30

327 14 3
                                    

Ina tsaye bakin titi motan Yaya Haidar ta tsaya gabana, a tunanina ma ɗaukana zai yi, na taho da zumuɗina na kai hannu zan buɗe motan kawai naga ya figi abarsa, haushinsa ya kuma tuƙeni dan dama aciki nake da shi, ban taɓa sanin ya tsaneni haka ba sai da akayi maganan aurenmu da Yaya, lokacin da Baba yace bai amince ba yay ta min dariya a ɓoye, yana kuma nuna farin cikinsa a fili. abun ya dinƙa bani mamaki dan ni da girmana ban taɓa ganin dariyarsa haka ba, har yana ce min an gaya min kowa mahaukaci ne irina da za'a ɗauki mara asali a bani, to tun daga nan ma ko zamu bugi juna bana gaishe shi, sai dai ya wuce na wuce. sai biyar na yamma muka gama lectures, ina fitowa daga hall na hangi Malama Muhsina zata shiga motarta, na damƙawa Intisar jakata na ƙarasa wurinta da sauri ina kiran sunanta, ta dakata da rufe murfin motan, ina nishi na gaidata, ta amsa min da fara'arta. "Beauty lafiya dai na ganki haka?". ta tambayeni tana dafa kafaɗata. ƙasa nayi da kaina saboda tsananin faɗuwar gaban da nake ji da kuma fargaba, na tafi duniyar tunani ta katseni ta hanyar kiran sunana. "Beauty wani abun ya faru ne?".
ta fito daga motar tare da ɗago fuskata, ina kallonta kawai naji saukar hawaye a fuskata, lokaci guda kuma na fashe da kuka, a kiɗime ta shiga tambayana mike faruwa, ta kwantar da kaina bisa kafaɗarta tana shafa bayana, ni dai acikin zullumi nake kuma a fargaba nake, yanzu idan ya kasancewa babu wata alaƙa da Yaya da su Proff ya zanyi da rayuwata?, ni ko da badan soyayyarmu ba zanso ace duniya ta san shima yana da asali. muryana na rawa nace,"Malama kwana biyu banga Proff ba". sai tai murmushi mara sauti har ya bayyanar da haƙoranta tace min,"Brother ai yayi aure". na waro ido a zabure ina dubanta da mamaki, itama kuma tana kallon reaction ɗina da mamaki, ban kai ga magana ba tace,"hala ba ki sa ni ba dama?". knooding kaina kawai nayi mata, sannan nace"Allah ya sanya alkhairi, amma dai yana ƙasar nan ko?". na tambaya jiki a sanyaye. kai kawai ta ɗaga min alaman ehh, sai nace ko zata bani numbansa, tace yace kar ta ba ni amma zan iya zuwa muje ta rakani inda yake, na shiga mota muka je can wajen faculty of science, wani haɗaɗɗan office muka shiga, yana daga kan kujera yana juyawa muka shiga, sai daya sallami baƙonsa sannan ya maido da hankalinsa kanmu. haka kawai kuma sai naji ina jin nauyinsa, a kunyace na gaida shi ya amsa min aciki, Nan Malama Muhsina tayi masa bayani, yay min kallo ɗaya yace, "lafiya?". ina wasa da yatsuna nace,"dan Allah Sir kayi haƙuri da abinda na maka". "karki damu". shine abinda yace yana ɗauko takarda ya fara rubutu, na kalla Malama Muhsina muka haɗa ido, na karayar da kai sai ta kama hannuna muka ƙarasa gaban table ɗinsa taja min kujera tace na zauna, ya dakata da rubutun da yake ya ɗago ya dubemu ni da ita yace,"wani abunne kuma?". "Brother kayi haƙuri mana. tana sonyi magana da kai ne". "ta tsaya a tsaye ta faɗi ko menene". ya faɗi hakan ba tare daya dubemu ba. nace,"Sir dama don Allah ina gayyatarka ne zuwa gidanmu gobe, dan darajan Allah karka ce a'a". tsayawa yay yana kallona da nazari, kamin ya taɓe baki yace,"naje gidanku a matsayina nawa kenan?". nai juyi da idanuna, na yatsine fuska sannan nace,"ni dai don Allah kawai ina so kaje ne". shiru yay baice komai ba har sai da Malama Muhsina ta sanya baki tukunna yace,"oak sai nayi shawara da zuciyana". daga haka yace mu fice masa a office.
