Chapter 3

7 1 0
                                    

Nov 1, 2020

3

1986 Kano.

Yaron da yake rike a hannunta take kallo, yaran da duka satin shi biyar a duniya, wasu hawaye masu dumi na tarar mata cikin idanuwa. Amman zuwa yau tasan cewa kukan nan babu wani amfani da zai musu, kukan ba zai dawo mata da kaninta ba, ba zai canza kaddarar yaron da yake hannunta ta Maraici a satika biyu bayan haihuwar shi ba. Ba zatace tashin hankali bakonta bane ba, tasan shi a lokacin da ta raya Yayya, ta kuma san shi a lokacin da Ahmadi ya hadata da Maryama da ta zame mata Karfen kafa (Rufaida Omar). Tana kuma cikin shi har yanzun da Maryama ta ajiye kwai a cikin gidan Ahmadi, dan duk lokacin da zata ga giccinta ko kukan yaran nata Haris, sai taji wani abu ya tsirga mata.

Kwance take a daki tun bayan da tayi sallar asuba satika biyu kenan da suka wuce, haka kawai jikinta yai wani irin sanyi, ba shida alaka kuma da fadan da sukayi da Ahmadi tasani, kishinta a duk ranar da yake dakin Maryama daban da abinda takeji yanzun. Ko daya shigo ya dubata ma da safe inda yake bata kalla ba, ballantana ta amsa dukkan tambayoyin da yakeyi mata. Tana jin shi harya fice, dakyar ta iya tashi ta watsa ruwa, Rayyan ma tayi mishi wankan. Gobe ko jibi take da niyyar yaye shi, a karo na farko da har zatayi yaye batare da wani cikin ba.

Zatayi karya idan tace abin baya damunta, bata da kowa da yake fahimtar ta duk dangi, daga Gwaggo Bare sai Khadi. Yayyanta mata da suke ciki daya data gwada fada musu damuwar ta zancen su kusan kala dayane

"Kiyi hakuri da kaddarar ki Maimuna, kowa da kika gani ba son kishiyar nan yakeyi ba, ki cire wasu zarge-zarge daga ranki tunda mijin ki na son ki"

Shisa ta koyi kame bakinta a gabansu, son da suke ikirarin Ahmadi nayi matane dalilin komai, sunki fahimtar soyayyar nan tashi da yake matace yake rabawa da Maryama. Soyayyar da aka ga yana mata ce ta tsone idanuwan su Maryama harta shigo mata gidan miji. Yanzun kuma soyayyar da suka kasa nasarar dakushewa gabaki daya a zuciyar shice dalilin da take zargin suna son hana mata cigaba da ajiye yara a gidan Ahmadi. Ko da ta tambaye shi tana so taje gidan Gwaggo Bare a lokacin bai hanata ba, tana zuwa da kukanta ta shiga gidan, tana saka Gwaggon yin fatali da rariyar hannunta da take tankaden garin dawa tana mikewa ta tarbeta

"Na shiga ukku ni jikanyar Munzali... Maimuna lafiya?"

Cewar Gwaggo bayan ta taimaka mata ta kwance goyon Rayyan ta sabashi a nata bayan ta daure da zani. Kai Maimuna take jijjigawa kukan da takeyi yana kara yawaita

"Gwaggo har yanzun shiru, ban taba wata shidda cikakku ina shayarwa babu wani cikin a jikina ba. Ina tsoron ko Maryama ta shafemun mahaifa..."

Salati Gwaggo takeyi tana karawa

"Anya su Maryama basu kwashe kayan su daga gaban Ma'aiki ba? Ina mutanen nan suke so sukai haqqi? Wato gaje gidan gabaki daya sukeyi shisa ake so a hanaki haihuwa. Wallahi bokan Karime yayi karya..."

Bata bar gidan Gwaggo ba saida ta tabbatar mata da taji labarin wani Gwani da yafi Malaminta kwarewa, dan shi sha yanzun magani yanzun ne. Yasan ilimin taurari fiye da misali, zataje wajen shi ya buga musu kasa ya fayyace musu abinda yake faruwa. Koyayane har gida zatazo tayi mata bayani, sai a san yanda za'ayi. An kuma tabbatar mata da cewa da gaske daurin mahaifa akayi mata, cikin kogon maciji aka binne asirin, ranar yini tayi kuka kamar ranta zai fita, sanda Ahmadi ya dawo duka fuskarta a kumbure take, shine musababbin fadansu, tambayarta da yayi ko lafiya ta kuma amsa shi da

"Rabona da lafiya tun kafin na yayibo mana Maryama, tun kafin ka bata damar da zatayi amfani da ita wajen kassarani"

Tana ganin tashin hankalin da yake cikin idanuwan shi kafin ya karasa cikin dakin sosai yana tsugunnawa kusa da ita

"Wani abin tayi miki? Da na fita tayi miki wani abinne?"

Ahmadi yake tambaya, wannan karon cikin idanuwa Maimuna take kallon shi

HausanovelWhere stories live. Discover now