Jan 4, 2021.
28
Kwance take, dakyar take iya daga idanuwanta. Haris ne ma ya kirata a waya yana tambayar ta ko tana son cin wani abu, tace mishi yoghurt. Da yawa ya siyo ya kai mata daya har daki, sauran yace ya saka mata a fridge. Shima ko rabi bata sha ba ya fita daga ranta, kusan aman shi tayi. Hannun ta dafe yake da cikinta da ta fara ganin alamar ya dan taso, saboda bata da tumbi da can. Lumshe idanuwanta tayi tana jin suna mata wani radadi saboda kukan da takeyi, ko hasken waya bata so a cikin idanuwan nata. Bata taba tunanin zata kwana ta yini ta sake kwana ta yini tana kuka ba sai da labarin rasuwar Bilal ya daki kunnenta.
Ita safiyar ranar da akayi rasuwar bacci ta dan samu, saboda ta kwana tana kuka, ta kwana cikin tashin hankalin rabuwa da Rayyan, ta kira shi yafi sau hamsin bai daga ba, ko ya daina son ta tana son ya saurareta, tana son ta fada mishi batasan yanda akayi abinda ya faru din ya faru ba. Tana son ta bashi uzurin da kowa ya kasa yi mata, ta kare kanta kamar yanda Ayya ta kare Bilal, yanda ta kira abinda ya faru da su da sunan kuskure. Saboda idan Rayyan da kan shi ya barta ina zata je? Wa zai karbeta? Waye ba zai dora alhakin komai a kanta ba?
Kuskurenta ne daukar kafafuwanta taje gidan su, ta rigada ta san wannan, bata tsaya ba har dakin su. Amman batajin tana da laifi a cikin jirin da ya fara dibarta cikin yan mintina kadan da zamanta. Ta zauna ne ta dan huta, ta maida numfashi, bama zata ce ga dalili kwara daya da yasa ta zauna ba, tunda ko Rayyan yana nan ba ko yaushe take zama ba, baya bari, da ta shigo yake mikewa. Da taji maganar shi kamar yanda ya hana mata zama a dakin, da gidan ma gabaki daya ko da suna nan, balle kuma basa nan, watakila da bata zo in da take ba yanzun.
Da tarin burin da take da shi na auren Rayyan bai ruguje ba. Da bata ga tsanarta a cikin idanuwan shi ba. Abbu ya kara hargitsata da furucin shi, saboda idan duniya duka zata hade da ita a waje daya bata hango yanda zata fara zaman aure da Bilal ba. Ko na minti daya zuciyarta bata taba doka mishi ta wannan fannin ba, yanda zata fara kwanciya ta tashi da shi karkashin inuwar aure da sanin ya rabata da komai da take takama da shi, banda Martabar ta harda Rayyan, harda Hamman ta. Ba laifi take kokarin dora mishi ba, amman zata iya farawa idan suka kasance inuwa daya.
Tashin hankali ne shimfide take hangoma rayuwarta da ta birkice cikin kankanin lokaci. Da tunani kala-kala a ranta har gari ya waye, da tayi alwalar asuba ma sai da ta koma ta dan kwanta saboda sanyin da ta dinga ji da yake akwai zazzabi a jikinta. Ta samu bacci ne ba jimawa, dan ji tayi kamar tana bude idanuwanta ta mayar da su ta rufe ne taji kamar an fasa kuka, yanayin da ya sakata bude idanuwa babu shiri, ba kuma karya kunnuwanta sukayi mata ba, kuka ne, dakyar ta iya saukowa daga kan gadon, da yake window din dakinta ta wajen harabar motocin gidan ne, zagayawa tayi ta leka ta hango kusan kowa na gidan a wajen. Kafin kunnuwanta su tsinto mata
"Bilal ya rasu"
Cikin muryar da bata san ko waye bama, bangon wajen ta dafa tana runtsa idanuwanta, duniyar na wulwula mata kafin wani abu ya tsirga mata a ciki yana saka bayanta amsawa. Babu shiri ta durkusa saboda azabar da ta dirar mata ga kidimar mutuwar Bilal da take mata kamar almara, sunan Allah duk wanda yazo bakinta shi take kira, tana dafe cikinta da kamar ana tsinka wani abu a ciki, kafin wasu irin hawaye kamar an kwance wani abu a cikinta su fara zubo mata. Sai a cikin kwanakin mutuwar washegari ta fara jero neman gafarar Allah saboda sabon da tasan ta dinga yi na yanda za'ayi Bilal ya rasu.
Kafin wani matsanancin tsoro ya tsirga mata na yanda zai fara amsa tambayoyin shi a kabari, tunanin ko abinda ya gifta a tsakanin su zai rushe tarin ayyukan shi. Ranar bata iya runtsawa ba, gani take kamar da ta rufe idanuwanta itama mutuwa zatayi gaba da ita. Kuma tana jin daudar da take da ita tafi ta Bilal, duk laifukan shi ba zasu wuce abinda ya gifta a tsakanin su ba. Amman ita kam duk wani karami da babban laifi haka ya dinga gifta mata a rai yana kara hautsina mata lissafi.