na taɓe baki na harare shi ta ƙasan ido, na tafi gida cike da zullumin son ganin ya gobe zata kasance, Allah yasa dai tunanina da mafarkina na jiya ya tabbata. washe gari kusan huɗu na yamma muna zaune a parlo mai gadi ya shigo, ya gaida kowa sannan ya kalleni yace,"Sabina kinyi baƙo a waje". "ni kuma?". na tambaye shi. na san dai ba Proff bane domin da shine kirana zaiyi, ko da bai kirani ba Malama Muhsina zata kirani tunda tare na roƙa da su zo. "kace bana nan". shine abinda nace da shi ina maida hankalina kan wayata. Anty tace da shi,"Audu je ka ce tana zuwa". na ɗago ina marairace fuska zanyi magana ta ɗaga min hannu alaman bata son jin komai, haka na tashi ina ƙunƙuni na fice, ina kallon Gwaggo ma ta bini da ido tana aikin kyaɓe baki.
yana jingine da jikin mota na same shi ya harɗe hannayensa a ƙirji, nayi masa kallon sama da ƙasa kamin na ɗauke kaina, ganin banda niyyar ƙarasawa inda yake yasa shi takowa da kansa yazo inda nake, yay sallama na amsa babu yabo babu fallasa, tun bai fara magana ba na dakatar da shi da cewa,"minti ɗaya kacal". ƙasaitaccen murmushi ya sa ki yace,"ranki ya daɗe minti ɗaya ai kamar busowar iska ne, ba zai isheni isar da saƙon da nake tafe da shi ba". ban kai ga magana ba sai ga Yaya Haidar, na wani ɗauke kai gefe guda na kama ƙugu kamar wadda ke shirin dambe da shi. baƙona ya bashi hannu suka gaisa, ya giftamu ya shiga gida sai kuma ya dawo, ya dafa kafaɗar mutumin su kai gefe guda, tsawon minti uku suka ɗauka suna magana, ban san me Yaya Haidar yace da shi ba naga ya dawo ya shiga mota ya tafi. shi kuma yazo ya wuceni yay cikin gida, na ɗaga kafaɗa na wuce nima. zan shiga side ɗinmu kiran Yaya ya shigo wayana, naƙi ɗagawa saboda ina faɗa da shi. ko zama banyi ba saiga Yaya Haidar ya shigo parlo ransa a ɓace, kaina ya tsaya yana aikin huci, tun bai kai ga furta komai ba na saka kuka ina faɗin,"ni dai ban san me nayi maka ba a rayuwa ka tsaneni, sai kace ki ba ƙanwarka bace". yasa ƙafarsa ya ta ke min tawa cikin salo na mugunta, nayi ƙara na miƙe tsaye gabansa nima ina huci nace,"Allah ya isheka abunda kake min. duk girman da nake baka bai isa ba dole sai kaja abinda raini zai shiga tsakaninmu". ya hankaɗani kujera na zauna, cikin kakkausar murya yace,"wallahi tallahi duk ranar dana kuma ganinki da wani a waje sai belt ɗin nan ta tsinke a jikinki". "tunda gaka ubanta ba". Gwaggo dake kallonmu tun ɗazu tai maganar tana jifansa da harara. bai saurareta ba yaci gaba da cewa,"ki bar ganin waccen tsohuwar tana ɗaure miki gindi kina abinda kika ga dama, na rantse miki da Allah a wannan karan banga mai hanani jibgarki ba acikin gidannan". "da yake ni kuma tsayawa zanyi, kuma Allah ba zan fasa kula samari ba tunda dai ba kai zaka aureni ba". na ɗanyi ƙarar wahala nace,"Gwaggo kice ya sakar min hannu".Gwaggo na kallon Anty tace, "Zara'u tun kamin raina ya gama ɓaci na tashi naiwa wannan fitsararran yaron rashin mutunci kice ya bar ɗakin nan". ta faɗa tana haɗawa da ƙwafa. yay banza da Anty ma dake masa maga har sai daya waiga yaga Gwaggo tayo kansa da taɓarya tukunna yay saurin sakar min hannu daga damƙar da yay min ya fice. ya barni da nishin wuya dan kamar an ɗaureni da ƙarfe haka nake ji. ina jin Anty sai sakin murmushi ta ke kaɗan kaɗan, na ɓata fuska nace,"ni dai