31

7 1 0
                                    

Jan 16, 2021.

31

"Abbu ka yafe mun, dan Allah Abbu ka yafe mun, duk ku yafe mun..."

Shine kalaman da sukewa Abbu amsa kuwwa a cikin kunnuwan shi harma da kai. Muryar Layla na zauna mishi da wani yanayi, yanda tayi maganar kamar tana saka ran fitar duk abinda yake cikinta zaizo ne da ajalinta. Da kan shi shekaranjiya bayan sun sake kwasowa zuwa asibiti cikin dare ya samu likitan yace

"Wai ba zakuyi mata aiki ku ciro abinda yake cikin nata bane? Tun da satin nan ya kama yarinyar nan take cikin wahala, dan Allah ku duba lamarin"

Murmushin karfafa gwiwa likitan yayi mishi yana kuma bashi tabbacin babu wata matsala dan wasu matan nayin haka. Ba zai manta ba, ko Mami takan yi doguwar nakuda, ta Layla din ce dai take tsaya mishi a rai fiye da duk wadanda yagani a baya. Nakudar ce saita taho mata gabaki daya sunzo asibiti sai kuma ta lafa ace ba haihuwar bace su sake kwasa su koma, yau ne karo na hudu a sati daya. Ita take ciwon amman zai iya rantsewa rashin natsuwa ya saka sunyi zuru-zuru gabaki dayan su. Yau kam ko da sunce ba haihuwar bace shikam zaice a barta a asibitin ne kawai.

Bai san akwai tsoron da zai danne na ganin jikan da zai diro ahalin su da gurbataccen asalin da bashi da masaniya a kai ba sai yau. Ko da yake zaice akan cikin Layla ya fahimci ba mata kadai ke da gulma ba, ba kuma su kadai tsegumi ya tattara ya zaunawa ba. Tun bai gane kallon da akeyi mishi a masallaci ba, da yanda har wani dan jinjina kai wasu a cikin mutanen unguwar sukeyi kamar alamun tausaya mishi duk idan sun hada idanuwa, ciki harda mutanen da gaisuwar musulunci ce kawai take giftawa a tsakanin su.

A cikin irin mutanen ne wani ya iya samun karfin gwiwar tarar shi sun fito daga masallaci yana fadin

"Alhaji ashe kuma haka wannan lamari ya faru da yar wajen ka? Allah ya kiyaye na gaba, kasan yarane yanzun ka haife su baka haifi halin su ba, kana iya kokarin ka akan tarbiyar su suna dauko maka magana. Allah dai yasa an dauki hukunci mai karfi akan yaron da yayi ta'asar"

Tunda ya fara magana kallon shi kawai Abbu yakeyi, shi da kan shi sai da ya tsargu ya fara kame-kame yana barin wajen. Amman tabbas zantukan shi sun rigada sun isar da sakon da yake son su isar a zuciyar Abbu, mutane sunyi gaskiya, zancen duniya baya boyuwa, ba kuma komai bane idan ka binne yake kwanciya lafiya, wasu hawaye yaji masu zafin gaske sun taru a cikin idanuwan shi. Da girman shi da komai, ashe kallon tausayin da kowa yake mishi kenan a cikin unguwar, kallon yanda martabar gidan shi da ahalin shi ta tabu. A ranar sai da ya kasa hakuri yake labartawa Mami abinda ya faru, sai dai murmushi tayi mai cike da karayar zuciya.

Don dai batason kara daga mishi hankali shisa bata fada mishi ya taushi zuciyar shi ba, ba zatace ga lokacin da maganar cikin Layla ta bullu a cikin dangin su ba, ko ta hanyar da hakan ya faru. Duk da tana son dora alhakin akan Anty Uwani, dan itace ta zo gidan tayi sa'ar ganin giccin Layla, duk da a lokacin akwai hijabi a jikin Layla, kuma cikin duka bai shige watanni ukku ba. Da farko bata kawo komai a ranta ba akan yawan ziyarar da yan uwa na jiki da na nesa suke kawo mata ba, sai da suka fara tambayar inda Layla take da yanda suka kwana biyu basu ganta ba, suna yin tambayar idanuwan su na yawo a cikin gidan kamar zasu iya hangota ta cikin daya daga bangwayen da suke zagaye da dakin.

"Tana lafiya. Alhamdulillah"

Shine amsar da suke samu, sai ko murmushi mai ciwon gaske daga wajen Mami din, tana so tace musu Layla tana makaranta ko dan gujema tarin tambayoyin su, shisa a irin lokuttan take zabar ta mike ta kawo musu abin sha ko ta kawo wani zancen da zai sa su kyaleta, amman sai sun san yanda sukayi suka dawo da zancen akan Layla. Tun tana kuka bayan tafiyar kowanne a cikin su har zuciyarta ta bushe. Duk zuwan bai musu ba sai da suka dinga turo yaran su 'yan matan suna kusan yini a gidan. Haka makota ma da suka fara mata zarya, har mutanen da bata taba sanin da zaman su a cikin unguwar ba.

HausanovelWhere stories live. Discover now