33

8 1 0
                                    

Jan 30, 2021

33

Fitowa tayi daga wanka, idanuwan ta kan Nur suka fara sauka kafin ta saki salati

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Idanuwan shi Rayyan ya daga ya kalleta a kasalance, kamar bai san dalilin yin salatin nata ba, yana kallo ta karaso ta kama Nur tana karewa gashinta da yake tsaye birci-birci duk ya cakude waje daya kallo wani malolon bakin ciki ya taso ya tokare mata wuya. Ita kadai tasan wahalar da tasha daren jiya tayi mata kitson, da kuka da komai, har dukanta sai da tayi, saboda Rayyan din ya kwana asibiti wajen aiki, Aminu Kano bangaren masu matsalar kwakwalwa. Ta san indai ya dawo ba za'ayi ba tunda Nur ba son kitso takeyi ba, ko kibiya ta gani a hannun Layla sai ta saka kuka.

"Kwance mata kayi?"

Ta tambaya, gira Rayyan ya daga

"Me yasa zakiyi mata kitso? Kin matse mata kai dakyar take motsa wuyanta, har gefen kan ya fara yin alamar kurji"

Sakin Nur tayi kawai, idan tayi magana tsaf hawayen takaici zasu biyo baya. A shekaru uku da aurenta da Rayyan ba zata ce bata cikin kwanciyar hankali ba. Amman tunanin da tayi na cewar auren Rayyan shine zai gyara mata komai, idan tana tare da shi babu wani abu da zai dameta ne ya sha bamban. Mutane ne suka nuna mata damuwar ta babu inda zata je, kamar yanda suka koya mata rayuwa da damuwar a kasan zuciyar ta. Ko biki akeyi ko suna idanuwan mutane akan Nur suke fara sauka, Nur suke fara gani, kamar yanzun rayuwar ta gabaki daya ta tattara ne akan yarinyar

"Ita ce wannan ko? Allah sarki"

Sune kalaman da suka fi tsaya mata a kirji suna sakata jin wani irin ciwo na ban mamaki. Ba manta yanda aka sami Nur tayi ba, amman na rana daya tana so ta rufe idanuwan ta, ta bude su ta kalli yarta a matsayin ya, ta kalleta batare da taga tabon da tayi mata ba, tabon da shi kowa yake fara dubawa. Ba son kai zatayi ba, amman Nur tana da kyau, sosai tana da kyau saboda tana kama da Bilal, kamannin da yasa in ba sanin su kayi ba sam ba zaka gane ba daga jikin Rayyan ta fito ba, gashi tana da hasken fata kamar na Rayyan din. Sai dai kyawunta ya kasa dishe munin tabon da yake tare da ita.

Shekarar su daya da aure, Rayyan ya saka ta sake yin jamb ta nemi gurbin karatu a BUK.

"Kina da buri kafin faruwar komai, abubuwa da yawa sun canza miki, bana son ya zamana harda wannan...ki koma makaranta Layla, kiyi karatu, ki fita da sakamakon da kike burin fita, ki nemi aikin da kike fatan samu"

Shine kalaman shi, kalaman da suka bude mata zuciyarta suna dawo mata da burin ta sabo. Ko ba komai makarantar ta rage mata damuwa, yanzun tana shekara ta biyu, ta sha wahala a farkon zango na biyun a shekarar saboda laulayin cikin da yake jikinta, ga kula da Nur, tunda Rayyan yaki yarda a sakata makaranta sai a sabon zangon da za'a shiga, dan ma bakomai take yiwa yarinyar ba saboda Rayyan in dai yana gida fiye da rabi da kwata na lokacin shi yana kan Nur dinne, in ba bacci tayi ba ita Layla bata samun kan shi sam. Duk da haka ta sha wahala, tunda in dai aikin safe yakeyi sai ta dafa mishi abinda zai tafi da shi. Wata ukku na farkon cikin ta wahala sosai, yanzun ne ma ta dan samu saukin laulayin.

Yau da ya kama asabar zasu je gida ne gabaki dayan su. Basu ma tashi da wuri ba, indomie da kwai ta dafa ma Rayyan din da Nur, ita tana da sauran doyar da sukaci da daddare, ita tayi warming taci. Yanzun ma mai ta shafa ta dauki kayanta tana ficewa daga dakin ta kyale su. Sanda ta dawo ta gama shiryawa tsaf

"Ki gyara mata kan, ina takalman ta?"

Ya bukata, inda suke Layla bata kalla ba

"Magana fa nake yi"

Rayyan ya sake fadi da alamar dariya a muryar shi, sarai yasan ta kule, ranta a bace yake. Babu yanda zatayi da shine kawai tunda ya fita rikici, ya kuma fita iya fada. Baisan sau nawa zai gaya mata ta daina ma Nur kitso ba, duka yarinyar yaushe kanta yayi kwarin da za'a kama shi ana mai kitso, ko gashin kirki ma babu, keyar ba komai har yanzun. Kawai salon a saka mata ciwon kai. Ya ce ta dinga shafa mai sai tayi mata kalba ta saka mata hula, kan da za'a rufe in ba rigima ba meye nayi mishi kitso. Sanin Layla ba kula su zatayi ba yasa ya mike yana daukar Nur din, da kan shi ya karasa in da kayanta suke ya samo wata farar hula mai duwatsu a jiki ya saka mata, takalman ma shi ya dauko mata.

HausanovelWhere stories live. Discover now