Anty karki ce komai". ta kuma murmushin daya bayyanar da haƙoranta tace,"ai bama komai zance ba jikar Gwaggo". da tsokana Amina dake kusa da Gwaggo tana tayata ɓare gyaɗa tace,"ai mun gama ganewa mu dai, ah to". na wurga ma ta harara tace, "dilla rufe min baki". ana idar da sallar magriba Malama Muhsina ta kirani a waya tace min gasu a ƙofar gida, da zumuɗi na miƙe ko adu'a ban ƙarasa ba na fito ina cewa,"Gwaggo yau za ki girgiza da wani al'amari matuƙa. bama ke ɗaya ba kowa na gidan nan sai ya girgizu". "shirmammiya kawai". tace da ni ba tare da ta kalleni ba. Yaya Abba yace, "ina za ki?". "baƙi nayi yanzu zan dawo". ban kuma tsayawa jin cewar ɗaya daga cikinsu ba na fice. da kaina na turo Proff a kekensa har parlonmu, gabana sai dukan uku-uku yake. muna shiga Gwaggo ta kallemu ta ɗauke kai tana cewa,"Allah ya maida ƙoƙo masaki, ita dai cuta ba'a ƙarya da ita ko a kwaikwayeta, atou ni gaskiya nake faɗa". ta faɗa a nata tunanin duk Yaya ne. dariya nayi na ƙarasa da shi gabanta, taja tsaki tace,"ka ga zagalo ka kiyayeni ina faɗa maka. kasan dama haushinka nake ji yau kwata-kwata baka zo ka sha maganinka ba, shine yanzu zaka zo ka sa ni a gaba da shirmenku da baya ƙarewa kai da ita, to yasin ka kiyayeni ko na ɓarar da kai a keken nan, ka duba fa yanda maganin nan ke maka aiki, ka fara zama ɓul-ɓul abinka. wannan da nono kake sha ai yau dole na yayeka". daga Proff har Malama Muhsina kallonta suke da nishaɗi da kuma burgewa, ta kuma kallonsa a fusace tace,"wai kuwa ba za ka kauce min daga hanya ba sai na kifar da keken". nai saurin janye Proff daga gabanta dan nasan zata aikata. kusa da Yaya Abba na zauna na ƙwace wayar hannunsa nai masa nuni daya kalla inda Proff yake, sai yanzu ne ya ɗago ya kalle shi ya girgiza kai kawai. shima yana cewa,"ka tashi daga ɗan wasan ƙwallo ka koma jarumin film kenan". shima dariya nayi masa, su kuma duk aka ɗaure musu kai, dan Gwaggo miƙewa tayi ta dungure masa kai tana cewa,"dama ace keken ya maƙale da kai ko zuwa safiya ne naga ta ƙaryar kwaikwayo". ina ɗora haɓata a kafaɗar Yaya Abba nace,"Gwaggo ki dawo ki tarbi baƙi, dan wannan ba jikanki da kika sa ni bane, saboda sababi ma kin gagara lura da ta kusa da shi". tace,"na ganta sarai. ba zan dai kulata ba ne tunda bai sanar min da zuwanta ba". cikin rashin fahimta Malama Muhsina tace da ni,"Beauty ya dai?". nai mirmushi nace,"So nake su gama nasu mamakin kamin kuma na jefa ku a al'ajabi". tai min kallo mai kama da harara, na ɗauko ruwa na kawo musu, shi dai Yaya Abba bina da ido kawai yake, ina jinsa ya cewa Gwaggo wannan yarinyar kuwa anya lafiya, tace to ainima kaga na fara tsorata da lamarinta sai nake ganin kamar mutanen nata ne suka kawo ma ta ziyara. ni kuma abunda na tsani ji kenan tace wai mutanena, hakan yasa na doki ƙafa a ƙasa nai tsoki ina cewa,"Gwaggo ni fa lau nake, wannan ba Yaya bane. na tsinto shi ne shima kuma ina da yaƙinin da alaƙa tsakaninsa da Yaya". "shima a bolar kika ɗauko shi?". ban kulata ba na fita ina cewa su Proff suyi haƙuri 2mints. ni da Yaya muka dawo, muna shigowa parlon idon kowa ya dawo kanmu, kuma a lokacin kowa ya miƙe a razane harta shi Proff dake zaune sai daya razana yaja kekensa baya, shi kuma Yaya kallon ikon Allah yake yi, tsoro kuma ya fara ɗarsuwa a zuciyoyin kowa.
