*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(24)*
nabi bayansa da kallo ina hararsa kamar zanyi kuka, banda ina tausayinsa da saina faɗawa Gwaggo yanzun nan ta rama min.
***Ƙwiiiiii kake ji a sanda Alhussain yay wani mugun take burkin motar, Allah ya rufa asiri baibi ta kan matar da ta ɗauke yaronta ba daya fito daga cikin shop, Alhussain ya kifa kansa akan sitiyarin motar idanuwansa a rumtse. a wannan lokacin da wasu hawayen da bai san sanda suke saukowa ba, a wannan lokacin Gwaggo dake gaban motar ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyar data amsa gaba ɗaya acikin motar. ta buɗe baki tana ta fitar da numfashi, gefe ɗaya ƙirjinta sai lugude yake kamar allon ƙirjinta zai faso waje. a yanda take ji inda za'ace zuciyarta ce ta fito tayoyin motar tasu tabi ta kan zuciyar ta mitstsike ba zata musa ba, tsawon wucewar wasu daƙiƙu kamin ta dawo hayyacinta, sannan ta dubi gefenta inda Alhussain yake wanda har sannan goshinsa ke akan sitiyarin. sautin muryarta ya fito da wannan fargabar da bata gama barinta ba. "Yaya kasheni zaka yi?, saura kaɗan fa kabi ta kan ɗan mutane ina hankalinka ya tafi?". magana take tayi amma sam bai ɗago ba kuma babu alamar zai ɗago ɗin. hakanne ya ɗarsa tsoro a ranta ta miƙa hannu ta ɗago shi, sai ta ganshi ruwan hawaye duk ya wanke masa fuska, yayinda da idonsa dake buɗe ke kallon waje, inda wannan matar da ɗanta ke tsaye tana rungume da shi tsam ajikinta. "kai lafiya? menene? kai ka juyo ka faɗamin halin da ake ciki, kukan namiji ko tashin hankali". yasa hannu ya goge hawayensa, sannan muryarsa ta fito cikin wani irin rauni me tsinka zuciya yace,"Gwaggo wasu iyayen Mata suna tsananin son ƴaƴansu, irin soyayyar da zasu iya jefa kansu a kowanne irin hatsari". sai yay shiru wani hawayen na ƙara sauko masa, kuma har wannan lokacin ƙwayar idonsa bata ɗauke daga kan wannan matar ba da yake jin wani abu akanta na tsarga masa ba. Gwaggo da tai kasaƙe tana dubansa tace,"hakane. amma maganar daga ina haka?". a wannan lokacin da ya shiga magana muryarsa na fita ne da karyewar kowanne harafi, kuma a yanzu kuka yake sosai. "Gwaggo me yasa tawa mahaifiyar bata kasance irin sauran ba? me yasa tata zuciyar babu wannan ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa?...Gwaggo ni ba ƙaramin yaro bane, na girma, na zama cikakken namiji, amma me yasa kullum nake jin ina buƙatar mahaifiyata a kusa da ni? ina tsananin buƙatar na jita a kusa dani...in da tasan ba zata so ni ba me yasa ta zaɓi ta samar dani ta hanyar da bata dace ba?, ta samar dani ta gurɓatacciyar hanya, dalilin da yasa ta jefar dani kenan a bola...ina sonta, duk da haka ina sonta Gwaggo, kuma na yafe mata ba, kuma zanso tazo gareni ko da na second ɗaya ne, nima na samu naji wannan ɗumin jikin na uwa da kowanne ɗan sunnah yake samu, wallahi ina sonta Gwaggo, ko kaɗan bana fushi da ita". ya ƙarasa furucin da wani irin murmushi me ciwo dake fita a saman fuskarsa, yana mai saka hannu ya goge hawayen fuskarsa sannan yaywa motar key suci gaba da tafi. "ka tuna me likita yace maka?". Gwaggo ke cewa da shi, kuma ba tare da ta jira cewarsa taci gaba da faɗin,"yace damuwar dake danƙare a zuciyarsa zata iya haifar maka da matsala nan da lokaci kaɗan...ka daina damuwar haka, ajikina ina jin akwai wani ɓoyayyan lamari tare da kai". tai shiru tana saka yatsa ta dungure masa kai. "kaje dan kanka tunda ni baka ƙaunar kasancewa tare da ni". sai kawai fuskarsa ta washe da wani murmushi, yasa hannu a kafaɗar Gwaggo, haka yaci gaba da driving ɗin har ya kaita inda take son zuwa.
