17

72 9 0
                                    

*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(17)*
a lokaci guda furucinsa ya daki tsakiyar kaina. Na zaro ido a tsorace ina dubansa nace,"na shiga ukuna, ni ɗin na maka sata?". Ya ɗaga min gira ɗaya alaman ehh, a ruɗe na shiga ce masa,"wallahi ko Gwaggona tasan bana sata, Kuma ban taɓa yunƙurin yi ba. kuma don Allah karka je kace ma Baba na maka sata, ba zai tsaya jin komai ba zai ɗauka tsatstsauran mataki akaina. Ni dai nasan ban maka sata ba amma ka faɗa min ko mene indai kuɗin account ɗina ya kai zan biyaka ta ke anan". Ina faɗa duk na rikirkice, tsorona Allah tsorona Baba ya kuma korata daga gida. a wannan duniyar tashin hankain da Proff ya jefani naji maganarsa na shiga kunnuwana da cewa,"kuɗi ko kuma wata kadara ba zata iya biyana abinda kika satar min ba, dole Baba da kike tsoro shi zansa Daddy nah yaje ya sama ya faɗa masa, ta yanda Baba da Daddy nah zasu yi saurin yanke hukunci dai-dai da buƙatata". kawai saina fashe da ina faɗin, "wallahi tunda uwata ta haifo ni duniyar nan ban taɓa yiwa kowa sata ba. ko wancan karanma sharri Umma tayi min. dan Gwaggo nah ta bani tarbiya mai kyau wanda ko kallon abinda ba nawa ba bana iya tsayawa yi". Sosai nake kukan har sai dana kifa kaina a gwiwata, wannan wacce iriyar ƙaddara ce. Naji ya cika bakinsa da iska ya furzar, a cikin siga ta lallashi yake ce min, "ohhh Beauty please stop crying mana, am just kidding you ba zan faɗawa Baba satar da kika mani ba". na ɗago idona masu ruwan hawaye nace,"au da gaske ne ma na maka satar? To mene na satar maka?". y gyaɗa kansa sau uku kamin nan yace,"ofcourse kin sace min abu mai muhimmanci a tare da ni, amma i promise you i will not tell your Dad for now, but for sure zan faɗawa Momy nah, what ever she decide akai then...". Bai ƙarasa ba ya kanne min ido guda yana cije leɓensa na ƙasa, yana abu kamar Yaya Haidar. Ni kam na shiga uku, wannan rana ta yau bata zo mani a sa'a ba, na kuma fashewa da kuka, naji yana cewa, "shikenan idan kina so na bar maganar to ki bani haƙuri". Ai da sauri na ɗago nace, "kayi haƙuri". "haka ake bada haƙuri?". Na karayar da kai, na kama kunnuwana nayi exactly yanda nake bama Yaya Abba haƙuri idan na masa laifi, "Don girman Allah kayi haƙuri". Hasken flash yasa na ɗago ido ina kallonsa, ƙyasss naji ƙarar ɗaukar hoto, zanyi magana kawai na ƙyaleshi, ba buƙatata kenan ba. "Sabina Auwal right?". Ya jefo min tambaya. na ɗaga masa kaii "ehhh". "nice name Beauty". Na murguɗa masa baki, ya tari numfashina da cewa, "yauwa and i will also tell Baba kina murguɗawa manya baki". Na ɗago zan bashi haƙuri na tuna abinda Gwaggo tace min duk sanda wani yace ina murguɗa masa baki. Na turo bakina gaba nace, "ai dai ko Gwaggo tasan ina yi, kuma ma ai a wurinta na koya. Saboda haka ko an kai ƙarata wurin Baba ba abinda zaice, "Ƙaramar dariya naga yayi, ina marairaice fuska na haɗa hannuna nace, "don Allah kai wane?". a karo na babu adadi ya janyo leɓensa na ƙasa ya cija sannan ya shafo sumar kansa yace, "sunana Muhsin Muhammad Na kowa...". Bai ƙarasa abinda zaice ba na wurga masa tambayan, "a kano kake?". Ya kaɗa min kai, "nop, ni banma taɓa zuwa Kano ba. Mahaifina balaraben sudan ne, also my Mother she's shuwa arab, mu 6 duk an haifemu a misra, wata