da mamaki sai naga Malama Muhsina ta doka tsalle ta iyo kansa ta ƙanƙame shi tana ihun murna. "babu tantama babu shakku tabbas kai Hussain ɗinmu ne, dama Mom tace jiya tayi mafarki da kai kace ka kusa zuwa garemu". ta sake shi tana shafa fuskarsa, Mamaki ya hana kowa magana saini dana haɗiyi wani yawu nace. "Malama me yasa za ki ce haka?". ta kama hannuna tana hawaye tace,"aina kuka same shi? ko kuma nace mene alaƙarku da shi?". "Yayana ne fa". na faɗa da ƙinƙina. ta girgiza kai ta juya ga Proff wanda yay mutuwar zaune tace,"Brother ya kake ganin abun kamar a mafarki ko?". kasa cewa komai yay sai hawayen farinciki daya ya goge. ta ƙara cewa,"ni dama jiya tunda tace min tana so muzo gidansu ne saboda akwai mai kama damu nasan cewa da wuya da kamar wuya ya zama ba Hussain zan gani ba, naƙi faɗa muku ne kawai dan kar muzo aga akasin abinda muka ƙwallafa a ranmu".
a wannan lokacin da ta ke magana idon Alhussain akan fuskarta yake, kallon bakinta yake da fitar kowacce kalma daga bakinta, tabbas zai iya yin rantsuwa wannan yarinyar itace matar dake zuwa masa acikin mafarki, kawai banbancin guda ɗaya ne, waccen dattijuwa ce, wannan kuma matashiyr budurwa ce, sannan sautin maganarsu ba ɗaya ba ne, amma indai ata iya kamannin zai bari bata da maraba da ta cikin mafarkinsa.
ya rufe ido ya buɗe cikin abinda baifi second ɗaya ba, kamin laɓɓansa su tale a hankali da faɗin,"su wane waɗannan ɗin? wane wannan mai kama dani?". Yaya ke min wannan tambayar, kuma banbi takanshi ba na fuskanci su Yaya Abba ina cewa, "ba ina faɗa muku ba kuna ganin kamar na samu taɓin hankali ne har kuke cewa aljanu sun buɗe min ido". sannan na karkato kansa ina daɗa cewa,"Yaya ina jin ajikina su ɗin ahalinka ne duba da tsananin kamar dake tsakaninku". girgiza kai ya hau yi yana cewa,"ko kusa, ni bana da wasu ƴan'uwa. ni ka ɗai ne a rayuwata sai ku da Allah ya bani daga baya..ita wannan yarinyar ma da kike gani itace na baki labarin cin mutuncin da tai min wancan ranar". sai ya dubi Malama Muhsina yana cewa,"ko ba kece kika ce min ɗan gidan matsiyata ba?". sai kawai ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka da faɗin,"dama kai na faɗawa haka? dan Allah kayi haƙuri 2wins bro, ban san kai bane, inda nasan kaine babu ta yanda za'ai na faɗa maka hakan...kai fa jinina ne, mu uku haka aka haifemu a rana ɗaya, lokaci ɗaya, kuma mahaifa ɗaya, amma ƙaddarar rayuwa ta rabamu na tsawon shekaru masu yawan gaske...dan haka ina roƙonka dan Allah kayi haƙuri hasali ma wulaƙamci ba halina bane, lokacin daka bigeni ina cikin ɓacin rai ne shi yasa har na yaɓa maka maganganu masu ɗaci, kuma daga baya nayi dana sani dan sosai Anie tai faɗa da kuma nasiha". sai kawai yasa hannu ya tureta a jikinsa yasa kai zai bar ɗakin, dan gani yake kamar wannan abun shirin film ne, yana ganin abunne kamar wani abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba a duniyar zahiri.
