*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(19)*
Washe gari da safe bayan mun karya ina ɗaki muna waya da Farhana ina faɗa mata zanzo kano ba ƙaramin daɗi taji ba, Gwaggo ta shigo ta samu gefe ta zauna tana jiranmu gama wayar, kuma da alamun fuskarta tana so tai magana dani ne, Amma sam babu alamun zamu ƙare wayar, da ta gaji da jira tace. "yau naga ikon ubangiji, yo sai kice min Gwaggo tashi ki fita ba yanzu zan gama wayar nan ba". Ina jin haka nace da Farhana. "ga Gwaggo ku gaisa". Washe baki tayi kana ta ke faɗin,"ahh haka za ki ce min Farhana ce mutan kano". Farhana ta gaishe da Gwaggo ta amsa mata, Gwaggo tace,"Farhana ki gaisar min da Hajiyarki sosai da sosai, insha'Allah idan na shigo kano zanzo har gida mu gaisa, eh kifa gaishe ta don nasan halinki sarai kamar yadda nasan na ƙawarki ato". Ni dai karɓa nayi ina dariya Gwaggo tace nayi na gama Baba yana jirana. Jin haka yasa na katse kiran duk da ina son tambayar Farhana ya Yayana yake, kamar wadda na bata ajiyarsa, amma ban samu damar hakan ba, saboda Gwaggo ta kafa ta tsare. Ina fita na iske su Gwaggo da sauran matan gida duk a parlo ni ɗaya ne babu, gefe guda na samu inda Gwaggo ta ke bayan na gaisar dasu Baba da sauran Matan gida da Yaya Abba. Ko kallon inda Yaya Haidar yake banyi ba, Gwaggo ce kawai ta lura da haka. Gwaggo tace, "yauwa dama ba komi bane, Sabina ce zata je ganin dangin ta shi ne nace barin sanar daku, har tafiya ta tashi ace bamu sanar ba, ato idan damai sha'awar zuwa shima sai yaje yaga nasa dangin". Gwaggo tana rufe baki Umma tace, "ah ai kuwa ba za'a rasa masu zuwa ba, su Zainab ma zasu je dama suna son zuwa dama ce basu samu ba". Baba yace, "sunyi hutu ne?". ɗan sosa ƙeya Umma tayi kafin tace, "ai wai da naga Gwaggo ce tace idan damai sha'awar zuwa shisa na faɗa haka". Gwaggo tace, "ai sanin asali shisa kare yaci alli, yo ai nasan kwanan zancen, dama na faɗa ne kawai don naga hankalinku kuma sai gashi nagani. To ku babu ma mai zuwa ita da Abba kawai ya isa su tafi su lafiya insha'Allah, ato ni na gama magana kunga tafiyata". Tana rufe magana bata jira cewar Baba da kowa ba ta ja hannuna muka bar wurin. Baba yayi ƴar dariya yace, "ni zan fita babu mai magana?". Baba ya tambaya da buƙatar amsa. Shiru suka yi, alamu ya bashi babu mai magana suka yi mashi fatan alkhairi ya fita. Bayan komawar mu ɗaki kuwa Gwaggo ta shiga haɗa min kayana da duk wani abin buƙata ta kuma jaddada mani akan na riƙe azkar sosai kar nayi wasa da shi, ta kuma haɗa min magungunan da zan riƙa sha ina shafawa, duk da tasan bai yiwu lallai nayi amfani da shi ba. Na dubi Gwaggo nace, "naga Gwaggo sai haɗa kaya kike, kuma naga ba yau ne tafiyan ba sai gobe". "yo ke banda ke da abinki, ai saboda karki manta wani abin, nifa idan zanyi tafiya tun ya rage sati nake kimtsa komi nawa, saboda gudun mantuwa, bare kuma Sahibina Allah sarki, Allah ka jaddada Rahma a gare shi". da Amin na amsa mata bayan na samu wuri na zauna. Gwaggo ta ɗakko wancan ta ɗakko wannan duk tana yi min bayanin wanda zan bama idan Allah yayi tafiyan nawa gobe.*Ɗaya Ɓangaren.*
