Chapter 9

15 1 0
                                    

Nov 17, 2020

09

Shi sam baiga dalilin da Haris zaice tare zasu koma makaranta ba. Ya fahimci zumudin da Bilal yakeyi, duk da baiji shi ba sam a tafiyar farko da zaiyi. Yanzun ne yake jin dadi da Bilal din zai kasance makaranta daya da shi. Amman yana da tabbacin surutun da zasu dingayi shi da Haris kafin su sauka Zaria kan shi yayi ciwo. Shisa ya zabi yau din a matsayin ranar da zai koma, kawai saboda Haris yace zaiyi gaba, amman ya nace ya zauna jiran shi.

Yau ma tunda ya tashi yake jan jiki, duk da hakan na da alaka da hankalin shi gabaki daya da yake kan Layla. Sam baiji motsin ta ba, ya dade a bakin kofa da safe yana ganin shige da ficen yaran gidan har suka tafi makaranta, amman bai ganta ba, yaso ya tambayi wani ko jikin ne yasa bata fito ba, amman gaisuwar da suka dinga mishi ce tasa bakin shi yin nauyi saboda surutun har ya fara hawar mishi kai. Haka ya gaji ya koma, ga kasa da baisan waya shigo da ita dakin ba, sai da ya kara sharewa sau biyu tukunna yaji ya taka tsakar dakin da ya sha tayal ya mishi dai-dai.

"Kai fa muke jira... Kana ganin har biyu ta wuce, dare kake so muyi?"

Bilal ya fadi yana shigowa dakin, kafafuwan shi Rayyan ya bi da kallo

"Kai ka shigo da kasa, ban san sau nawa zance ka dinga cire takalminka a bakin kofa ba, har takalmi na siyo na yawo a daki, amman baka amfani da naka"

Numfashi Bilal ya sauke, yana zare takalman daga kafar shi, ya saka hannu ya dauka yana fitar dasu bakin kofa, kwana biyu da Rayyan din baya nan wannan ka'idojin na shi duk ya manta su, karasawa yayi ya zauna gefen gado

"Yanzun ba zaka wanke hannun ka ba, ka taba takalmi haka zaka kama kofi, yasa na daina hada kofuna da kai"

Numfashi mai nauyi Bilal yaja yana fitar wa

"Hamma ka sama mun lafiya, hannun ka ne ko nawa? Maganar da ake so kayi ba ita zakayi ba, sai kace bakin ka ya gaji da magana, amman baya taba gajiyawa kan tsegumi"

Duk surutun shi sama-sama Rayyan din yake ji, hankalin shi yayi nisa wajen tunanin ina da ina takalman Bilal din suka taka, wacce kazantar ya kwaso da su ya kuma saka hannu ya damuka, wannan matsalar shi ce kamar yanda ya fada, amman Rayyan din bayason yaje ya taba mishi wani abu da wannan hannun nashi daya dauki takalma. Ya dauka surutu da mutane ne abinda yafi tsana a zamantakewa, sai da ya fara girma yagane kazanta ce abinda yafi tsana, tsantsanin da yake da shi ba karami bane ba.

Lokutta da dama baka raba shi da karance-karance kan kwayoyin cutukan da suke rayuwa da mutane a mu'amalar yau da kullum. Yana son lafiyar shi, yana bala'in ririta lafiyar shi, tana jerin abu na farko da yake roka a dukkan addu'ar shi, shisa yake kara taka tsantsan idan ya tsare da iyawar shi, Allah saiya taimake shi. Dan ya kula mutane basu da wani buri daya wuce su ja mishi amai da gudawa. Haka shekaranjiya da suka dawo daga masallaci Bilal ya siyi wani rake, kuma har yake mishi tayi, tun suna hanya ya fara gabza kamar bashi da hankali.

"Ka tashi dan Allah ka shirya mu tafi"

Bilal din ya fadi yaba dorawa da

"Hamma..."

Ganin da yayi kamar Rayyan din baya jin shi, sai lokacin ya kalle shi

"Meye? Karka dameni, kuyi gaba da Hamma Haris mana, dole sai kun tafi dani?"

Ya karasa maganar yana mikewa, shi ya gama shiryawa, Layla ce baigani ba

"Ni na gama shiryawa, ka tashi..."

Rayyan ya furta kamar an mishi dole, mikewar yayi, kafin yai wani motsi Haris ya daga labulen dakin tare da yin sallama, idanuwan shi ya tsayar kan Bilal dan yasan ko Rayyan yayi wa magana kai tsaye ba lallai ya amsa shi ba

HausanovelDonde viven las historias. Descúbrelo ahora