sai dai a sanda yake ɗora ƙafarsa a bakin ƙofa Maganar proff ta dakatar da shi, kuma maganar tasa ce fa ƙara furgita kowa, dan jin muryarsu exaclty. hakan yasa shi dawowa da baya yana ƙarewa mame kama da shi dake zaune a keken guragu kallo, sai dai duk ta yanda yaso ya ƙaryata zahirin abun ya faskara, illama wata ƙauna ta daban da bai taɓa jin irinta yaji tana huda ƙofofin jikinsa akansa, yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba a game da mutane biyun da suke ikirarin kansu da su ƴan uwansa ne, duk da cewar har yanzu Hassan ɗin bai ce komai ba game da hakan, kallon ido cikin ido suke su biyun, yayin da acikin ƙwayar idanuwan kowannensu ke haskawa da hoton wasu yara su biyu suna riƙe da hannunsu, suna ta ihu, suna kuka me ban tausayi, kuma ba tare da sun san me ya rabasu ba, ƙarar ihun kukansu na ƙarshe ya zamana babu wanda yasan ta yanda hannayensu ya rabe. a yanzu ji suke kamar yanzu ne wannan al'amarin ke faruwa, cikin kan Hassan da Hussain wannan kukan rabuwa shi ke amsa kuwa acikin kunnuwansu. da sauri kuma a tare duk su biyun suka ɗora hannu suka toshe kunnuwansu suna masu rumtse ido.
abunda kowa bai sani a wannan lokacin ashe Gwaggo tuni ta suma, sai yanzu da Amina tai magana mukayi kanta duka, aka yayyafa ma ta ruwa ta farfaɗo tana wasu surutai kamar na rufeta da duka saboda takaici. cewa ta ke wai ita dama tun usuli tasan Yaya ba mutum bane lamarinsa yafi kama dana mutanen ɓoye, dan Allah a kirawo Haidar yazo ya ƙonasu. hankalin Yaya a tashe ya janyota jikinsa yana ma ta magana, sai kawai ta tsala wani uban salati tana karanto wa'innahu min sulaimana wa'innahu bismillahi rahmani rahim. faɗa ta ke tana ƙara maimaitawa, shi kuma yana ƙoƙarin fahimtar da ita. sai dai a wannan lokacin ni kuma hankalina gaba ɗaya ya tattara kan Malama Muhsina dake faɗin,"ehh wallahi Mom, komai fa. Mom kawai kizo kina ganinsa za ki tabbatar da ɗanki ne".
daga cikin wayar Hajiya Fa'iqa tace da Muhsina,"Daughter ya yanayin yarinyar yake?". Muhsina ta kafe Sabina da ido tana karantowa Hajiya Fa'iqa yanayinta. ta cikin wayar Hajiya Fa'iqa tace,"a bayan wuyanta ki duba min akwai?". Muhsina ta zauna kusa da Sabina, yayin da ta yaye mayafin dake jikinta ba tare da ta sani ba, sannan a hankali kuma muryarta a sanyaye ta fito da faɗin,"ehh Mom akwai".
abinda Muhsina tace da ita kenan, kuma a daidai wannan lokaci daga gefen gadon da Hajiya Fa'iqa ke zaune ta zuƙi wata iska ta furzar da ƙarfi, wanda hatta Dad dake shigowa a lokacin sai da yay saurin jefa ma ta tambayar,"Sweart heart lafiya dai?". abu biyu ta ke ji a tare da ita ayanzu, wanda dukkansu babu wanda zata iya kwatantawa, burinta a yanzu bai wuce ta isa inda suke ba, taga duka yaranta a haɗe, ta janyosu jikinta ta rungumesu da tsananin farinciki, da adu'ar Allah kar yasa wata ƙaddarar ta kuma rabata da su. sai dai kuma ta ya ya?, ta ina zata fara? ta ina zata fara yiwa Hussain da Sabina bayani?, da wanne yaren zata yi musu bayanin da su iya fahimta ba tare da dukansu sun shiga wani hankali ba?. "wanne irin kuskure ne wannan da bai sanat da ni shi kuskure bane tun a farko". ta faɗi hakan a fili, yayin da Dad ya ƙaraso gabanta yana tambayanta me ta ke cewa, sai kawai ta miƙe tsaye tana cewa da shi,"Daddy mu fara zuwa ga Yaran nan tukunna".

