*(14)*
*Safiyar Litinin*
kasancewar yau monday tushen aiki, kuma yau ɗin da izinin Allah zan fara ɗaukan lectures, dan haka tunda na kammala azkhar ɗina ban koma bacci ba shiri kawai na fara yi, abunka da farin shiga zumuɗi duk ya cika ni, Sabinan Gwaggo a jami'a.Kwalliya nayi sosai wanda ta ƙarɓe ni matuƙa musamman da na ɗora da medical glass ɗina, dama gani ƴar son kwalliya da ado, tabbas duk wanda ya kalle ni dole ya so kuma ganina. Tunda na fito parlo na kalla yanayinsa nasan Gwaggo bata tashi ba, saboda indai ta farka ta fito zata sa karatun ƙur'ani ta kuma saki turare.
Jakata da mayafina na aje kan kujera na wuce kitchen don samarwa kaina abinda zanci, dai-dai da zan shiga nayi karo da Yaya Haidar zai fito, da sauri naja baya na yi gefe a tsorace, Allah ya taimake ni ban tankwaɓar masa da kofin shayin da ke hannunsa ba.Na murguɗa baki gefe don banda niyyar gaida shi, sai naji kamar na koma idan ya fita sai na dawo, wata zuciyar ta ce min kawai na tsaya na ƙara ba shi hanyar wucewa, ina kallonsa ya wani haɗe rai yana jifana da harara, bai yi niyyar saurarena ba amma saboda neman magana yaja tsaki yana kallon kayan jikinsa kamar nayi masa ɓari a jiki.
Ya ɗago ya kalle ni yana kuma hararata, ya ƙara jan tsaki ya ce,"Ba kya gani ne da ba za ki iya lura da tahowar mutane ba".Na kalle shi kaɗan na ce,"ai ban san da tahowan na ka bane, kuma ina sauri ne".
Tsaye yayi yana kallona ta ƙasan ido,"stupid girl". Ya faɗa yana ƙare min kallo still ta ƙasan ido, ni dai zumɓuro baki na ke ina alla-alla ya wuce, wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗauka yana waya, sai da ya gama wayar kana ya bar wajen, na bi bayansa da murguɗa baki.
Da na shiga kitchen ɗin ma rasa me zan dafa nayi, na duba agogon da ke saƙale a wurin, lokaci ƙara tafiya yake kuma yau tara ne zamu shiga lectures, ga time har takwas tayi, na doki ƙafa a ƙasa, ko me fa zan dafa sai yaja min lokaci tunda ni bacin Indomie na ke ba, ko tea ɗin zan dafa it will take time too, tunawa nayi da Yaya Haidar zai fita da tea Kettle a hannunsa, da sauri na suri cup da spoon, na zuba madara da bounvita da nescape na fita, ina zuwa kuwa na sameshi kan kujera yana kurɓan shayinsa, nanje gabansa na tsaya ina sosa gefen kunnena.
Ya saci kallona ya ɗauke kai kamar bai ganni ba, na turo baki gaba na duƙa gaban table zan zuba tea a tsawace ya ce da ni,"kee".
Na ɗago ina marairaice fuska na ce, "Please Yaya Haidar, Makaranta zan tafi and idan na ce i will wait to cook something i will be late. tea ɗin da yawa, barinsa ma za'a yi tunda Gwaggo ba ta sha".
Na faɗa ina ɗaga kettle ɗin na jijjiga naji yawansa. "wallah idan ba ki aje min kayana ba sai na zabge ki da mari, ke kika dafa min da za ki zo ki ce na ba ki, mara kunya kawai ana magana kina turowa mutane baki, me zai hana ki jira Kakar taki tazo ta dafa miki, ko kuma ni bawanki ne da zan dafa abu ki ci".
Ya faɗa yana ƙara tamke fuska. Na aje ina ƙunƙuni ina cewa,"to amma ai dai a kitchen ɗin Gwaggo tah aka dafa".
Ashe ya jiyo ni, hakan yasa ya ce,"an dafa a kitchen ɗin na ta kuma ba za'a bayar ba, bar min nan wuri ko kuma na yi ball da ke".
Na miƙe na bar masa wurin, cikin raina ina faɗin mutum ba abinda ya iya sai shegen ci, tunda ya zo gidan nan kamin kowa ya tashi zaka kalla ya tashi ya dafa abincinsa, kuma aikinsa kenan shan tea ko da rana ko da dare, sai kace wani balarabe. Kitchen na wuce na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na sauke na dama curstad, na fito na wuce dining nayi zamana ina shan kayana, Gwaggo ta fito ta sameni, tana kallona ta fahimci akwai abunda akai min. dan haka ta dakata daga gyaran ɗaurin zani ta ce min,"ke kuma me aka maki kike faman ɓata rai da sanyin safiyar nan? duk da ke dama uwar miskilanci ce, ko ba'a taɓa ki ba iskokanki zuwa ɗaukar fansa su ke".
Na aje cup ɗin na ture shi daga gabana, daga tashinta zata hauni da faɗan da ba ya mata wahala. Taja ƙaramin tsaki tayi juyawarta zata bar wurin tana cewa,"ke dai kika sa ni da halin nurƙufancinki da baida kyau, tashi na kenan ban bawa cikina ba, ba za ki sani magana ba".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...