Dec 5, 2020
16
Kwance take a cikin hostel a kan gado, ta lumshe idanuwanta, ba dan gadon yafi nata na gida ba, amman wani irin nishadi take ji yana shigar ta, nishadin da bata da kalaman misalta shi. Ta dauka ita da Zaria sai a mafarki, yanda Mami ta dauki fushi da ita har kasan ranta ta hakura da karatu a Zaria. Ta jigata, ta sha wahala, akan gwiwoyin ta da hawaye cike taf da idanuwanta ta tsugunna tana baiwa Mamin hakuri saboda bata ga abinda tayi mai zafin da zaisa Mami ta daina mata magana ba
"Ban san sau nawa zan jaddada miki MARTABAR MU a matsayin 'ya'ya mata ba kafin ki fara kare taki"
Mami ta fadi tana dorawa da
"Bance ki dubani ba, ki duba kanki da maraicin ki, yanzun mutunci ne ace kuna wannan rike junan ke da Rayyan?"
Hawayen da suka tsiyayowa Layla ta goge da hannu
"Ni dai Mami dan Allah kiyi hakuri, nace ba zan kara ba, na daina, dan Allah kiyi hakuri"
Numfashi Mamin ta sauke
"In zakiyi hankali dai kiyi, dan an Abbun ku ya tambayi Rayyan din yace ba son ki yake ba..."
Duk wani abu da Mami ta fada bayan nan bai karasa kunnuwa Layla da suka toshe da kalaman Mamin na karshe ba, har kuma ta baro gidan bata samu wani nishadi ba sai yanzun da take a kwance. Kwananta hudu da wani irin zazzabi da ya wajigata. Mami bata taba mata karya ba tun tasowarta, amman kiri-kiri ranar ta tsinci kanta da karyata Mamin, saboda karta komawa Rayyan shisa tayi mata karyar da bakin shi yace wa Abbu baya sonta. Bata tsammaci ya sota ba, batama san da gaske ta daga burinta akan shi ba sai da Mami ta fada mata kalaman da taji kirjinta kamar an kunna wuta a ciki.
Kwana tayi tana kuka, da safe fuskarta kamar kwabin alkubus saboda yanda ta kumbura, Mami bata ce mata komai ba, ko wanke-wanke tanayi tana kuka haka ta karasa shi ranar. Kuma yanzun ma da ta tuno kalaman sai da taji wani irin daci ya taso mata yayi tsaye a karkashin makoshin ta.
"Mami sai dai kiyi hakuri, amman ni ba zan rabu da Hamma ba, ko ya rabu dani ni ba zan rabu da shi ba. Mayya ce, amman mayyar shi"
Ta furta a hankali, kalmomin "Mayyar shi" din na zauna mata. Abin ya hade yayi mata yawa, saboda har suka bar gidan Rayyan baya mata magana, baya kiranta ya saka tayi mishi wani abu. Idan daga nesa ya hangota zai kalli wani wajen, ita kuma tsoron Mami yasa ko a waya ta kasa kiran shi. Ranar da zata koma makaranta babu kalar wa'azi da nasihar da Mami batayi mata ba, duk da batasan me Abbu ya fadawa Mami ta yarda tabarta komawa Zaria ba. Amman tana da yakinin yana da alaka da yanda watanni shidda ne kacal suka ragewa Rayyan din ya kammala karatun shi gabaki daya.
A mota wannan karin gidan gaba ya zauna, daga ita har Bilal bai musu magana ba, Aisha ma da suka biya suka dauketa, da ta gaishe da shi Layla bata ga yayi alamar yaji ba ballantana ya amsa, muryar shi take son ji da dukkan zuciyarta, amman yayi shiru, cikin kujera ma ya shige yanda ko wuya ta dan leqa ba zata iya ganin shi ba har suka sauka. Bata gaji ba dan da ta sauka ta zagaya ta bangaren shi tace
"Hamma..."
Gilashin murfin motar ya daga yana jan shi sama ya jingina kai a jiki yanda ko fuskar shi ma ba zata gani ba. Za kuwa tayi karya idan tace abin bai mata zafi ba. Dakyar ta danne hawayen da taji suna shirin zubo mata, duk da kwakwalwar ta na son ta tirsasawa zuciyarta tuno maganar Mami, ta tauna taga ko da gaskiya a ciki taqi yarda, hakan zai iya barazana da zaman lafiyarta fiye da yanda take ciki yanzun. Ko Rayyan baya son ta bai fadawa Abbu ba, bai fada ba, tana da sauran buri akan zai kalleta da fuskar soyayya wata rana, idan ma baiyi ba ya aminta da tarin soyayyar da ita takeyi mishi, ya ishe su.
Wayarta ta dauka da take ajiye a gefe jin sakonnin da suke ta shigowa. Tun a hanya an mayar da ita group daman, duk yanda taso ta daina karance-karance da takeyi sai ta tsinci kanta da kasawa, duk idan Nanaa ta turo mata sai ta karanta. Da kanta tace a mayar da ita tun tana mota, duk da wani abu a kasan zuciyar ta na son nuna mata tarin kuskuren da yake cikin hakan, yanayin da take jine ya rinjayi wancen kashedin. Gara taji da abu daya, duk da kome ta karanta din sai ta dinga hasaso Rayyan a tare da ita, cikin yanayin koma meye yake faruwa a abinda take karantawar.
