*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(23)*
cikin ɗagin murya yace da ni. "ba za ki bani ba?". nima na cukule ina kauda fuska nace, "ehh ai kaima ga taka can kaje ka ɗauka ka ƙarasa sha, idan kuma ka ƙoshi da itane sai ka ɗauka wani sabo a kwali ai akwai da yawa". Na faɗi hakan ina fito da ita zan kuma kaiwa bakina, cikin amon muryarsa nan mai dadi ya dakatar dani. "don girman Allah karda kiyi gangancin sha, wallahi Allah bata dace dake ba, babu abinda takeyi fa ce ƙara damuwa amma bata maganin komai...". na saki wani yalwataccen murmushi da sautinsa ya amsa acikin ɗakin. sai ya ɗago yana kallona da kallo irin na mamaki. na ɗaga masa gira nace,"Yayana wai ni zaka ma wayo ko, saboda karna sha zaka ce min haka, to naƙi wayon sai nasha nima naji irin daɗin da kake ji acikinta har yasa kake min rowa". Kasaƙe yay yana dubana yayinda yake jin wani abu ga me dani na ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa. sai ya kulle idonsa ya wani fizgi numfashi. "na rantse ba wayo ne nake miki ba. Da gaske nake miki bata maganin komai kuma wallahi bata dace...". Bai ƙarasa ba nayi saurin sanya yatsana a leɓensa alaman yay shiru. "Yayana". Na kira sunansa kiran daya ji har ƙwaƙwalwarsa, ya zuba min ido kamar yanda na zuba masa idanuna da suka taru da ruwa. "Yayana idan har wannan abar bata dace da ni ba to na rantse da Allah kaima bata dace da kai ba, saboda mutumin kirki baya shanta, mutumin da yake jin tsoron Allah baya shanta. idan har kana son lafiyarka ba zaka shata ba, idan har kana so damuwarka ta yaye ba zaka sha ba sai dai ka ɗauka maganin damuwa kankat Al-qur'ani me girma ka karanta, wannan shine hanyar da ma'aiki ya koyar damu, ba wai mu ɗauka abinda mun san zai cutar damu ba don magance damuwarmu, ita ɗin fa haramun ce na faɗa maka haramunce mene yasa ba zaka haƙura da ita ba?". Bayan na numfasa naci gaba da cewa,"haƙiƙa ba zan hanaka damuwa ba amma ba zan bar damuwa ta dameka ba Yayana, amma ina so ka fahimci cewar ƙaddararka ce a haka domin tuni Allah ya rubuta hakan zai faru da kai, dole ne kayi imani da ƙaddararka muddin kana son cika mumini na ƙwarai. A baya na faɗa maka bayan imani da ƙaddara akwai haƙuri, Yayana kayi haƙuri da yanda ka sami rayuwa, Allah da kansa yake cewa ana cikawa masu haƙuri ladansu ba tare da ƙididdiga ba. Yayana shaye-shaye babban zunubi ne mai girma ya kamata ka nisance shi, musamman abinda zai kawar da hankali ko kuma yasa maye, Allah ya mana umarnin mu guji kayan maye zamu rabauta, da kansa acikin littafinsa mai girma ya ambaci kayan maye da aikin shaiɗan. Ka sani lallai fa aikata saɓo yana hana arziƙi ya kuma gusar da ni'ima da albarkar dukiya. Don girman Allah Yayana kayi haƙuri da ƙaddarar da ta sameka, ka bar shan abinda yake haramun". Na faɗa hawaye na sakko min. Ganin yanda nake hawaye gaba ɗaya sai yaji ya ƙara shiga damuwa, ya rumtse idonsa ya buɗe sau uku a lokaci guda. "don Allah ki bar kuka bana son zubar hawayenki". Muryana na rawa nace,"wallahi Yayana wannan hawayen ba zasu taɓa daina zuba ba har sai randa ka rabu da wannan haramtacciyar abar. Na rantse maka idan har zaka dinga shanta to ko da yaushe hawayena zai dinƙa zuba a ƙasa ne. ka faɗa min a yanzu mene ka nema ka rasa da har ba zaka iya rabuwa da ita ba? Ka faɗa min ko mene shi na maka alƙawarin samar maka shi ko don ka bar cutar da kanka in har baifi ƙarfina ba. ko kuma Baba ya gaza yi maka ne?, Adu'a fa itace maganin damuwarka ba wannan muguwar abar ba". na numfasa na goge hawayena sannan nace," *ALLAHUMMA INNI ABDUKA, IBN ABDUKA, WABNI AMATIKA, NASIYATI BIYADIKA, MADIN FIHA