basu dawo ba sai bayan la'asar, tana shigowa ko zama batayi ba Zainab tazo tace mata Umma babu lafiya, ta zabari ƙafa ta fice a kiɗime sai salati ta ke zabgawa kamar ance mata ta mutu ne. yanzu ma da Yayana zai wuce da gayya ya kuma sa ƙafa ya shafe min tafin ƙafata, ya kuma yi wucewarsa kamar bai san abinda ya aikata ba, baƙinciki ya isheni kawai na fashe da kuka, Yaya Abba dake bacci ya farka ya doka min tsawa akan nai musu shiru, ni dai ban kula shi ba naci gaba da kukana ina kiran Gwaggo. "wai ke me yasa kuka baya miki wahala?". Yayana dake durƙusawa kusa dani ya faɗa. na ɗago na kalle shi na ɗauke kaina, na maida kaina ƙasa naci gaba da kukana. ina kallonsa ta gefen ido yana murmusa fuska saboda walaƙanci, na ɗago ina miƙa masa hannuna nace,"ni dai kunce min na cire shi haka nan kamin ka ƙarasa dagule minshi ya koma dungulmi". na faɗi hakan bana kallonsa saboda ina jin haushinsa. murmushin mungunta yayi, yay ƙwafa kaɗan kamin yasa hannunsa ya kuma dame min na hannun gaba ɗaya, ai ban san lokacin da na kuma fashewa da kuka ba ina dire diren ƙafa, cikin tsawa Yaya Haidar yace. "dilla Malama wannan wane irin rashin hankali ne?". ina sheƙar kuka nace, "don Allah Yaya Haidar kazo ka kunce min na hannu ɗaya na cire sauran, duk an dagule min shi karya zama na tsofaffi". harara ya zabga min yace,"uban wani ya sa ki yin ƙunshin? idan ba ki shiga hankalinki kin cire shi kin tashi kin wuce ciki ba sai na tashi na ɓarar dake anan wurin. kuma karki rufe mana baki ki kalla yanda zanyi dake". ina kallon yanda ya kafeni da ido yana min wani mugun kallo. ni kam ina zumɓura baki nace,"to ni ya kake so nayi, ba zan iya cirewa da kaina ba, kuma Iklima ta tafi islamiya. kawai dan anga Gwaggo bata nan sai a dinga cin zalina, da ace ma ina da Yaya mace babu me min irin hakan". can shima Yaya Abba ya hauni da masifa,"na rantse da Allah kika katse min bacci gaba ɗaya saina taso nazo nan na faffale ki da mari, shashasha kawai, har yanzu ke ba za ki girma da kuka ba". ba shiri naja bakina na gimtse, saboda ko kowa ba zai iya aikata abinda yace ba shi zai iya, dan ya tashi yasa waya ya tafasan jiki ba komai bane a wurinsa, ganina yake kamar ƴar shekara biyar. ni ban san me nayi musu ba suka tsaneni haka, babu mai tattalina acikinsu matsayina na ƙanwarsu, abu kaɗan zanyi su hayayyaƙo min, dama ga abinda ke ƙara basu haushi shagwaɓa ni da Gwaggo ke yi, ina sheƙar kuka naketa ƙunƙuni, Yaya Haidar ya taso a harzuƙe zai bige ni. Yayana ya riga shi isowa, ya tankwashe ƙafarsa tare da kamo hannuna yana kunce min lallan. "Malami kai kuma miye hakan?". Yaya Haidar ya faɗa yana mai jifansa da harara cike da jin haushinsa. Yayana yayi masa shiru, yana sa cokali ya kankare min lallen, dama tunda yazo sam basa shiri da juna, ko magana basa yi, idan kuwa ta kama dole to a rigima za'ayita. sai can ne kuma yay maganar a fizge yace,"kai yanzu idan aka barka sai ka daketa?, Haidar kana abu kamar ba wayayye ba". Yaya Haidar ya mayar masa da cewar,"to kai abinda kayi a wurinka wayewa ne? ka kama hannun yarinyar da ba muharramarka ba da sunan kai mai ilimi". na kalla Yayana naga yana murmushi, a tunanina hannu ɗaya zai cire min sai naga ya kamo ɗayan ma ya shiga cire min, yana gamawa da hannaye ya shiga cire min na ƙafata ma. Haka Yaya Haidar ya gama kwasar haushinsa anan tsaye ya fice ya bar parlon a fusace. ni kuwa yana gama cire min na miƙe ina cewa,"kuma ban gode ba". na faɗa ina murguɗa masa baki. kamin na bar wurin ya damƙo