Tsaye na ke gaban mirrow ina drying gashina, wayana maƙale a kafaɗana muna waya da Farhana, har yau bata bar fushi da ni ba akan zuwan da nayi naje na dawo banje gidansu ba, bayan nace mata a gidansu zan sauka. ina dariyar masifar da take aikin yi na ke bata haƙuri ina cewa ita dai ta cika mita, na ce mata inan zuwa ai, taja tsaki ta kashe wayan.
Ban kai ga kammalawa ba wayana ya kuma ƙara, na miƙa hannu na ɗauka, sunan Proff na gani a jikin screen na yawo ta hanyar vedio calling, na cuno baki haɗe da yin ƙaramin tsaki na ajiye, na rasa me yasa kwana biyu yake takura min da kira, shima kiran dole sai ya ce vedio call, idan ban ɗaga ba kuma ya addabeni da message, har sai na fusata na ɗaga zan masa tsiwa sai karsashin muryarsa ya hanani aiwatar da komai, ta hakan zargina akan Yayana ya ƙara yawaita, na kuma ɗora ayar tambaya akansa akan abinda zuciyata ke saƙa min a game da shi.
Ina ta ƙunƙuni a zuciyata kiran ya kuma shigowa a karo na kusan biyar, dai-dai da lokacin da nake ɗaure jelar gashina, garin kai hannu na katse kiran sai na danna answer ba tare da na sani ba naci gaba da abinda nake. sai bayan da na kammala na ɗau wayan zan fita kawai naga mutum ya tallabi fuskarsa yana aikin kallona, kallonsa nayi ya sakar min murmushi yana faɗin,"gyaran gashin yayi kyau, sai ya ƙara fito da beauty nah, kin kalla kanki a madubi kuwa ko kuma kin bar min gari na faɗa?".
Na samu bakin gado na zauna ina zumɓura baki, nayi ƙasa da kaina ina cewa,"to wa yace ka kalle ni?".
Wani siririn murmushi ya saki yace,"yanzu ni har sai an bani izinin kallon Beauty? kallonki fa shine abincin idanuna".
Na ɗago ina kallonsa, nayi shiru bance komai ba saboda wata magana da ta haska acikin kaina, wannan furucin nasa yayi salo da na Yayana da ya taɓa cewa Kallon Cutie nah abincin idanuwana. kamar yanda Proff yay ƙuri yana kallona haka nima na ƙura masa ido, don so nake na ga ai na yake a zaune, idan har naga wani abu mai kama da gidan nan to tabbas zargin Yaya da na ke na shine Proff to ya tabbata, sai dai banga wani alamu na shaidan hakan ba.
Ya ce da ni, "Beauty please ki bani aron hankalinki yau muyi magana kinji".
"ina jinka". na ce ina daɗa haɗe fuska.
"ki fito gani a ƙofar gidanku". nayi saurin ɗagowa ina dubansa da mamaki,"gidanmu kuma?".
Ya ce,"kar ki ɗauka wasa, am serious".
Ina daɗa dubansa na ce,"ta ya akai ka san gidanmu, ni fa ban yarda da kai ba".
Yay murmushi mai sauti kamin ya ce,"Beauty me nayi kuma na rashin yarda, kin kalla nan". ya faɗa yana nuna min wata ƙatuwar waya dake ɗaya hannunsa. map naga yana aiki, lallai ma mutumin nan wato wayo yay min kenan ya kirani ya biyo sahun kiran, kamar ya san tunanin da na ke yace,"nayi miki wayo ko. kiyi haƙuri na zo ba tare da izininki ba, umarnin zuciyata na bi, yanzu dai ki fito waje muyi maganan da ya kamata".
"ai bani nabce kazo ba, don haka sai ka koma".
"aikuwa to yanzu zan shigo da kaina, dama yau weekend nasan Baba na gida kinga sai na sanar masa da abinda ke tafe da ni". nayi zumbur na miƙe ina faɗin,"ni ban saka ba, gani nan".
Ƙaramin gyalena na ɗauka na yafa na fita, na ce da Gwaggo nayi baƙo ina zuwa, ta bina da kallo baki a sake wato abin ya bata mamaki, ina buɗe ƙofan parlo naji tana cewa,"wayyo ni Hannatu daɗi barni da raina, yau Sabina taga zaɓin ranta, yau zanyi kwanan farinciki, dama zuwan wannan rana nake ta jira, Allah yasa dai ku daidaita, fargabata Allah yasa kar jami'an tsaron kanki su sauya miki ra'ayi, domin nima a yanzu banda burin da ya wuce naga na kai ki gida mafi girma da daraja a wurin ƴa mace".
Tana ta murna take faɗin haka don har da ƴar rawarta, ni dai ban kulata ba nayi ficewata. gaban gate ɗin gidanmu kaɗan yay parking motan nasa, na ƙarasa wurin da sallama, da jikin motar na jingina sai haɗe rai nake, ni har ga Allah ban so wannan zuwan nasa ba, wayana yay ringing, ina kallo naga sunansa ne, na ɗaga ina cewa,"to mene kuma na kirana bayan gani na zo, ai nasan ka ganni ka fito mana".
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...