Chapter 13

14 1 0
                                    

Nov 28, 2020

13

Kwance Bilal yake yana nazarin wani lissafi, saboda har an fara test tun satin daya gabata, jarabawa nata karatowa. Amman Rayyan zaune yake yana zane, wani lokacin zaka rantse da Allah hutu Rayyan yake zuwa yi Zaria ba karatu ba, saima lokacin jarabawa, idan baka gan shi yana zane ba, to zaka iya ganin shi yana kwance shiru, tunda shi dai baya hada hanya da wata kafar sada zumunta, har dan whatsapp din da akeyi ma bayayi. Asalima wayar shi da screen din ya fashe yar karamar Nokia ya siya ya saka sim din shi a ciki.

Idan wani abu na makaranta ne daya kama sai an duba yanar gizo, da kwamfuta din shi kirar laptop yakanyi amfani. Kuma yana daya daga cikin mutane hudun da suke jagorantar ajin su ta fannin karatu, inda Rayyan dinne na biyu, idan da zai maida hankali ma tsaf zai zama gwarzo a ajin.

"Wai ba test kace kuna da shi ba?"

Bilal ya bukata, kai Rayyan ya jinjina mishi

"Ba zakayi karatu ba?"

Raba idanuwan shi da takarda Rayyan yayi ya kalli Bilal din, kallon da yake fassara "Da ni kake?". Kafin ya mayar da hankalin shi kan zanen da yakeyi

"Lokutta irin haka kana sakani inajin kamar bani da kokari"

Dan numfashi Rayyan ya fitar

"Kana da kokarin ne? Tun dazun kake kallon takarda daya"

Bude baki Bilal yayi, kafin ya mike zaune

"Kasan wanne lissafine? Kake kira takarda daya kamar wani abu marar wahala"

Fensirin hannun shi Rayyan ya ajiye, ya dan juya zaman shi yana mika hannu ya fisge takardar da take hannun Bilal, duba tambayar yayi, batare daya dago ba yace

"Ina misalin? Wanda akayi?"

Tashi Bilal yayi ya dauko jakar shi yana fito da littafi ya dubo wani misalin yana mikawa Rayyan daya karba, sosai ya nutsar da hankalin shi yana ganin yanda aka fitar da abin. Kafin ya fara duba wanda Bilal yake nazari, a idanuwan shi yaga yanda komai zai kasance, juyawa yayi ya ajiye akan tebir, cikin mintina kasa da sha biyar ya gama fitar da shi yana jefawa Bilal din

"Ba zaka maida hankali sanda ake maka abu a aji ba, kana can kana wasu tunane-tunane..."

Rayyan din ya fadi a fadace, dauka Bilal yayi yana duddubawa, murmushi yayi

"Bayani zakayi mun dalla-dalla..."

Hararar shi Rayyan yayi yana sake hade fuska, dariya Bilal yayi mai sauti wannan karin yana tashi ya janyo kujera ya zauna gefen Rayyan din daya ke watsa mishi wani kallo

"Ni kyaleni"

Ya fadi saboda surutu Bilal zai sa shi yayi, watakila sai yayi mishi bayani sau biyu ko fiye da haka, amman sai ya zaqulo wata tambayar yayi mishi. Haka kuwa akayi, har saida ya kule daya fahimci Bilal din ya gane, surutun kawai yake so ya saka shi. Ganin yayi Rayyan din yayi banza ya kyale shi yasa Bilal komawa kan gado abin shi, so yake ya sake fitar da lissafin a wata takarda daban dan yaga koya fahimta, shekarar shi ta farko ya fadi jarabawa guda daya. Rayyan yaita mishi fada kamar zai mare shi, wani lokacin ko bai niyyar karatu ba yakan dauko yayi saboda masifar Rayyan da ba karewa takeyi ba.

Ranar ne karo na farko da yaji kamar yayi dissapointing din Rayyan din, yanayine da baya so ya kara faruwa. Duk da kwakwalwar su ta bambanta, yana iya kokarin shi. Rayyan zanen shi yaci gaba dayi, amman baya tafiya yanda yake so, saboda yau ya kasa rufe gabaki daya tunanin shi kamar yanda yakanyi a lokutta irin haka. Layla ce manne a ran shi, tun jiya bai ganta ba, har wayarta ya kira amman a kashe. Yanzun ma wayar da take ajiye kan tebir ya dauka ya duba ko ta turo mishi sako, amman shiru, sake gwada kiranta yayi yana jin bata shiga ba, kamar matsalar network tunda ba'a ce mishi a kashe take ba

HausanovelWhere stories live. Discover now