ba, zata gane hannun Bilal a cikin dubban hannaye, saboda zai rike nata hannun kamar yanda ya rike shi yanzun, cike da yarda da kaunar shi da batajin wani da bai san zafin da ba zai iya fahimta.

"Bilal"

Ayya ta kira yana daga mata kai kawai saboda kukan da yake yi, abu na farko da duk wata mahaifiya takeyi a lokacin da take ganin hawayen da na ita bace sanadin zubar su shi Ayya tayi, zame hannun daga cikin na Bilal ta kama shi zuwa jikinta duk kuwa da girman shi, kan shi ya dora a jikinta yana sake sakin wani sabon kukan, kukane na kewar ta, na kewar su gabaki daya, kukane na ban hakuri, kukane na abubuwa da yawa. Ba zaice ga lokacin daya dauka a haka ba, amman bai dago ba sai da yaji zuciyar shi ta daina nauyin da take mishi tukunna ya dago yana kallonta, ita yau ta nemi inda hawaye suke ta rasa, da kansu sun san cewa yanayin da take ciki sun girme su.

"Bana cikin motar Ayya, ban shiga ba, bana ciki"

Sune kalaman da suka zo ma Bilal, kallon shi Ayya takeyi, kallon shi take saboda bata taba saka ran sake ganin shi ba, kallon shi takeyi kaunar shi da babu inda taje mata tana tasowa tana kuma shafe duk wani bangarori na zuciyar ta daya hakura da shi, bangarorin da sukayi jinyar rashin shi, hannuwan shi ta kama tana saka fuskarta a ciki hadi da sauke wata irin ajiyar zuciya da ta budewa hawayenta waje, wannan karin ita ta kwantar da kanta a jikin Bilal, kukan ta yana sake fito mishi da sababbin hawaye

"Kaga me kayi ko Bilal? Kaga me tafiyar ka tayi mana?"

Rayyan yake fadi yana kifta idanuwa saboda baya son ya fara kuka, yanajin su duka ba kuka sukeyi ba, idan ya fara ba zaiji lallashi ba

"Daada"

Nur da ta fito ta kira Rayyan din, da gudu take tahowa tana saka zuciyar shi mantawa da komai da yake faruwa saboda yanda take dokawa da tsoron karta fadi, bai sami natsuwa ba sai da yaga ta zagayo ta kama kafafuwan shi kamar ta dade bata gan shi ba, ko daki ya shiga tana wani dakin, idan ya fito haka take barin duk abinda takeyi ta tashi ta rugo ta rike shi kamar yayi wata tafiya mai nisa, sai yaji ta nutsar da shi, ta saka zuciyar shi wani irin sanyi. Ganin ta dago daga jikin shi tana kallon Bilal yasa shi kallon Bilal din shima. Sosai Nur take kallon Bilal kamar ta san shi. Abinda kafin psychology yayi mishi bayanin shi yake ganin tsakanin Ayya da Bilal, tsakaninta da sauran yan gidan shi yake gani tsakanin Nur da Bilal da har lokacin baima kula da ita ba.

Hankalin shi gabaki daya yana kan Ayya da ta dago tana saka hannunta ta goge fuskarta da shi. Shima Bilal tashi fuskar yake gogewa, hakuri yake so ya bata, amman kalaman sunki fitowa. Ko da Nur bata kai haka ba, sam yarinyar batayi qwiya ba, kowa ya dauketa zuwa takeyi, gashi bata tsoron mutane, kawai magana ce batayi sosai

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 27, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HausanovelWhere stories live. Discover now