Kwance yake a makeken gadonsa, mai kyau da tsari, kayan alatu sun wadatu a ɗakin babu ƙarya, alaƙalami ba zai iya bayanin yadda ɗakin ya wadatu da tsaruwa ba sai ido in ya kalla. Sallama tayi fuskar ta ɗauke da murmushi. Ta samu gefe guda kan kujera a kusa da gadon ta zauna kana tace, "Bro barka da hutawa". ɗan juyo da fuskarsa yayi gareta kana ya motsa bakin shi tamkar baya son magana fuskar shi babu yabo babu fallasa yace, "Barka dai Sis, dafatan an samu biyan buƙata ko?". "umm an samu, amma sai an bani tukuici zan bayar don Mom haka tace". ɗan murmushi yayi kafin ya furta,"me kike buƙata ki faɗi min, duk da nasan kinfi ƙarfin komi a wuri na, but tell me um". "to shikenan, na yafe sai dai nayi fatan asha soyayya lafiya yasa kuma ita ne Aunty'nmu". Amin ya amsa da shi kafin yace, "duk kinsa ni ƙaguwa, kin gagara bani na gani". Ƴar ƙaramar takarda ta miƙa mashi, ya ɗakko wayan shi yayi dialing number, da ike yana Amfani da true caller a ta ke sunan ta ya bayyana, ba shiri wani ƙayatatcen murmushi ya samu muhalli a fuskarsa. "bari naje wurin Mom kafin nan ka gama". da to ya amsata sannan ta fice a ɗakin. Sau biyu yana kira bata ɗauka ba sai ana uku ya yi sa'a ta ɗaga tare da yin sallama, sallamar da tayi barazar ɗauke numfashinsa cancakas, da gaggawa tare da nasarar ubangiji ya samu ya dawo gareta ya amsata yana faɗin. "Ina fatan ban katse ma Beauty baccin da ta ke mai cike da farin cikin ganina a cikinsa ba". Jin kalmar Beauty yasa tuni na gano wanda ke magana, hakan yasa nace,"Barka da Safiya Sir, ina kwana, na tashi a bacci tun ɗazu, yasu Mom?". "Masha Allah, Mom tana lafiya. How was your nyt?". "Alhmdl Sir". Na faɗa ina jin wani yanayi na jin nauyi a tare da ni. wucewar wasu sakanni na katse shirun daya ratsa nace,"amma Sir where do you got my number?". Murmushi naji yayi, bai kuma ce komai ba. Na kuma cewa, "Sir ina tambayanka ne fa, answer me please". murya a ɗan murɗe yace,"Do you think I will let you go without paying me for what you stole from me. Abune fa mai muhimmanci kika sace min, so I have to find you wherever you are, even if it's not on the phone. Ko da kuwa zan murɗa keke nane naje har birnin sin". Gabana ne ya buga ras, naji kamar an karza min magogin kaushi, tuni idona ya ciko, muryana a raunane nace,"nifa wallah ban maka sata ba, kuma ma naga nace ka faɗi min ko nawa ne Allah zan biyaka, amma ka daina cewa nayi maka sata, har ga Allah bana so ake dangantani da wannan kalmar". ba tare da na bashi damar magana ba na karawa Gwaggo wayar a kunne ina faɗin,"Gwaggo ki sanar da shi ban taɓa sata ba, ya daina cewa na masa sata...". "shine muna malamin da yace kin masa sata?".Ta tambaye ni tana dafa katifa ta miƙe daga kwancen da ta ke. Kamin na bata amsa yace, "Gwaggo ina kwana". Naji ya faɗa cike da girmamawa. Gwaggo ta ƙura min ido, na ɗaga mata kaina alamar ehh, tayi gyaran murya sannan tace da shi,"Kai kuwa bawan Allah tsakani da Allah haka ake rayuwa, haka kawai saboda ɗaukar alhaki kace ɗiyar albarka tayi maka sata, to gaskiya ka sauya hali saboda wannan ba halin ƙwarai bane. Ni Ƴar jikalle tah ko tsinke bata taɓa sata ba, atoh sai kaje can ka nemi wanda yayi maka sata, idan ba haka ba hukuma ce zata raba ni da kai, ba zan lamunci ganin ka ɓatan sunan Jika ba, a hakan ma ƙazafin da kayi mata kaje kai da Allah, yo wannan ai kai fitinannen bawa ne". Daga inda Muhsin yake yay dariya mara sauti, yanzu ya gane Gwaggo Kakata ce ba mahaifiyata ba, ya buɗi baki zai magana Gwaggo ta tari numfashinsa da faɗin,"yo tsaya yanzu mene na kiranta a waya ma, ko wani sharrin zaka kuma ƙulla mata?". Nayi caraf nace, "Gwaggo haka fa yace ba zai taɓa barina ba duk inda na shiga, dole ne sai ya nemo ni ko da kuwa a keken guragunsa ne". tai wani zabura ta ƙara gyara zama kan tace,"au gurgu ne ma shi? Kai amma wannan anyi Fitinannan gurgu, ko