harƙallar aiki ta kawo Daddy nah nan Abuja, ataƙaice bamu haura 4years ba anan, like you see me ina da asali, kuɗi, gata da duk wani abu na jin daɗin rayuwa, sai dai banda lafiyan ƙafa, as soon kuma zamu koma can ƙasarmu da zaran Daddy ya kammala abinda yake. So kema sai ki shirya becouse we are going along with you, acan ne za ki amsa hukuncin satar da kika mani". Zan buɗi baki nayi magana Malama Muhsina ta shigo. "Brother is time for the meeting". Na kalla ya duba agogonsa yace,"oh shet". Sai kuma ya kalle ni ya kalleta yace, "Sister zo ki tayani lallashin Beauty tun ɗazun ta ke kuka taƙi yin shiru, kuma kin san na tsani kuka bare nata ma da babu daɗin ji kamar kukan shanuwa". Ya faɗi hakan yana wani toshe kunne, Zumbur na miƙe tsaye na ƙwace hannuna daga nasa, don cin mutunci kukana ne mai kama dana cow, ina tura baki na raɓa Malama na ɗauka jakata dake kan kujera nayi ƙofa. Sai dai a rufe take, na juyo na kallesa naga yanda yake dariya ƙasa-ƙasa, na kawar da kaina cike da jin haushinsa. Malama Muhsina ma tayi siririyar dariya ganin yanda na cukule tace, "Soryy Beauty ki rabu da Brother nah, idan kika biye masa zai ta sanyaki kuka ne. Bari nazo na buɗe maki". Ina kallo ta kamashi sosai kana ta ɗora shi kan wheelchair nasa, da alama dai ƙafafunsa basa aiki kwata-kwata, mutum ba isashshen lafiya sai ɗan banzan surutu da neman magana". tana buɗe ƙofa nayi ficewana raina duk a dagule, gefe ɗaya kuma ina saƙa abubuwa da dama a raina ina warwarewa, a wannan lokacin kowaye ya ganni yasan kwai abinda ke ƙasan raina saboda yanda nake zabga ƙwafa. ina kan hanya Yaya Abba ya kirani, na ɗaga wayan nace masa gani nan zuwa, Allah sarki bawan Allah ashe har yanzu yana jirana. Intisar ma ashe tun ɗazun tana waje zaman jirana, tana hangoni ta taso da sauri tana aika min tambayan me ya faru, ni dai shiru na mata ban saurareta ba nayi tafiyata ina sha re hawaye. ina zuwa mota na buɗe na shiga, da shigana na ƙara fashewa da kuka, tambayar duniya Yaya Abba yace me aka mani shima na masa shiru, gaba ɗaya ba komai ke damun zuciyata ba sai kewan Yayana, tausayinsa na kuma ratsa ni, ganin wannan mai kama da shi ya matuƙar ƙara tada min da kewansa, ya zama dole naje naga halin da yake ciki, bazan dawo ba har sai idan da shi ne, Allah yay mana wannan arziƙin da ba zan taɓa barinsa a wahala ba. dan Na gama gane Proff ba Yayana bane shi ya fiya surutun wofi, Yayana kuwa magana ma wahala ta ke masa. a ƙufule Yaya Abba yace, "ke ban san iskancin banza fa. Ina miki magana kin min shiru, exams ɗin ne tayi wahala?". Kai kawai na girgiza masa, sai yaja tsaki ba tare daya ƙara ce min komai ba. ganin yanda ransa ya ɓaci yasa nace,"Yaya Abba dama ana halittar mutane iri guda ko da ba identical twins bane?". Ko kallo na bai ba, sai guntun tsaki daya kuma ja, bai ƙara saurarena ba har muka isko gida. Ina shiga parlo na faɗa jikin Gwaggo dake zaune, ko ta kaina bata bi ba sai taɓe baki da tayi, ganin dai kukan nawa bana ƙarewa bane tace. "ke wai Ubanki Auwalu aka yi miki da za ki zo ki sani a gaba kina faman kuka, bayan kin san ba abinda ke ɗagan hankali a duniyar nan sama da kukanki, za ki faɗan mene ko kuwa?". na mata shiru ina ƙara ƙanƙameta, a gaskiya ina bala'in son ganin Yayana, dan a yanzu jin zuciyata nake na wani matsewa sa