*(2)*
kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. Sama-sama na ke jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?".Ta faɗa tana ƙarasowa inda na ke. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"A'a ban san shi ba, ban ma san waye ba".
Cikin ƙarfin hali nayi magana ina daɗa dafe kaina, ta matso kusa gare ni da tashin hankali tana dafa kan nawa ta shiga jera min tambayoyin,"lafiya?".
A wannan lokacin babu abinda na ke so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsakuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba.
"Na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace wata mahaukaciya".
Muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa akaina. magana na ke so nayi amma na kasa, sai laɓɓana da ke aikin yin rawa, ko idona da ke buɗe kaɗan dishi-dishi na ke gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen, tayi azamar riƙe ni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi.
Hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana kuwa bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa na san kuka ta ke na kiɗima, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n da na san ba shi da hannu a wannan halin da na shiga.
Ta dage akan sai ya faɗa mata abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi mata magana ba.Kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya same ni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba. Da ace ta san irin azabar da na ke ji acikin kaina, da kuma hoton da ke haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji.
"Na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwaggo?".
Kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar da ke wucewa ta cikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da na ke ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi.
"Ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan sai na yi maka ihu, ka zo ka sakar min ƴar'uwa dan na san koma menene kai ne sila,, kai maye ne ka kamata mugu".
Duk da cewar ba sosai na ke gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, a haka na ƙara damƙe hannunsa gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zai ci gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min,"Barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni".
Shi yasa komai zai ƙara faruwa da ni ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu lafiya kuma babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nayi sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ɗin ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya in dawo daidai da yanda na ke.
Sai naji nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa.Sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa, kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron da ke bin mahaifiyarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu na ke dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi a nan, sai dai komai zai faru ya faru da ke.
Gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai da na jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi? Kin manta halin tsananin da kika shiga ne yanzu?".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...