7

119 12 4
                                    

*(7)*
Fitowana daga banɗaki kenan na shigo ɗaki ina goge kaina da na wanke. Na ji muryan Yaya Abba a cikin kunnena yana faɗin,"kinga farar singlet ɗina?".

"Ban ganta ba, bani na kwashe kayan ba sai dai ka tambayi Gwaggo".
Na ƙaraso wajensa ina ƙara faɗin,"Yaya Abba dan Allah zuge min".

Ya kama zip ɗin rigata ya zuge min sannan yasa kai ya fice yana ta zabga mitar da ba ya rabo da ita. Ni mamaki ma yake ba ni ko ciwon baki ba ya yayi, matarsa dai ta shiga uku.
Yau dai ban ji Gwaggo ta tanka masa ba, kuma nasan saboda kar tayi magana ne su yi da shi shiyasa ta share shi.

Ni kuma da ina gyara ɗazu na ga singilet ɗin amma na manta inda na ajeta shi yasa nace masa ban gani ba, dan ina cewa ban san inda na aje ba na shige su da jarabarsa. Maza ma dai da shegen ƙazanta ya ci ace ya sauya singiletin wai amma a haka yake cewa farar singileti bayan duk ta fara koma ruwan madara.

Sa da na gama shiryawa na fita falonmu da yake madaidaici, na zauna na ci sauran ɗumamen tuwon da Gwaggo tace ta rage min, ina gamawa kuma na dawo ɗaki na ɗauki littafin da na yi renting shekaranjiya na shiga karatu, tun a daren jiya na gama karanta book 1 ɗin, Nana Haleema ce ta rubuta shi ina masifar son littafanta.
Sai wajen sha biyu na miƙe, na fito falon ina gyaran ɗaurin ture kaga tsiyana sai ga Farhana ta shigo bakinta ɗauke da sallama.

Fuskarta na washewa da siririyar dariya ta ƙaraso inda nake, wanda ni kuma ganinta yasa na cukule fuska, na dakata da waƙar da nake yi, ina faman cika ina batsewa, sai ta kawo hannu da nufin ture ɗaurin nawa tana faɗin,"Bari na ture sai naga tsiyar".

Na wani bankama mata uwar harara sannan nace,"Da kuwa kinga tsiya ganin idonki".

Tayi dariya tana kama hannuna da nufin mu zauna kan kujera, na turje ina daɗa nuna mata nifa ban bar fushi da ita ba. cikin daɗin baki ta kama cewa,"Haba mana Sabina wai mene kike hakan...wai so kike sai duniya ta jimu ta mana dariya, mutum nawa kika sani da basa son relationship ɗin mu,haba mana comon let by gone be by gone mana".

Ta faɗa tana duba na tare da manno min kiss a goshi. ganin dai kamar ba zan sakko daga kan dokin fushin da na hau ba sai fuskarta ta sauya zuwa damuwa, nan fara'arta ta ɗauke gaba ɗaya, ni kaina na sani Farhana na tsananin so na, haka nima, bama iya faɗan minti biyar bamu shirya ba, mu kan yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu na ɓacin ranmu, duk da cewar wani lokacin ni na kan kasa haƙuri amma ita ko menene haƙuri take yi. 
Sai dai a wannan karon ina mamaki da silar abunda yasa na ke faɗa da ita har na ke irin wannan fushin haka, fushi da ita akan mutumin da ban sani ba, na tsince shi ne kawai a hanya, har kuma na ke jin zan iya rabuwa da ita akansa, bama ita kaɗai ba, kowa ne ne gani na ke zan iya rabuwa da shi muddin bai samawa Yaya lafiya ba.

Na kauda fuskata gefe guda domin bama zan tankawa maganar da tayi ba. tana ƙara riƙe hannuna da na ke son ƙwacewa tace,"Kinga indai akan Yayanki ne kwantar da hankalinki, daga yau ba zaki ƙara jin bakina akansa ba. Wannan alƙawari ne na maki".

Jin hakan yasa na juyo ina dubanta in kalla shin maganartata da gaske ne, ganin na zuba mata ido ina karantar fuskartata yasa tace,"Wallahi da gaske na ke miki, ni bazan yarda wani ya lalata mana zumuncinmu ba. Tsakanina da shi Allah ya shirye shi kawai, ko ba hakan kike so ba?". n

Sai sa'ilin na saki fuskata ina murmushi, kamar yanda muke yi ada yanzu ma haka mu kai, domin kuwa tafin hannuna ɗaga na bata muka tafa ina faɗin,"Yawwa ko ke fa, yanzu naga haskenki".

Ta min harar wasa da cewa,"Ji min walaƙanci, duk wannan uban hasken nawa baƙi kike ganinsa dama?".

Ina dariya nace,"Yo da kike zuzuta hasken na ki, ai na bogi ne tunda na bature ne, ke fa ƴar dare ɗaya Allah kan yi bature ce Farhana".

Na faɗa ina dariya sosai cike da tsokana, ta kawom duka na kauce nayi ɗaki da sauri. Har ɗakin kuwa ta biyo ni muna dariya, Gwaggo na linke kaya ta bimu da ido. Sai da na ɓuya a bayanta ta samu damar yin magana tana duban Farhana.

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now