Harufan bakina na fita a kakkarye na ce da shi,"Don Allah Yayana".
kalaman bakin suka fito acikin siga ta roƙo ina mai ƙare damƙe hannunsa. Cak ya tsaya ya dawo ya zauna, yana ta so ya ƙwace hannunsa daga ruƙon da na masa amma na hana, kansa na kallon ƙasa yay shiru bai magana ba, damuwa na ƙara bijiro min na datsi shirun da cewan,"Yaya zuciyata matsewa takeyi, dan Allah ka faɗa min wannan ciwon fa? Kuma me kake yi anan?".
Ya ɗago ya tsareni da ido, sannan ya buɗi baki ya ce,"ni me yasa ba za ki amsa min nawa ba?".
"to ai ni na fara tambayanka".
Ya ce, "idan har aka ɗora duka tambayoyin a bisa mizanin ma'auni, nawa ita tafi muhimmanci da cancantar amsawa sama da taki, duk da cewan tambayanki yafi yawa amma girman tawa ta rinjayi taki. Na rantse miki idan har ba ki bani amsar dalilin da yasa kika fito babu niƙab ba, zan tashi na tafi, tafiyar da har abada ba za ki kuma ganina ba".
Ban san lokacin da na haɗa yatsuna da nashi wuri ɗaya ba ina wasa da su, na fara magana ina cewa,"kamin mu bar gari na zo har sau huɗu bana samunka, har a ƙarshe na bar maka saƙo wanda idan ka gani zaka neme ni. ba haka kawai na daina zuwa inda kake ba, mun koma Abuja da zama ne sai yau na samu daman zuwa, kuma na bar niƙab ɗina a can shisa, ita kuma Hajiya bata da shi bare na amsa na saka. Yayana tunda na tafi kowanne rana a cikin tunanin halin da kake na ke, haka zalika a cikin kowanne daƙiƙa na bugawan agogo jiran tsammanin kiran wayarka nake amma shiru. Yayana ina ka tafi a wancan lokaci? Me yasa na dawo na sameka a wannan halin?".
Idonsa na kallon gefe guda ya ce,"abubuwan da yawa...na farko an yiwa wata yarinya fyaɗe har ta mutu shine aka ɗora alhakin hakan akaina, na jima kamin gaskiya ta bayyana, ashe Baban Yarinyar yana harkar ƙwayoyi sai suka samu matsala da yaransa shine suka ɗau fansar abunda yay musu akan yarinyar. bayan na fito da ƴan kwanaki aka sace yara anan anguwar, mutane suka ɗora min laifin da banji ba ban gani ba akan cewan ni na sace su, bisa wannan zargin nasu yasa ƴan sanda suka kamani, nasha wuya sosai a wurinsu har naji inama na mutu na bar wannan rayuwar, a ranar da zamu wuce kotu ranar aka ga yaran, sati ɗaya kenan da aka sake ni, na dawo duk inda naje na zauna domin samun mafaka sai an kore ni, babu wanda ya tsauyawa halin buƙatar taimakon da na ke ciki sai limamin wannan masallacin, shine ya kaini chemist aka bani kulawa, ƙasan bishiyar nan yanzu shine mafakata".
Tunda ya fara maganar na ke hawaye sosai, har ta kai ga na daina sauraron abinda yake cewa, hannu yasa ya dafa goshina ya ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye. Ina kallo ya yagi ƙasan rigarsa yay min tsumman goge hawayena "kina so a kuma kamani ne?".
Ya faɗa a yayin da yake gogen gefen idona wanda nake tunanin kwalli ne ya zazzago. Na shiga girgiza masa kai da sauri alamar a'a.
"to ki bar kuka, kar mutane su ganki ace nayi miki wani abun, a ƙara kamani ayi min ɗaurin rai da rai".
Babu shiri na tsayar da kukana, ina faɗin,"Wallahi ba zan taɓa yafewa wanda yay maka wannan sharrin ba, wallahi ba zan taɓa yafewa wanda ya wahalar da kai ba, Allah ya bi maka hakkinka. Me yasa daka dawo baka kirani ba?".
"ta ina zan kira ki?".
"na fa aje maka letter da zan tafi, na san kuma har zuwa lokacin yana nan tunda babu wanda ke shiga sai kai, kuma nayi yanda ko da iska ba zai iya figansa ba bare ruwa ya lalata shi".
Yay wani murmushi mai ciwo, damuwa na daɗa bayyana a tare da shi.
"tunda na sanyo ƙafata cikin anguwar nan ake min ruwan duwatsu akan sai na koma, da ƙyar wasu bayin Allah suka taimake ni. Ba daban ina da yaƙinin idanuwana zasu ƙara ganinki ba, da ba ki zo kin kuma samuna anan ba".
Hannunsa da ke cikin nawa ya daɗa matsewa ya damƙe, idanunsa a runtse ya shiga juyi da kansa yana faɗin. "Tunda suka kamani, tunda suka sanya ƙafafuna a sasari, tunda suka jefa ni a ɗakin duhu, a kowanne bugun azabtarwar su, a kowanne nau'in horo mai wahala, a duk wani bugu na zuciyata ke ce a raina, bana jin daɗin duniyar, har sai na rufe idona na hasko ki aciki sannan na ke samun sassauci. Don Allah ki ce min kina da alaƙa da ni, ki ce ke ɗin jinina ce, ki ce kin shigo rayuwata ne domin ki canja duniyata".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...