HUKMUKA, ADLUN FIHA ƘADA'UK. AS'ALUKA BI KULLI MIN HUWA LAKA, SAMMAITA BIHI NAFSAK, AU ALLAMTAHU AHDAN MIN KAL'IK, AU ANZALTAHU FI KITABIK, AU ISTA'ASARTA BIHI FIL ILMI GAIBI INDAK, AN TAJA'ALIL QUR'ANA AZIMA RABI'A ƘULUBINA, WA NURA SUDURINA, WAJALA'A AHZANINA, WA ZAHABA HUMIMINA WARMUMINA*, wannan adu'ar itace Annabi ya koyar damu, kuma yace in har ka karanta Allah zai tafiyar maka da damuwarka ya kuma musanya maka da farinciki a maimakon damuwar. Don Allah Yayana kafi ƙarfin zuciyarka ta hanyar hanata abinda take so in har na saɓon Allah ne". abunda nake gani a ƙwayar idonsa dabanne, wani abu dake haskawa yana motsawa tare da zuciyata. motsin yatsunsa kawai nake iya gani a wannan lokacin, kuma kamin ƙifatawar idanuwana sai ganinsa nai ajikina, ya rungumeta tsam, kuma duk jarumtar namiji, duk yanda yaso ya hana wannan ruwan hawayen zuba ya kasa, sai kawai ya fashe da kuka yana daɗa matseni a sanda yake cewa. "haƙiƙa ke ɗin kina da baiwar da ba ki san kina da ita ba, iliminki da kyawun halinki sun dace dake, ki godema Allah da wannan baiwar da yayi miki. na rantse miki daga yau na barta, na rantse ba zan kuma sha ba tunda ba kya so. na barta har abada. Nima ban san lokacin da nake sha ba, baƙincikin ta yanda aka sa me ni shi yake jefani cikin wannan hali, iyayena basu kyauta min ba, Amma wallahi nayi miki alƙawarin daga yau ba za ki kuma ganina da ita ba har mutuwa, kin riga kin gama yi min gatan da duk abinda kika ce a gareni zanbi umarninsa". Jikina na rawa na raba shi da jikina. "Yayana ba don ni nake so ka daina ba, nafi so ka daina don Allah". Murmushin daya ƙawata fuskarsa ya sa ki yace, "zan daina don Allah kuma zan daina don ke". Ya faɗi hakan yana bani hanky na goge hawayena. Ina kallo ya tattara sigarin ya zuba a baƙar leda, yana cewa da ni,"kin gani ma na kwashe su duka, Yanzu zanje na zubar a shara". Ni dai tsaye na miƙe ina kallonsa, yellow t-shirt da black jeans ɗin daya sa sun masa matuƙar kyau, ya juyowa muka haɗa ido nayi saurin rufe idona. Dab dani naji ya tsaya, yasa hannu yana shafa kumatuna yace, "ƙanwar Yayanta bayan wannan akwai wani abun da kike so na daina?". Na buɗe lumsassun idanuna ina kallonsa, ya ɗaga gira yana waro min ido yace, "ehen yi magana mana". ina murmushi na buɗe masa tafin hannuna, ya kalla ya kalleni, na ɗaga masa gira kaɗan ina cewa, "duk dana yarda da kai amma ina so ka mani alƙawari, saboda idan harna kuma ka maka kana shan sigari wallahi nima sai na sha". Ya ɗora nasa tafin hannun kan nawa yana cewa, "na maki alƙawari". Na sauke numfashi nace,"to ka bari ka fara cin abinci tukunna kamin ka fita yarda wancan abun. abincin yana parlo na ajiye maka, Gwaggo tace idan ka gama tana nemanka". Fita nayi na barsa yana zuba abinci, zan shiga side ɗinmu Yaya Haidar ya kirani. Na ƙarasa wurinsa nace gani, fuskarsa a murtuke yace,"me ya kai ki side ɗin wancan ɗan tsintuwar?". Na ɗago da nuna rashin fahimtar maganar tasa. Cikin ɗagin murya ya kuma ce min, "ba ina miki magana bane". Ya miƙo hannu zai buge min baki yana cewa, "za ki maida bakin ko saina fasa shi". "to aini ban gane wa kake nufi ba". "ni za ki rainawa wayo. Ba ki san wanda nake nufi bane, tunda yazo gidan nan na fahimci kanki na rawa, kina wani shishshige masa. Shi sarki ne da ba zai iya zuwa ya ɗauka abincin da kansa ba kamar yanda mukeyi? sai kin wani ɗibi jiki kin kai masa". Na ɓata rai nace, "to ai naga shima Yayana ne tunda ya zama ɗan gidan nan". Bai kuma cewa da ni komai ba naji yaja dogon tsaki ya bar wurin a fusace, nabi bayansa da harara.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...