*A irin wannan lokacin.*
kasa zaman falon nayi hakan yasa na taso na dawo ɗaki saboda kaina da naji yana sara min, haka kuma cikina na murɗawa sosai, dan lokacin dana taso idon Yaya akaina yana tambayana menene nace ya zauna tare da ƴan'uwansa kamin du Daddy su iso zan shiga toilet ne babu komai. sai dai ko dana shigowa ɗakin na zauna a gefen gado, dafe kaina nayi da ƙarfe yayin dana toshe kunnena guda da nake jin kukan jariri, sautin kukan na ƙaruwa da ƙarfin da ba zan iya toshe kunnena daga jinsa ba. sai kawai na kifa kaina akan gado, na rarumo pillow guda 2 na danne kunnuwana, amma sai dai me? kamar ina ƙara ingiziza kukan Babyn ne, kuma a yanzu da nake neman Allah yayi min luɗufi daga daina jin kukan, sai sautin wannan mutumin da nake gani acikin barcina yana faɗin wai in tallafe jaririn, na lallashi ya bar kuka, kukan da yakeyi akan rashin mahaifinsa ne...lokaci ɗaya wasu tarin tambayoyi dake neman fasa min ƙwƙwalwa suka cika cikin kaina, kuma da na rasa ta inda zan sami amsarsu kawai saina fashe da kuka, kuka sosai nake yi, sai dai abinda ban sani ba a wannan lokacin shine, hawayena na sauka ne a saman wata kafaɗa da ban taɓa arba da ita ba sai a yau, kuma ɗago da idona da zanyi wa zan gani?
kuma kallon matar ya haɗe min da jin maganar Gwaggo dake cewa,"kai ni fa ban yarda da wannan lamarin ba daya fi kama da alamara. jama'a duniya kuji min mata, aya zan gasgata maganarki, ina kakar Yara ki dinƙa ce min ke Babarsu ce, kawai saboda kinga kyawawa shine za ki zo kiyi min fashinsu...to kai Auwalu tun iskata bata tashi ba kazo kayi min waje da waɗan nan halittar. kai yau naga abunda yafi ƙarfin kaina, yo zancen wofi ma kenan...kai Haidar zo kayi ruƙiya a gidan nan dan babu makawa mutanen ɓoyen yaran nanne suka bayyana~".

*End Of Book 1.*
*ALHAMDULILLAH.*
_Dukkan Yabo da Godiya su tabbata ga Allah daya bani ikon rubuta wannan littafi kashi na farko, haka kuma ya bani ikon kawowa ƙarshensa a yau lafiya lau....ina miƙo sakon godiya da gaisuwa ga tarin masoyana da suka sami damar karanta wannan littafi, waɗanda muka yi tafiyar a tare...na gode na gode da comment ɗinku, votes da sharing Allah ya biyaku da mafificin alkhairi.._

_Labarin Alhussain Book 1 yazo muku ne a free, yayin da Book 2 zai zamana na kuɗi ne akan farashin naira 300...ayi haƙuri nasan hakan ba zai maku daɗi ba amma nima ina so kuyi min adalci. saboda haka ga mai buƙatar book 2 sai ya neme shi a application na ArewaBooks, acan ne kaɗai zaku same shi dan bani da document kuma magana ta gaskiya ba zanyi document ba...so mafi a'ala in har kina so ko kana so ka shiga ArewaBooks site nasu ko kuma Application nasu ku saya acan, kamar dai yanda kuka saba siyan littafanmu dake OkadaBooks...hanyar siya me sauƙi ce sai dai ga wanda bai gane yanda kan App ɗin yake ba kuna iya tuntuɓar wannan numbern 09031774742 dan ƙarin bayanin yanda zasu siya....insha'Allah zan fara releasing ɗin Book 2 a ranar alhamis 24/03/2022, zan kuma hatta mashi a ranar 1/04/2022 nan da kwana goma kenan. so ga mai ra'ayin bin pages muna iya fara tafiya tare dan tafiya ce da babu fashi da izinin Allah, idan kuma mutum yafi so sai ya kammala to sai ya jira juma'a ta sama idan Allah ya kaimu da rai da lafiya...ga wanda na ɓatawa a wannan tafiyar tamu ina neman yafiya dan Allah._

*ina godiya a gareku masoyana, ina maraba daku a ko da yaushe🥰.*

#Oum Ramadhan.
#mikiyawritersassociation.
#22/03/2022.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 11 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now