21

96 12 8
                                    

Bayan Kwana biyu, Zaune nake kan plastic chair a balcony da ke upstairs namu, ina karanta wani haɗaɗɗan novel mai ɗauƙe da wata iriyar soyayya mai burgewa, da kuma sawa kaji kana buƙatar kasancewa da saurayinka a lokacin, ban ma san sunan littafin ba sai da shafin ya yanke min, da sauri nayi scrolling back na duba sunan novel ɗin. *ƘADDARA TA RIGA FATA* naga an rubuta daga haziƙar marubuciyar nan mai suna Anty Nice, cikin sauri na Kunna data na buƙaci da a turo min sauran, babu ɓata lokaci kuwa sai ga Halimahz ta turo mani, godiya nayi mata sosai sannan na kashe datan naci gaba da karatuna, ban ɗau wani lokaci ba na kammala karanta shi, Soyayyan Hummy da Dr ta ƙayatar da ni, sosai littafin yayi daɗi ya kuma faɗakar, ba ƙaramin jinjinawa marubuciyar nayi ba.

Daga nan kuma na ɗora da littafin Al'amari, tunda naci karo da page ɗin da ake zayyano kamannin Hammah Saddam na fara shiga wani yanayi, gaba ɗaya yanayin kamannisa da ake lissafawa sai yake min kama da Yayana, Banbancin su ɗaya Yayana ya fishi haske sosai, wani sanyayyan murmushi na saki ina ƙara gyara zaman karatuna, Saurin lumshe ido nayi a lokacin da nayi katari da wurin da Hammah Saddam ke nunawa Tasleem ɗinsa tsantsar so, Na jinginar da kaina bisa kujera ina daɗa lumshe ido ina ƙiyasto ni da Yayana.

Take kuma naji ruwan hawaye na cika min ido, kewar Yayana ta dakar min zuciya, ina shirin fashewa da kuka na jiyo ƙarar hayaniya a compound, tashi nayi na leƙa, su Aisha na hanga sun kewaye Inna Karima suna murnar zuwanta, tsallen murna na buga na wurgar da wayata akan gado na fice da gudu ina, "oyoyo Innah".

Ina zuwa na ɗafe jikinta. "laaa kunga yarinya zata kada ni". Ta faɗa tana dafe jikin mota, Sakinta nayi ina dariya.

Ita kuma ta bini da wani kallo tana taɓe baki, Kamar dai yanda na faɗa muku a baya, Inna Karima macece da Allah ya dasa mata zuciyar kushe, a hakan ma kallon da take mini tana taɓe baki neman makusa take a jikina, kai ni dai na godewa Allah da Gwaggo bata yo halinta ba, na basar kamar ban san tanayi ba, ina ƙara faɗaɗa fara'ar fuskata ina masu sannu da zuwa.

Jakar hannunta na amsa, ina kallon Mardiyya a gefe sai wani shashshan ƙamshi take, ko takanta ban bi don ba shiri muke ba, na kalla yarinyar da suka zo tare, wanda na fahimci itane ƴar aikin da aka kawo mana, ina mata murmushi nace muje ciki ƴar ƙanwata, ina ta jin daɗi na sami abokiyar hira duk da ni bana zaman kaɗaici tunda ina da Gwaggo. Inna Karima ta yaba gidanmu sosai, ni dai hankalina nakan naji batun kwana nawa zasu yi.

Ta kalla Gwaggo ta ce,"wai Matan gidan basa nan ne?".
"suna nan mana".

"amma naga babu wadda tazo ta gaida ni".
"ni kaina da na ke zaune da su ba gaida ni suke ba, gani dai uwar miji, basa ganina da girma wannan tarihin kin sani ba sai na ƙara ba ki ba, don haka kinga ni dai bana son magana don na san halinki, nima adu'a nake musu Allah ya shirya su".

Abincin da Inna Karima ke ci ta tashi akai, ta fita compound tasa aka kira mata su Umma, tayi musu tatas wanda har dukanmu sai da muka ji dama bata zo ba, saboda yanda tasa Baba a gaba tana masa faɗa tana zaginsa, su kuwa kowacce haƙuri ta shiga bata don suna tsoronta, ita bata wasa kamar Gwaggo da take ƴar barkwanci. Har dare Inna Karima bata bar masifa ba, Gwaggo dai bata ce mata komai ba, don dama idan tana masifa duk bakin Gwaggo mutuwa yake.

Mai aikinmu Iklima na kusa da ni a zaune, saboda ni bani da ƙyama, tunda suka zo nasa tayi wanka na bata kaya masu kyau ta saka, cikin lokaci kaɗan har mun fara sabawa da ita, yanzu haka ma kallo muke a wayata, Mardiyya na gefenmu tana waya da saurayinta, na bawa Iklima wayar na ce taci gaba da kallon kamin na dawo.

A parlo na samu Inna Karima tasa Baba gaba sai zazzage shi take akan yaƙi aurar da ni, ya barni sai kumbura nake ina jera kafaɗa da shi da matansa, ba zai aurar da ni ba sai karatun boko ya gama lalata ni tukunna, wannan kayan haushi da yawa yake. Shi dai Baba haƙuri yake bata yana kuma ƙoƙarin ganar da ita, amma kwata-kwata taƙi fahimta, har cewa ta ke da mahaifiyata nan ba zata taɓa zuba ido tana ganina a haka ba ban cika mace ba har yanzu, saboda ita tasan ƙimata kuma tana ƙaunata...

AL-HUSSAIN CompleteWhere stories live. Discover now