da yake kunfi masu ƙafa iya shege, to ai sai ka fito sak a mutum kace mata kana barar na abinci ko na magani, sai a taimaka maka, amma ka wani fa-ke da tayi maka sata saboda rashin tsoron Allah. To na riga na gama gano ka taimako ne kake buƙata, sai kazo har gida ka roƙi Ubanta ya taimaka maka, ka daina bibiyar min ita da baƙin sharri, idan kuma ka ƙara cewa tai maka sata zanyi adu'ar kekenka ya wuntsula da kai a tsakiyar ruwa". Naji yay ƙaramar dariya, farinciki a tattare da shi yace, "Hajiya Gwaggo ai dama ni nafi so ta faɗa min inda gidan nasu yake, yanda idan iyayena ma suka zo Baba zaifi taimaka min". tana gutsurar goro tace, "aiko dai Auwalu zai taimaka maka sosai, kazo da kai da iyayen naka insha'Allahu duk wani kuka da kuka zo da shi zai share muku hawaye. Gidan ba wani wuya gare shi ba ai da kunzo...". Tunawa nayi da abinda yace min a wancan rana, Nai saurin saka hannu na rufe mata baki, duk na ruɗe nace,"Gwaggo karki faɗa masa inda gidan nan yake, wallah haka yace indai yazo sai ya faɗawa Baba na masa sata kuma ina murguɗawa manya baki". "iye". Ta faɗa tana jijjiga kai tare da cewa,"yo ai ce min za kiyi me haɗa husumiya ne shi kamar waccan shirgegiyar matar uban naki. To ɗan gurgu kana jina ba, laqad ja'akum baƙin sharrinka ya koma kanka. Kinga Sabina kashe min wannan wayar kar raina ya tugunzuma ya ɓaci nayi tattaki naje har inda yake". Na sauke mata wayar daga kunnenta ina dafe ƙirjina dake bugawa, ina jinsa kamin na kashe wayan yana roƙon Gwaggo don Allah ta masa kwatance, ni kuwa na kashe ina hararan wayar. Na lumshe ido na kwantar da kaina bisa pillow ina kallon sama, ina jin wayata na ringing naƙi ɗagawa, saboda nasan shine, sai dana ji ƙarar shigowan text tukunna na miƙa hannuna na ɗauka, na buɗe ina karantawa. _Please Beauty help me pick my call, na rantse za kisa naje na yiwa Mom kukan dana jima ban mata ba. My eyes are desperate to see your beautifull face, ba zan iya juriyan har sai an koma school kamin na kuma ganinki ba, i can't bear it anymore, dole sai kin biyani satar da kika mani zan ƙyaleki._ Ina gama karantawa na taɓe baki, na kuma murguɗawa saƙon nasa baki shima. Na jefar da wayar gefe na mayar da murfin idona na rufe, ina jin Gwaggo na min magana nai mata shiru. Gaba ɗaya tunanina da ɗokina ya tafi akan naje kano naga Yayana, idanuwana can see nothing fa-ce fuskarsa, haka zalika my ears can hear nothing but the sound of his golden voice wanda yake iri guda dana Proff, da ace zanje Kano na rasa Yayana tabbas zan dawo na kama Proff nace shine, saboda ban manta da wani kallo da Proff yayi min ba a wancan rana, sak kallon da Yayana yay min a ranar da nake bashi abinci a baki. Naja doguwar ajiyar zuciya na sauke, na miƙa hannu zan jawo pillow na rungume naji an ɗala min duka a bayan hannu, a zabure na miƙe naga Gwaggo na wurgan harara, na bo-ne fuska ina turo baki gaba sai fama ƙifta idanu nake. Yau rana ta farko da tace da ni, "mutum sai shegen turo baki gaba kamar shantu...in har ba ki daina wannan mugun abun da kowa ke ƙorafi akansa ba wataran sai jaɓa tayi miki kiss". na tuntsire da dariya sosai. nan ta kuma hau bambamin bata son wannan ƴr iskar dariya, Allah kuma ya rabani da sababinta a sanda ta jiyo motsi a parlo, ta fita da sauri tana faɗin,"ga Aliyu can ya shigo yi min ta'adi da sanyin asuba, yo ta'adi ai sata ne. wannan yaro dai da gani Unguwar Zoma bata gasa shi da kyau ba".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...