1

600 47 4
                                    

*Ina farawa da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai.*
_______________________________
*ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....kazalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai da ke cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana ya ke tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shi ne; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine me cece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!...*

*Kano, ƙarfe uku na Yamma.*
Sanye na ke da maroon hijab wanda ya ɗauki kyawuna matuƙa, a yayinda Farhana ke yafe da ƙaramin gyalenta wanda itama yay ma ta kyau sosai. Cikin takun natsuwa da hankali muke fitowa daga cikin Sahad Store da ke nan anguwar zoo road. Ledar hannun Farhana kawai zaka kalla ka gane cewa ba ƙaramar siyayya ce muka yi ba. muna tafe muna magana a cikin nishaɗi, duka idanuwanmu kewaye da gilashi, sai dai akwai banbanci a tsakanin gilashina da nata,  domin nawa na magani ne wanda ake kira da medical glass, ciwon idon da na gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata rabo da shi a kullu yaumin.
Zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key.

"Wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin da na ke kunna Ac'n motar.

"Yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower".

Cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani".

Na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggona na san yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima".

Farhana ta ce,"kinga ba wannan ba ma, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa".

"To amin dai, Allah ya nufemu da rutsa shi".
Na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare da ni.

Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki.
Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu samu me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa da ke mana bayani bamu yi ba muka fice dukkanmu rai a ɓace, dan ni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin da na san ƙarya ce kawai yake gilla mana.

AL-HUSSAIN CompleteOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz