*(16)*
*Kano, Bompai Police Station.*
*9:00pm*"Wallahi ba zan yarda ba, kuma ba zan yafe ba, dan haka Officer kayi moving case ɗin nan zuwa court a gobe".
Dattijon da ke zaune kan kujerar da ke fuskantar Officer Yahya Murtala ya faɗa, cikin hargowa yake maganar, yayin da fuskarsa ke ɗauke da tsananin ɓacin rai da kuma tashin hankali. wannan tashin hankalin da ya sameshi tun a ranar da aka sami gawar ƴarsa da aka yiwa fyaɗe.
Officer ya sauke numfashi sannan ya koma baya ya jingina daga jikin kujerarsa da ke juyawa da shi gefe zuwa gefe. biron da ke riƙe a hannunsa a saman leɓensa yay shiru yana nazari, tsawon wucewar daƙiƙa uku tukunna ya sake sauke numfashi ya fuskanci Alhaji Musbahu Wasai ya ce da shi,"Alhaji karfa ka manta har yanzu bamu da wata ƙwaƙwƙwarar hujjar da zamu tura wannan yaron kotu, zarginsa kawai mukeyi, har yanzu bamu tabbatar ba".
Alhaji Musbahu Wasai ya taso masa sama a cikin muryar faɗa yana cewa,"Officer babu wani batun zargi anan. akwai wata hujja da za'a samu ne bayan wacce muke da ita?...sai dai kuma idan wanda yay wannan aika-aikar ne ya biya...".
Bai kai ga ƙarasa maganar ba Officer ya ɗaga masa hannu. "Alhaji ba'a ɗakin matarka kake ba, saboda haka ka iya bakinka anan wurin".
Shiru ya sake ratsa ofishin gaba ɗaya na wucewar wasu sakanni. kamin daga bisani Officer ya ɗaga waya ya kira, cikin daƙiƙar da ba zata haura ɗaya ba Corporal Murshid ya shigo, tsaye daga gefen table ɗin Officer ya sara masa, sannan muryar Officer ta fito cikin bada umarni.
"Corporal".
"yes Sir".
"kaje ka faɗawa Sergeant a ƙara komawa kan yaron nan. ayi duk yanda za'ai musami abunda muke so ayau ɗin nan".Corporal ya ƙara sarawa yana cewa,"Oak Sir".
Daga hakan ya juya ya buɗe ƙofa ya fita. Officer ya kalli Alhaji Musbahu ya ce,"kai kuma kaje zamu nemeka...sai dai abunda na ke so kayi keeping a mind ɗinka shine, hukuma bata gudar da aikinta ta irin tsarinka...mun san abunda muke, mun kuma san abunda ya dace...i hope you get me".Alhaji Musbahu bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana bin Officer da wani irin kallo sannan ya taka ya wuce zai fita, sai da ya je bakin ƙofa maganar Officer ta dakatar da shi. "ina fatan kasan inda ka kawo case ɗinka, Bompai!".
Alhaji Musbahu ya jijjiga kansa kawai sannan ya buɗe ƙofar ya fice.
*9:30pm, cikin Cell.*
Kansa duƙe yake a ƙasa, yayin da hannayensa ke riƙe da kumburarriyar ƙafarsa, ciwon da ke saman goshinsa na zubar da jini kaɗan-kaɗan. yaja dogon numfashi ya sauke tare da rumtse idonsa sakamakon zafin ciwukan da ke ratsa ilahirin jikinsa._"Ya Rahman ka kawo min agaji, ka kawo min ɗauki, ubangiji ka wanke ni daga wannan laifin da ake zargina da shi. Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar"._
Zafin ciwon kafaɗarsa yasa shi ƙara rumtse ido sosai, wanda ya tabbata idan ba karaya bace to ya samu targaɗan ƙashi. _"Ya hayyu ya qayyum"_
Ita ce kalmar da yake ta nanatawa a fili har zuwa lokacin da ya fara samun sassaucin zafin ciwon. sannan ya ɗago da kansa ya jinginar jikin bango yana sauke numfashi a hankali a hankali.
kuma lokaci ɗaya hoton Sabina ya shiga haska masa acikin ƙwayar idonsa, maganganunta kuma na waccen ranar suma suka haska a kansa, ranar da ta zama ta ƙarshe da ya gargaɗeta akan karta ƙara zuwa inda yake, har yay mata rakiya zuwa titi ta hau mota.
A dawowarsa, mazauninsa inda yake rayuwa, wata sabuwar ƙaddarar da zai iya kiranta da mafi muni igiyarta ta zarge ƙafarsa, kuma bata sake shi ba har sai da ta kawo shi nan, cikin wannan cell ɗin da kwanaki ashirin da biyar kenan yana cikinsa, ba zaman daɗi ba, zama na wahala da uƙuba, zaman da a kullum yake cewa inama mutuwa tazo ta ɗauke shi.Sai dai a kullum abu guda zuciyarsa ke faɗa masa, ba zaka mutu yanzu ba, ba zaka mutu ba Alhussain har sai gaskiya tayi halinta, ba zaka mutu ba har sai ka fita daga wannan zargin. lokaci ɗaya yaji wani abu da bai san menene shi ba ya wuce ta maƙogoronsa, yayinda Sabina ta tsaya masa a ƙirji ta tokare wucewar komai ta wurin.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...