32

10 1 0
                                    

Jan 22, 2021.

32

Yafi mintuna sha biyar tsaye yana juya hular da ya kamata ace tana sanye a kan shi. Yau na daya daga cikin ranakun da suke da muhimmanci a rayuwar shi, ranar daya kamata yayi ta da mutanen da suke da muhimmanci a wajen shi, bai ma su Abbu gardama ba da sukace ya bari Layla tayi arba'in, yarinyarta ta danyi kwari sannan. Duk da ba wannan dalilin bane ya saka shi jiran, har a kasan zuciyar shi Bilal yake jira, a cikin kwanakin babu ranar da zata wuce idan ya kira gida baiyi tsammanin zasuce mishi Bilal din ya dawo ba.

Watakila harda kewar Bilal da yake ji a duk wata gaba ta jikin shi, kamar zuciyar shi na son gaya mishi baiji mutuwar Bilal yanda ya kamata ba saboda yana tunanin kamar bai rasa shi ba. Tun lokacin daya fara tunanin aure yasan baya bukatar wata hayaniya, a daura mishi aure kowa yayi fatan alkhairi ya tafi. Idan akwai abinda ya hango bai wuce shi da Bilal zaune a daki suna cin abinci suna hira bayan an daura aure, amman bayajin zai samu hakan yau. Baiyi kokarin danne Layla ba, ya tambaye ta

"Wanne irin biki kike so Layla? Dan Allah ki fada mun, bikin ki ba zai dawo sau biyu ba..."

Ita ma din tana daya daga cikin mutanen da basa son wata hayaniya ta biki, tuni suna fada ita da Jabir, bikin su daga su sai mutanen da suke da kusanci da zuciyoyin su suke bukata a lokacin bikin su

"Bikin da zan zama matar ka Hamma, daurin aure, shi kawai nake bukata"

Duk yanda idanuwanta ke kara gudun zuciyar shi sai da ya jima yana kallon cikin su yana neman gaskiyar maganarta. Bayason taji cewa kamar ita din bata cancanci kalar bikin da take mafarki ba

"Wai me kakeyi ne har yanzun?"

Bappa da a gidan ya kwana duk kuwa yanda Rayyan din yace mishi ba wani abu za'ayi ba, ya koma gida da safe ya dawo

"Ina ruwan ka dani ne Rayyan? Gidan nan naga na Abbu ne, kuma baice in tafi ba..."

Har a zuciyar shi yaji dadin zaman Bappa din, tunda kusan kwana yayi yana kallon ceiling cike da tunani kala-kala har wayewar garin

"Ku fa ake jira"

Haris ya fadi yana leko kan shi, turarukan daya hango na saka shi shiga cikin dakin sosai. Dauka yayi ya sake feshe jikin shi, Rayyan na bin hular da take kan shi da kallo, zuciyar shi na matsewa a cikin kirjin shi

"Hular Bilal ce ko?"

Ya bukata muryar shi can kasan makoshi. Kai kawai Haris ya daga mishi yana ficewa daga dakin. Kamar yanda ya fadawa Rayyan cewa zaije Zaria ya kwashe kayan su haka akayi. Rana daya ya ware, da wani irin karfin zuciya ya shiga garin Zaria har zuwa unguwar su Bilal. Harya shiga cikin gidan ma haka, ya san duk yawancin yan gidan, da Abdul ya fara cin karo daya karaso da sauri suna gaisawa yana dorawa da

"Ina Bilal? Lambobin shi gabaki daya a rufe, mun kasa samun lambar Rayyan, kaima taka tayi wahala saboda babu yan set dinku da sukayi saura, wallahi tunda aka dawo muke tunanin ko lafiya....sai yanzun muke tunanin kalar zaman da mukeyi da yanda ya kamata ace kowa yana da adireshin gidan kowa ko da halin ziyara bai samu ba"

Wani murmushi mai ciwo Haris yayi, zuciyar shi daya dauka ta dake yaji tana rawa, muryar shi ma a raunane yaji ta lokacin daya kalli Abdul da fadin

"Ya rasu, hatsari yayi. Ya rasu..."

Ya karasa maganar wani abu na tokare mishi makoshi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Din da Abdul ya furta cike da tashin hankali na saka shi raba Abdul ya wuce cikin gidan. Da yake ya karbi mukulli a wajen Ayya, shiya dauko ya saka yana bude dakin, bai shiga tashin hankali ba sai daya kunna kwan dakin yana ganin yanda yayi wata irin kura kamar mutane basuyi rayuwa a ciki ba. Dakin yake karewa kallo, yana hango wajeje da lokuttan da suke zaune a ciki shi da Bilal, sai yaji har kirjin shi ma zafi yake. Ba zaice ga mintinan daya dauka a cikin dakin ba kafin yaji shigowar yan gidan su Bilal din da babu wanda yace mishi komai, dakin suka fara taya shi sharewa.

HausanovelWhere stories live. Discover now