*(4)*
Hidimar aikace-aikace na ke tayi tun wayewar gari, yau babu inda ban gyara ba acikin gidan nan lungu da saƙo, hakan yasa ɗan ƙaramin gidan namu ya sake yin fayau da shi yay ƙal-ƙal, haka na ke sam bani da ƙiwar aiki, Gwaggo na yawan faɗa min Mamana na gada, amma duk wata bauta da na ke yi a gidan nan Yaya Abba ba ya ganinta dai-dai da misƙala zarratan.Wuyarta nayi wuyarta ya ɓata kuma ya kushe, wani binma idan ya ɓata yay ficewarsa nayi zuciya nace ba zan gyara ba, to bala'i ko sai dai idan bai dawo gidan ba, amma sai ya sauke min shi, ya dinga cewa Gwaggo wai tana sangartani, zan lalace na zama ƙazama, yay ta aikin zagina. Gwaggo tace masa to ubanwa ke faɗawa idan na gyara, ta hakan ne kawai na ke samun salama, amma ni kaina na san banda ciki guda muka fito da shi la shakka ba zan ke raga masa ba, ina da haƙuri dai-dai gwargwado amma ba kanwar lasa bace.
Kiran sallar azahar ɗin da na jiyo yasa na shiga sauri-sauri na kammala aikin kamin lokacin tafiya islamiya yayi, dan lokaci babu wuya yanzu agogo ya buga ƙarfe uku, dama da safe naji Gwaggo na cewa da Yaya Abba ya saka mata sabon batiri a agogonta, agogon me shegiyar ƙara da zarar cikar daidai yayi zai kama kiɗinsa me hawar min kai. Gwaggo ta fito zata shiga banɗaki tace da ni,"Sabina sannu da aiki".
Na amsa da,"Yauwa Gwaggo, kin fito alwalar ne, bari na zuba miki ruwan".
Ɗaya daga cikin botikan da ke nan tsakar gida na buɗe na zuba ruwa cikin buta kana na bawa Gwaggo. Alwala Gwaggo tayi ta koma ɗaki domin ta gabatar da sallar azahar. Idarwarta kenan sai ga sallaman Baba, ɗakin ya shigo inda ya zauna nan bisa kujera yana gaida ita.
Na shigo a lokacin na durƙusa na gaida shi tare da ajiye masa ruwa da abincin da na kawo mishi. bayan ya amasa min yace,"Yau ba makaranta ne?".
Nace,"A'a da akwai, ai da sauran lokaci. Amma yanzu ma zan shirya da mun gama cin abinci".
"To madallah. Ana dai dagewa ko?". "Ehhh Baba muna yi sosai".
Fuskar Baban ta washe da annashuwa yace,"Allah ya bada nasara, ya kuma yi muku albarka...ai ba'a bina kuɗin makaranta ko?".Ya faɗa a yayinda yake zuba ruwa a kofi zai sha. "Amin amin Baba na gode. ehh ba'a binka".
Na miƙe naje na ɗakko namu abincin ni da Gwaggo, ina cin abincin ina satar kallon mahaifina da na ke jinsa mafi soyuwa a gare ni. kusan tare muka cinye abincin da shi, saboda muna ci ana hira, nan da nan muka tashi kan shinkafa da waken da ya ji haɗin kayan lambu. na tashi na haɗa kan kwanukan da muka ɓata na kai kicin, na dawo na gyara wurin duk da ba wani ɓata shi muka yi ba, sannan na wuce zuwa ɗakinmu da muke kwana ni da Gwaggo.
Nayi wanka na shirya cikin unifom ɗina na islamiya kalar ruwan madara, kayan sun mun kyau sosai, jakar littafaina na ɗauka na rataya kana na fito nace da Gwaggo da Baba zan tafi. A gaban Baba na duƙa ina cewa da shi,"Baba kayi mani adu'a".
Ya dube ni cike da soyayyar uba ga ƴarsa sannan ya ɗora hannunsa saman kaina yace,"Sabina Adu'a ta zama dole, kije Allah yay maki albarka, ya baki nasara a rayuwarki. Allah ya kai ki lafiya ya dawo da ke lafiya ya kare ku a duk inda kuke".
Ina murmushi na ke amsa mishi da,"Amin Babana na gode sosai, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana".
Gwaggo ma tayo tata adu'a sannan na fita, Har naje soro sai kuma na dawo, saboda tunawa da nayi akwai inda na ke son zuwa kuma banda kuɗin mota, satina guda kenan rabon da na fita waje, dama inda makarantar boko ne na ke ɗan samun canji a hannuna, to anyi hutu, ita ma kuma islamiyar sai yaune muke komawa. to yanda na ƙwallafa rai da zuwa inda nake so naje yau ai yacce Baba ya shigo dole na nemi kuɗi.
Ganin na dawo Baba ya shiga tambayana me ya dawo da ni, ni kuma kai tsaye nayi masa ƙaryar zan siya littafi ne na manta ban karɓi kuɗin ba.Na faɗa masa ina tsoron kar yace babu kuɗin a hannunsa amma naje zai shigo makarantar anjima yay wa Malam Saminu magana su bada bashi kaman yanda aka saba. Sai Allah ya taimake ni naji kawai yana tambayana nawa ne kuɗin, da yake ban saba da ƙarya irin haka ba sai na rasa nawa zance, na tsaya ina kame-kamen kamar 200 kamar 150, sai kawai ya zaro 500 ya bani yace na riƙe canjin idan yayi saura, na kuwa amsa murna fal raina inata zabga masa adu'a.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...