hannuna, shima ya miƙe tsaye, dab dani ya tsaya yana cewa,"ina jin haushinki shine za ki ƙara ɓata min rai ko". ashe lallen daya cire min ya kwaso a hannunsa, ban sani ba naji ya mulke min shi a fuska, sannan ya cika ni yay ficewarsa. cike da takaici na ɗauka wayana dake ringing nayi ɗaki, ina tunanin abinda zan masa na huce, haka kawai ni ban san me nayi masa ba yana cewa yana jin haushina, na shiga toilet na wanko fuskana inata jera ƙwafa. ina karkaɗa kai na ɗaga kiran wayar daya kuma shigowa, sallamar muryar dana jine yasa ni rufe ido ina jin faɗuwar gaba, ban san me yasa ba a duk lokacin da naji muryan Proff sai gabana ya faɗi, kuma duk da cewan muryansa iri guda ne dana Yayana amma shi akan Yayana bana jin hakan, sai dai kaina yana ɗaurewa akan wasu al'amuransu. "Beauty nah". ya katse min tunanin dana tafi. "na'am sir". ko taya akai ya gane, sai ji nayi ya jefo min tambayar,"lalala wa ya taɓa min Beauty, wa ya ɓata miki rai umm Beauty nah?". cikin sanyin shagwaɓata nace,"Yaya ne, kuma ba abinda na masa". na faɗi hakan ina turo baki kamar ina gabansa. "Ya Salam shi Yayan da kansa, gaskiya bai kyauta min ba. amma kiyi haƙuri kinji, Yaya ne babu yanda na iya da shi da na ɗau mataki yanzun nan. yanzu kiyi haƙuri kinji, oya yi dariya naji". ya faɗa kamar yana magana da wata ƴar yarinya, ban kuwa san lokacin da dariyar ta subce min ba nace,"ai ka rabu da shi zan rama ne". Yay siririyar dariyar da sai dana furgita da jinta da kuma sautinta, na rantse da Allah irin dariyar Yayana sak, kalle-kalle na farayi a ɗakin naga ko dai shine ya shigo, sai naga babu kowa, na buɗe baki nace, "Proff...". ban ƙarasa ba naji an fizge wayata an jefar a ƙasa, ina ɗaga kai naga Yaya Haidar a kaina. da muryar ɓacin rai yake nuna ni da yatsa yana cewa. "ke ba ki da mutunci ba ki da hankali ba ki da tunani ba kya aiki da iliminki ko. kin maida kanki ballagaza kowane kare ɗora idonsa yake ajikinki, ki kalla a yanda kike fita parlo bayan duk kin san maza ne a wajen, amma saboda shashanci yay miki yawa an gama sangartaki ke ba ki san abinda ya kamata ba. to ki jini da kyau, duk randa kika kuma bari wancan ɗan tsintuwar ya kuma kusanto inda kike ma sai ranki yayi mummunan ɓaci, bare ki bari ya taɓa miki hannu, za ki kalla yanda zan dake". na buɗi baki zanyi magana naga har ya fice ya barni da takaici, ni yau kam gaba ɗaya sun gama ƙona min rai duk su ukun, shi ko meye ruwansa dani oho. Gwaggo kuwa tunda ta isa ɓangaren Umma taga yanayin da take ciki hankalinta ya tashi, ta fashe da kuka tana cewa,"Allah sarki Hajara sannu kinji. Allah ya ba ki lafiya ya yaye miki. wai dama shi ciwon tun yaushe ne?". ta ke tambayar Yaran. Amina tace,"tunfa jiya ne, ɗazu ma Baba ya turo Dr yazo yasa mata drip da allura. harta samu tayi bacci sai yanzu kuma da ta tashi jikin ya kuma dawowa". Gwaggo ta matsi ƙwalla tana ƙoƙarin kamo Umma ta sanyota jikinta tana cewa,"Allah sarki Sannu Hajara insha'Allahu yanzu za ki samu sauƙi, ba wai-wai za kiyi ba adu'a za ki dinga yi". tana gyara yafen mayafinta kuma take cewa,"yanzu ke gaki aba rusheshiya da na miƙar dake zaune ko kya ɗanji daɗi, jiki sai kace buhun masara. ke Amina zo ki taimakan mu ɗagata zaune, wannan kwanciyar ita zata ƙara kashe mata jiki". haka Gwaggo ta zauna a wurin Umma, sai nan da nan take da ita, bata baro wajenta ba sai da ta ga jikinta yayi sauƙi tukunna.
YOU ARE READING
AL-HUSSAIN Complete
Historical Fiction*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da si...