zafi. Ta tureni da ƙarfi tana cewa, "je can ki ƙarata da halinki ke ɗaya, idan kika ƙarar da hawayen kya rasa na zuwa ɗakin miji ace ba ki da kunya, ke baza'a taɓa tambayanki mene ke damunki ba ki faɗawa mutane ba a lokacin, sai kin gama iskance-iskancenki tukunna. to Wallah ki ka kuskura kishiya ta gane ma ruwan hawayenki gasa ki zata dinƙa yi". Sai a sannan ne nayi shiru, nace mata, "Gwaggo tunda munyi hutu yau don Allah ina so naje naga Hajiya da Mami da su Uncle Nasir". Ina nufin dangin mahaifiyata. Taja tsaki tace, "amma ke kuwa kina da abin haushi, dama abinda kike wa kukan kenan?". "a'a bashi bane. Wani Malaminmu ne yace na masa sata, har da kirani ofishinsa ya ƙara min wulaƙanci, shine nasa kuka sai yace wai Kukana kamar kukan Shanuwa, ita kuma ɗayar Malamar tamu tace min daƙiƙiya". Gwaggo tai wani zabarin gyara zane tana furzar da goron bakinta tace,"shi Malamin naku? Yace kin masa sata kuma kukanki kamar na shanuwa?". na ɗaga mata kai alamar tabbatarwa. ta jijjiga kai da kyau sannan tace,"To sata ta ƙare a ahalinsu, kuka kuma nasa ne ke kama dana tumaki. Ita kuma Malamar itace babbar daƙiƙiya da ta kasa fahimtarki. Kuma suje da halinsa na rashin kyautawa Allah zai saka miki, yanzu kije ki wanke fuskarki kizo kici abinci, na san babu abinda kika ci ki ka fice karatun da ba lada ba zunubi". na goge hawayena ina tambayanta cewa,"to Gwaggo zanje ɗin?". "za kije mana, ba kunyi hutu ba?". "ehh munyi har na wata guda ma". "to kinga kuwa kina da lokacinma da za ki je ki zazzaga musu. Ki bari idan Karima tazo sai ku wuce tare idan zata koma". Na miƙe ina cije leɓe nai ɗakina, gado na faɗa ina jin farinciki da nishaɗi, zanje naga Yayana, kuma mu taho tare da shi don bazan kuma barinsa acan ba, dole ne ma ya biyoni. Na rugume pillow inata murmushi ni ɗaya, dana rufe idona babu hoton dake haska min sai nasa, zumuɗi duk ya hanani sukuni, na ɗauka waya na kira Inna Karima na tambayeta yaushe zasu tace sai nan da sati biyu, ina jin haka ban san lokacin dana gilla mata ƙaryar ai Gwaggo bata da lafiya ba, aiko hankalinta a tashe tace min suna kan hanyar zuwa gobe ko jibi. Na kashe wayar ina dariya sai kuma na fara Allah na tuba Allah ka ƙarawa Gwaggo tah lafiya, ina haka ta shigo, hannunta ɗauke da kwanon abinci, yanayin da ta riske ni yasa tace, "ke lafiya?". "lafiya lau Gwaggo". Ta dire min abincin saman table tana faɗin, "da dai sauƙi kam, Allah ya bada lafiya inda rabon samunta". Ta juya za ta fice na dakatar da ita da tambayata. "Gwaggo kin taɓa ganin Halitta ɗaya a mutum biyu?". ta wani juyo a sukwane tana ambaton sunana, jin na amsa yasa ta cewa,"ohh ke ɗince dai". sai na ɓata fuska na turo baki gaba nace,"wai Gwaggo ba zaki bar ce min mai aljanu ba". tana gyara ɗaurin zanen da a ko yaushe nake takaicinsa tace,"to ai tambayar taki ce Sabina ta a bincika ce". "to ni dai ki bani ansata". "ansar me zan baki Sabinan Gwaggo?". na ƙara jefa mata tambayar, a wannan karon daya kasance tana fuskantata ne sai kawai ta bini da ido tana kallona da kyau cike da nazari, sai kuma tasa kai tayi hanyar fita tana faɗin,"to Allah yasa ba gamo kika yi ba...ni dai Rakiya Allah kayi min maganin abubuwan da suke neman fin ƙarfina".

*Please Vote, Comment and Share.*

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now