*BAYAN WANI LOKACI*
"Zai fi maka ka cire soyayyarta daga zuciyarka, ka cire burin aurenta a ranka, ka barta a wannan matsayin da ku ka fara bawa juna tun da farko".
"Saboda me?".
"Saboda ba zaka sameta ba, ba zaka aureta ba muddin ina numfashi a doron ƙasar nan, Hussain ba zaka aureta ba ko bana raye, Hussain yarinyar nan ba zata taɓa zama matarka ba, ka bawa zuciyarka haƙuri ka fara lallashinta tun yanzu".
Wannan furucin shi ya saka Alhussain saurin zuro ƙafafunsa ya sakko daga kan gadon, ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa yana ƙarewa bayan matar da baya iya kallon fuskarta kallo, kallonta yake da saƙawar mabanbanta abubuwa a cikin ransa. Sai dai a duk abunda ya saƙa ɗin baya iya warware shi, saboda haka yayi tattaki zuwa inda take a tsaye jikinta naɗe da lafaya brown colour me duwatsu, tana fuskantar kusurwar ɗakin nasa ta ɓarin hagu, daga tazarar da ba zata wuce inchi 2 ba a tsakaninsu ya dakata.
Ya tattaro yawun bakinsa da yaji kamar yana neman ƙafewa yace da ita,"wace ke?".Shiru tayi masa bata ba shi amsa ba, ya rufe ido ya zuƙi numfashi, gami da sanya hannu ya shafo bayan wuyansa yana kaiwa cinyarsa duka. "Wace ke? kuma me yasa kike min waɗannan maganganun?".
Ya ƙara tambayarta amon muryarsa na cika ɗakin gaba ɗaya. maimakon amsar da ya tsammaci ji daga gareta sai yaji sautin murmushinta ya fita a hankali, wanda ya tabbata murmushin ya tsaya mata iyaka leɓe ne kawai duk da cewar bai ga fuskarta ba. zuciyarsa tayi wani zafi dan haka bai san lokacin da ya ɗora hannu a saman kafaɗar matar ba dan juyo da ita, amma sai wanzuwar abu biyu ya hana hakan, farko wani azababben shock da ya ji ya ratsa gaba ɗaya jininsa har yay saurin ɗauke hannun yana yarfewa, sai na biyu kuma da matar taƙi juyowa tana me ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tare da matsawa gaba, kuma bakinta na furta masa,"Ba yanzu ba Hussain, ba yanzu zaka samu waɗannan amsoshin ba da sauran lokaci, lokacin ba mai tsayi ba, ƙiris ya rage, ƙiris kaman tazaran da ke tsakanin yatsunka".
Furucin da ya ƙara ƙamar da shi kenan a tsaye yana tsare bayanta da ido, dan ya tabbata in har ya ƙara taku ɗaya to zata iya guduwa, so yake ya samu dabarar da zai kai hannu ya fizgota ta juyo, kuma a yanda yake jin zuciyarsa na tafarfasa akan maganganunta zai iya aikata mata ba daidai ba.
"Ban sanki ba, kuma kema nasan baki sanni ba, dan haka ki fita acikin rayuwata da kike ƙoƙarin shiga, ba ruwanki da lamarin soyayyata balle aurena".
Wannan karon kam a zafafe yake maganar, yana mai yin ƙoƙari wajen ganin yay dabarar da zata sa matar ta juyo gareshi don yasan maƙiyarsa tunda wuri ya ɗau mataki.
"Tukunnama! me kike nema a wurina?".
Kai tsaye kuma ya ji muryarta fa fito da cewa,"Kai na ke nema Hussain, kai nake nema domin na faɗa maka muddin baka cire soyayyar yarinyar nan tunda wuri a ranka ba to la shakka zata zame maka guba, Hussain kar ka Ƙwallafa soyayyarta akanta domin hakan zai illataka, soyayyarta tamkar guba ce a gareka...kuma abu na ƙarshe da nake so na faɗa maka shine, Alƙalamin ƙaddara bai rubuta abunda ku ka tsarawa kanku ba Hussain, Alƙalamin ƙaddara bai rubuta muku ba, ka fara lallashin zuciyarka tun yanzu".
Da gama faɗar hakan ɓat sai matar ta ɓace. wanda hakan ya zama dalilin farkawar Alhussain a gigice yana ambaton sunan Allah. ya shiga murza idanuwansa yana daɗa ƙarewa ɗakin nasa kallo don tabbatar da mafarkin da yay ba gaskiya bane. ya sauke ajiyar zuciya yana mai duban agogo da ke saƙale ajikin bango.
"10:00am". Ƙarfe goma na safe haka agogon ya nuna A lokacin, sai yaji wani sabon yanayi da bai taɓa riskar kansa a ciki ba na rantsa shi, gabansa na faɗuwa, kwaɗaituwa da son ganin matar da ta zo a mafarkinsa na wanzar masa.
Sai ya mayar da kansa ya jingina ajikin gado yana me haɗe murfayen idonsa ya rufe. lokaci ɗaya mafarkin da yake yi tsawon kwanaki uku a jere ya shiga tariyo masa a cikin kansa, kwana uku kenan wannan matar tana zuwar masa da magana ɗaya.
_"Wace ita? Kuma me yasa take waɗannan maganganun? Wanne irin saƙo take so ta bar masa? Me alƙalamin ƙaddarar ya rubuta? Sunan Hussain da take kiransa da shi daga ina ya samo asali?"._
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...