Dec 7, 2020
17
A Zaria yai zaman shi, babu yanda Bilal baiyi da shi ba
"Ka zo mu tafi gida. Idan mukayi sati daya sai mu dawo. Ko dan Ayya..."
Kai Rayyan ya girgiza mishi
"Sai sun ganni zan musu laifi. Ka barni Bilal, ka cikani da surutu"
Shine amsar daya bashi, duk wata magana da Bilal din yayi bayan nan bai ko kalle shi ba ballantana ya amsa. Yana kokarin kare Layla ne iya yanda zai iya. Idanuwan Mami ko Abbu ba zasu hana shi riketa ba idan ya tashi. Ko dan Abbu ya nuna bayaso, akwai abinda zai tunzura shi ya rike Layla a gaban Abbu, abinda har yanzun ya kasa gane kan shi, yana fahimtar yanayin mutane tun kafin ya karanci fannin, shisa baya son su. Amman ya kasa fahimtar kan shi, ya kasa gane abinda yake damun shi.
Ya sha cin karo da abinda ake kira "Depression" a turance, yanzun haka yana kan magungunan shine da basayi mishi aikin komai banda kara mishi kuncin da yake ciki. Zuwa yanzun ya hakura, ya saduda da cewa akwai wani likita da zai mishi maganin matsalar shi, ko zaima fahimceta. Ya dai san katangar da take tsakanin shi da tabin hankali bata da kauri. Shisa ya zabi zama a Zaria, shi zai dauki duk wani surutu da za'ayi. Layla ba zata dauka ba, baya son kukanta, baya son ganin hawayen da bashi bane dalilin su a idanuwanta.
Sam ba zai iya zama a cikin gida daya da ita yayi mata nisa ba. Zaman shi a Zaria shine saukin su dukan su. Kuma ya ma tsaya ya karasa project din shi a satika shiddan da aka bayar ya tattara ya basu yasan ya gama. Su yake jira, ya tafi bautar kasa abin shi. Duk da Ayya ta kira shi a satin farko, sallamar da tayi ya amsa yana yin shiru
"Shine baka zo ba ko Rayyan? Yaushe rabon da in gan ka? Baka tunanin idan kai baka kewata ni zanyi taka?"
Akwai wani yanayi a muryarta a ranar da yasa shi fadin
"Ina abune haka Ayya..."
Yanda ta ce
"Hmm..."
Sai da yaji wani iri, kafin ta dora da
"Allah ya taimaka ya tsare"
Bai iya amsawa ba harta kashe wayar, daya sauke daga kunnen shi bin wayar yayi da kallo, lokutta da dama yakan nemi kusancin daya kamata ace ya kasance a tsakanin mahaifiya da danta a tsakanin shi da Ayya ya rasa. Sosai yake so yaji wannan kusancin, yakan ga Bilal na binta da kallo kamar babu macen da zata zamana da muhimmanci, kima da daraja a idanuwan shi kamarta, zai rantse murmushin da Bilal kan yiwa Ayya bai taba yi mishi irin shi ba. Akan fuskar shi zaka ga tsantsar kaunar da yake yi mata a shimfide. Ko a waya ta kira shi, kafin ya daga Rayyan ya san ita ce, saboda yanda fuskar shi take canzawa gabaki daya.
Ko ran Bilal a bace yake idan Ayya ta kira shi sai yayi murmushi, karshen bacin ran kenan a wasu ranakun. A tare da Bilal yake ganin kaunar daya kamata ta kasance a tsakanin shi da mahaifiyar shi. Zai karya idan yace abin baya mishi wani iri, sosai abin yake ci mishi rai, bambancin da yake tsakanin shi da sauran mutane mai girma ne. A tsayin satikan su kanyi magana da Layla, rannan ma tace mishi
"Dan Allah Hamma ka siya babbar waya"
Tun kafin ta karasa maganar ma yake girgiza kan shi
"Um um"
Ya furta
"Dan Allah, za muna chatting fa"
Numfashi ya sauke yana sakw furta
"Um um"
Jin ta fara cika mishi kunne yasa shi fadin
"Idan kika dameni zan kashe wannan in ajiye"