20

8 0 0
                                    

13 Dec, 2020

(An kirkiri Airport a Zaria domin tafiyar labari badan akwai ba)

20

Lokaci zuwa lokaci wanda yake kujerar kusa da shi a cikin jirgin yakan ja karamin tsaki saboda yanda Rayyan din yake bubbuga kafar shi a kasa cikin kosawa. Gani yake kamar jirgin baya sauri, baisan menene a nannade tare da harshen Bappa da kalaman shi ba, amman sunyi tasirin da suka saka shi daukar shawarar shi na tsayawa yayi abinda ya kaishi Bauchi ya wuce wajen, sai su duba idan akwai jirgin da zai tashi daga Bauchi zuwa Zaria, da yake a yar jakar shi duka katikan shaidar shi suna ciki, na makaranta, katin zabe da kuma katin shaidar dan kasa. Bappa na dubawa kuwa yayi nasarar ganin akwai jirgin da zai tashi karfe biyar da rabi na ranar.

Har suka gama abinda sukeyi a camp wajen azahar suka dawo hotel room din Rayyan bai daina mamakin yanda akayi Bappa ya saka shi zama a Bauchi har wannan lokacin ba, saboda gabaki daya hankalin shi yayi Zaria. Bai sake gwada kiran lambobin su Bilal ba duk ranar, wayar shi dai tana hannun shi, yana gudun kar ya sakata ko da a aljihune wani a cikin su ya kira ya zamana bai samu ba. Har airport din ma Bappa ne ya raka shi, a hanya ya tsaya ya sai mishi strawberry yoghurt, da yake yana da sauran biskit a jaka saiya hada ya dan sakama cikin shi, jiri har dibar shi yake idan ya mike, kuma yasan yunwa ce.

Bappa ya zauna da shi har sai da lokacin tantancewa yayi sannan suka mike a tare

"Nagode... Nagode sosai"

Rayyan ya tsinci kan shi da furtawa, saboda shine kalaman da zai iya fitowa da su da kalar karamcin da Bappa yayi mishi. Kai kawai ya jinjina ya furta

"Sai munyi waya"

Shima na shi kan ya jinjinawa Bappa, bai tabayin aboki ba balle ya san yanda yake. Amman yanajin da rayuwa ta hada shi da Bappa da wuri, watakila da sun zama abokai. Bayason mutane, amman Bappa yana mishi daban, ba shi da lokacin tunani akan abin saboda su Bilal da suka kara taso mishi suna danne duk wani kwanciyar hankali da yake tare da ita. Da su a manne cikin kan shi suka sauka garin Zaria. Kafafuwan shi kamar basa mishi saurin da ya kamata yau haka yake ji lokacin daya karasa bakin titi da yake da yar tafiya daga cikin airport din. Mashin ya samu zuwa gida

"Dari biyar"

Mai mashin din ya fadi, kai kawai ya daga mishi yana hawa

"Kayi sauri dan Allah"

Rayyan yayi maganar da wani irin yanayi a muryar shi, har sai da mai mashin din ya dan duba ta mudubi ko zai ga Rayyan din da kyau, ko a cikin abokai lokacin daya fara koyon tuqin mashin din "Dan asabe ganganci" ne lakabin shi, yanzun ma sunan Dan Asabe ya bace sai ganganci din, yanda yake jan mashin idan yana tuqi kowa mamakin samun kwastomas din shi yakeyi. Musamman idan ya busa hayaqin wiwi din shi, bakin shi babu hakora wajen biyar saboda hatsarin da yakan yawaita samu. Tabbas yau ko labari yaje ya bayar na cewa wani ya nemi ya kara gudu da shi a mashin babu wanda zai yarda.

Daman ance in da ranka zaka sha kallo, yau ya dauko mahaukaci. Sai yake jin shi a tsorace da Rayyan din, wani mahaukacin tas zaka gan shi, saika saki jiki kaji saukar duka. Haka suka lallaba harya sauke shi. Kafafuwan Rayyan din yaji suna mishi rawa, kamar suna son ce mishi ba zasu iya karasawa da shi cikin gidan ba. Zuciyar shi bata kara gudu ba sai da ya karasa tsakar gidan, har wani numfashin tashin hankali yake fitarwa, dakyar ya karasa dakin su yana ganin kofar a ture, daga hannu yayi cikin tunanin ya kwankwasa ko ya tura, ko kuma ya gwada saka mukulli. Karshe ya tsaya kan shawarar turawa, yaga dakin ya bude, duk da gidan akwai hasken wutar lantarki, dan ga mutanen cikin gidan nan sunata shige da fice, dan ko sun mishi magana ma bai kula da su ba.

Yana tura dakin ya ga duhu, makoshin shi ya bushe kamar an zuba ya shi, switch ya laluba ya kunna, duk yanda ya sha cin karo da tsayuwar bugun zuciya a karance da kuma a videos bai taba tunanin haka abin yake ba sai yanzun da ganin Bilal a kwance a kasa kamar gawa ya saka tashi zuciyar tsaya na dakika kafin ta soma aiki tana wata irin bugawa, wannan karin kafafuwan shi duka sunyi sanyi, gwiwoyin shi kamar an buge su da guduma haka yake ji, kasa yayi gabaki dayan shi. Da rarrafe ya karasa inda Bilal din yake yana dora hannun shi a jikin Bilal din

HausanovelWhere stories live. Discover now