*(10)*
Dukkan mu sai muka bi Gwaggo da kallo, Baba ya girgiza kai, a yanayin yanda tayi magana fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi, to amma babu damar yayi magana, dan yanzu zata dire masa ta ce dama shi ke ɗaure musu gindin zaluntar marayu, duk wani abu da su ke da sanya hannunsa a ciki, shima dama ba ƙaunarmu yake ba.kuji fa! wai mu da ubanmu amma abu kaɗan zai yi za tace ba ya sonmu. Ni dai har yanzu daɗi bai gama saki na ba tuni na nufi motana na buɗe na shige ciki ina dubawa, shi kuwa Yaya Abba na daga zaune kan wata kujera ya zuba ido yana kallon abinda ake. Anty da ta ƙware wajen iya kissa nan da nan ta kawar da baƙincikinta ta hau borin tayani murna, Anty macece da ta tsanemu sosai ni da Yaya Abba, don da tana da ikon kawar damu da tuni ta aikata hakan, amma kuma fa duk wannan ƙiyayyar ta ƙware wajen iya kissa, domin bata taɓa nunawa tana ƙinmu a gaban Baba, Ta inda tafi Umma wayo kenan, domin ita Umma agaban kowa nunawa take bata son ƴaƴan mijinta.
Shi yasa Baba idan zaka kwana dubu kana ce masa Anty tayi Laifi ba ya yarda, Ita kanta Gwaggo ba ta yarda da laifinta, saboda Anty makirar macece, Kuma ko laifi tayi to ta san hanyar da zata wanke kanta, amma itama tun a inda Gwaggo ta rafkowa lamarinta, ranar da tace Ya Abba ya shigar Mata ɗaki.
Anty ta taho inda na ke tana ta fara'a tana ce min,"Masha'Allahu mota tayi kyau sosai, inye su Sabina an zama ƴan gayu, lallai arziƙi mai daɗi, gaskiya na tayaki murna wallahi, Babanki ya gwangwajeki ƙwarai matuƙa, duk randa aka fara driving ni za'a fara ɗanawa, sai ki masa adu'an Allah ya ƙara wadata arziƙinsa ya kuma kare shi daga sharrin maƙiya mahassada, kema kuma Allah ya rabaki da sharrin ƙarfe".
Duk tana faɗaɗa fara'arta take tayani murnar, wanda sam bai kai har ƙasan zuciyrta ba. hmmm amma kun san me? saboda baƙar mugunta kun san kuma abin ba don Allah take ba, hannunta na kan wuyana tana bani wani mugun mintsini, da naga tana neman raunana min wuya sai na fito a motar ina yaƙe domin shegen mintsininta ya shige ni, na sauke hannunta daga wuyana na riƙe a hannuna, ina mata murmushi na ke cewa,"Ameen Anty na gode sosai".
Na faɗi hakan ne saboda Baba da ke tsaye a wurin, nima kuma cike da mugunta na ganyarata mata mintsini a hannunta da ke cikin nawa, ba shiri ta janye hannunta tana yaƙe da dukkan alama ya shigeta kamar yanda nata ya shige ni. Na juya wurin ƙannena nace su zo su ga motar, dan suna tsaye ne kamar gumaka, to da ke kowacce ta ɗakko halin uwarta haka suka zo suna leƙa motan suna taya ni murna, fuska babu yabo babu fallasa, ni dai a raina nace oho muku, ni bana ruƙo da irin yanda kuke min, kuma Allah ya ganar da ku.
Sai da Baba ya gama nuna mana komai na gidan sannan kowa ya wuce part nasa. Ina shiga side namu na raka Gwaggo ɗakinta, na nuna mata yanda ake amfani da duk wasu abubuwa musamman ma na banɗaki, ni ɗin ma ba kowanne abu na san ta kansa ba sai dai na jarraba musamman Ac. Duk wannan abun gwananintar da nayi mata ban burgeta ba, Sai da tayi min kushewar da ta saba.
Har da cewa ai ruwan zafin hita da akasa yake zuba a famfo da gangan aka saka don ya saluɓe mata fata ne saboda an san ba iya amfani zata yi da shi ba, to ita a cire shi kawai bata buƙata, ga gawayi nan dan ko gas ma ba zamu dinƙa amfani da shi ba an ce gobara yake haɗawa.
Ni dai ban ce mata ƙala ba, ita kanta dariyar ƙeta take min har na gama na fito. Ɗakina na wuce kai tsaye, ina shiga na hau cire kayana domin yin wanka saboda duk a gajiye na ke. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sirke da turaruka masu ƙamshin gaske, da aka jere su a toilet ɗin, ban wani jima a ciki ba na fito, ina fitowa na shafa mai da kuma faran powder. closet na nufa na zage domin ciro kaya, cak na tsaya ina riƙe da bakina saboda mamaki, kamin na buga tsalle na kurma ihu saboda daɗi, ashe shiyasa Baba ya ce babu buƙatar mu taho da kaya, mu bayar duk waɗanda mu ke da su.
Kayan na shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya, shegun kaya ne na alfarma kamar wata amarya aka zuba min a ciki sunfi set 30, Kuma duk abayas sunfi yawa dama su ne favorite nawa, ban san lokacin da na zube kan gado ba ina hawayen farinciki ina kuma kwaranyo Baba adu'a, oh ni Sabina ban taɓa mafarkin tsintar kaina a irin wannan daular ba, ko da kuwa a gidan miji duk kuwa da ina fatan samun miji mai yalwar arziƙi na halal, sai ga shi ashe zanyi katari da shi tun a gidan ubana, lallai arziƙi na ubangiji ne, shi ke badawa da hanawa a duk lokacin da ya so.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...