Chapter 7

12 2 0
                                    

Nov 14, 2020

07

Bai fara dana sanin neman gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello da take garin Zaria ba sai da ya samu. Bai san sa'a bace ko kuma matakan su daya tsallake ko kuma sanayya ta manyan mutane da Abbu yayi ta saka shi samun abinda ya nema. Kawai dai yasan ya fara dana sani ne daga jiya da Haris ya dawo har dakin su ya shigo da sallamar shi yana zaune, maganar shi ta farko bayan sun gaisa ita ce

"Abbu yake fadamun ka samu gurbin karatu a makarantar mu, shine ko ka kira ka sanar dani. Naji dadi wallahi, saboda duk bangaren lafiya dai ne"

Tsayawa yayi yana kallon Haris da yake magana kamar ya fada mishi ya zabi karantar fannin daya danganci kwakwalwa da sanin halayyar dan Adam wato Psychology saboda ya kasance waje daya da shi. Ya zabi fannin ne saboda yana son fahimtar wasu daga cikin halayen shi, wasu cikin tarin tambayoyin da yake tunanin bangaren zai amsa mishi akan kan shi, badan wani dalili ba. Kuma ko ba komai kaunar da yake ma uniform zai kasance yana saka farar rigar nan lokaci zuwa lokaci. Saka uniform ne abu daya da yayi kewa bayan gama sakandire din shi. Haka kawai sai yaga duk kayan da zai saka ba zasu kai yanda yake saka uniform yin kyau ba.

Wani lokaci can baya kaunar da yake ma uniform ta saka shi tunanin aikin soja, sai dai har kasan zuciyar shi yaji haka kawai ba zai iya nisa da gida ba, kuma bayason takurar da take tattare da aikin, yana da taurin kan da yake da tabbacin zai wahala a aikin. Zuciyar shi ba tada sanyin da zata lankwasu yayi biyayyar da yaji ana labarin yiwa manya. Shisa bai kara barin tunanin ya dame shi ba, kafin ya yanke hukuncin zabar fannin da ya zaba yanzun, yayi tunani kala-kala, ayyuka barkatai sun zo ran shi. Sai dai zuciyar shi tafi rinjaye akan Psychology din ne.

Haris din kuma yana bangaren lafiyar yara ne wato Pediatric. Ba shiga harkar kowa yake ba a gidan banda Bilal, anso hada su daki daya. Tashin hankalin da ya dinga yine yasa su Abbu suka bar su shida Bilal a daki daya. Lokacin da yaji labarin bangaren da Haris ya samu gurbin karatu da Bilal kawai yayi zancen

"Hamma zaiyi kyau da likitan yara...ko a gidan nan ka kalli yanda su Intisar ke son shi. Ko masallaci muka fito ba zaka rasa ganin shi rike da wani yaron ba"

Murmushi Bilal yayi

"Duk yaushe ka kula da Haris haka?"

Harar Bilal yayi

"Dan bana shiga harkar kowa baya nufin bana kula da abinda yake faruwa"

Jinjina kai Bilal yayi

"Naga alama ai, ko Ayya zancen da tayi mun kenan. Sanyin halin shi ne yasa yara suke manne da shi, ga kyauta kuma, ba zaka raba aljihun shi da dan biskit ko alawa ba"

Rayyan kwanciya ya gyara yana yin shiru, surutun Bilal ya cigaba da yi har saida ya kule

"Wai bacci kayi ko wulakanci ne yasa kayi banza ka kyaleni ina ta zuba ni kadai?"

Ba baccin da yakeyi, ya lumshe idanuwan shine, yana jin shi, a duka zancen shi babu wanda zai bada amsa, a wajen shi hirar ta rigada ta kare, ya fadi abinda yake son fada. Duk da yaso hirar tayi tsayi sai Bilal din ya kunna shi da maganar da yayi kan yaushe yake kula da halayen Haris. Yana so ya mayar da shi kamar baisan abinda yakeyi ba. Shisa sam mutanen da yake ji a ran shi basu da wani yawa, saboda halayen su na saurin cakar da shi.

Jiyan ma kallon Haris ya dinga yi, har ya gama surutun da zaiyi. Ganin ba amsa shi zai ba yasa ya tashi ya fita daga dakin. Yanayin fuskar shi ma ya bala'in bata ma Rayyan din rai, saboda haka kawai ba gayyato shi yayi ba, baice ya shigo daki ya same shi ba. Da suka gaisa bai sashi zama ya fara mishi hirar rashin dalili ba, yazo yasa yanajin kamar yayi mishi laifi. A fuska ya nuna baiji dadin shirun da yayi ba.

HausanovelWhere stories live. Discover now